Daga Khalid Idris Doya,
Wakilin jarida Leadership A Yau, Sashin Hausa na rukunin jaridun Leadership, Malam Khalid Idris Doya a ranar Jumu’a ya dale kujerar Ma’ajin kudade na kungiyar wakilan kafofin watsa labarai na kasa (Correspondents’ Chapel) ta kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ).
Malam Doya an rantsar da shi bisa wannan kujera tare da sabon sakataren kungiyar wakilan kafofin watsa labaran na reshen na Bauchi, Mr. Samuel Luka, bayan da suka tabbata ‘yan-takara marasa abokan hamayya a zaben cike gurbi na kungiyar da aka gabatar a watan Satumba na shekarar da ta gabata a Bauchi.
A wancan zabe dai da aka gudanar na watan Satumba da ya gabata, an zabi wakilin jaridar People’s Daily, Alhaji Ahmed Mohammed a matsayin shugaba, yayin da Auwal Hassan na gidan talebijin na Biewer TB da kuma Mr. Abdulra’uf Oyewole a matsayin mataimakin shugaba da sakataren kudi bida-bi.
Shugaban, wanda ya samu wakilcin sakataren kudi na kungiyar, Alhaji Najib Sani, ya kuma shawarci kungiyar ta wakilan kafofin watsa labarai da su cike gurbin mai binciken kashe kudade na kungiyar, wato Odita nan bada.