Wakilinmu Na Jigawa Mika’il T. Abdullah Ya Sami Karuwa

 

A ranar Litinin din makon da ya gabata 5 ga watan Jimadul Ula 1439 daidai da 22 ga watan Janairun, 2018, ne wakilinmu na jihar Jigawa, Mika’il Tsoho Abdullah, ya sami karuwar da namiji. An radawa yaron suna Ahmad Mika’il Tsoho, wanda za a yi shagalin bikin sunan a gobe Litinin 12 ga watan Jimadul Ula 1439 daidai da 29 ga wannan wata na Janairun wannan shekara ta 2018.

A madadin mahaifiyar wannan jariri, mu na rokon addu’arku da fatan Allah Ya raya shi bisa tafarkin Alkur’ani da sunnar Manzo (SAW). Allah ya inganta rayuwarsa ya albarkace ta ya kuma sa shi ya zama mai jin kan iyayensa da adinin Musulunci bakidaya.

Sannan duk wadanda za su halarci wannan shagalin suna, da fatan Allah ya kawo kowa lafiya ya kuma sa a koma gida lafiya.

Exit mobile version