Wakiliyar CPPCC Wadda Take Kokarin Neman Mafita Ga Sha’anin Kiwon Reindeer
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakiliyar CPPCC Wadda Take Kokarin Neman Mafita Ga Sha’anin Kiwon Reindeer

byCGTN Hausa
2 years ago
CPPCC

Kabilar Ewenki dake zama a yankin Mongoliya ta gida na kasar Sin, an yi mata lakabin “Kabila ta karshe dake yin farauta a kasar Sin”, kuma rayuwar al’ummar kabilar ba ta rabuwa da dabbar Reindeer, dabbar da ta sha bamban da sauran dabobbi, sakamakon yadda Reindeer ke bukatar neman abinci a daji, ba za a iya kiwon su a gida ba. Du Mingyan, ‘yar kabilar Ewenki ce, kuma mamba ce a majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC a takaice, wadda take kokarin neman mafita wajen kiyaye wannan dabba da taimakawa al’ummar wurin wajen samun arziki dangane da wannan sha’ani.

Sau tari ne malama Du Mingyan ta kai ziyarar bincike a sassan da al’ummar Ewenki ke rayuwa a birnin Hulunbuir dake yankin Mongliya ta gida, don fahimtar yanayin rayuwarsu. Bisa nazarin da take yi, ta gabatar da shawarwari da rahoto har 9 game da yadda za a raya ayyukan kiyaye Reindeer a wurin, kuma karkashin jagorancin hukumar wurin, an kafa yankin kiwon Reindeer na farko na kasar Sin a garin Aoluguya na ‘yan kabilar Ewenki da ke birnin Hulunbuir, an kuma gina wurin shakatawa bisa al’adun ‘yan kabilar Ewenki da ke shafar dabbar Reindeer, wanda ya samu matukar karbuwa daga baki masu yawon shakatawa.

  • Yadda Ake Samosa
  • CPPCC Ya Rufe Cikakken Taronsa Na Shekara-shekara 

An gudanar da taron shekara shekara na CPPCC a kwanan baya a nan birnin Beijing. A matsayinta na ‘yar majalisar CPPCC, Du Mingyan ta gabatar da shawararta, don neman sassan da abin ya shafa su samar da tallafi na manufofi, ta fannin kare dabbobin Reindeer daga cututtuka da kara haiyayyafarsu.

Du Mingyan daya ce daga cikin ‘yan majalisar CPPCC fiye da 2100 da suka fito daga bangarori 34 ciki har da tattalin arziki da al’adu da ba da ilmi da sauransu, wadanda suka hadu a wajen taron majalisar CPPCC don ba da shawarwarinsu game da yadda za a zamanintar da kasar Sin daga fannoni daban daban, don sauke nauyin dake wuyansu na ba da shawara kan harkokin siyasa da sa ido a fannin dimokuradiyya da tsoma baki cikin harkokin kasar.

Majalisar CPPCC na kunshe da wakilai daga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da sauran jam’iyyun demokuradiyya da ba na kwaminis ba, da wadanda ba sa cikin kowace jam’iyya, da rukunonin al’umma, da wakilai daga kananan kabilu da bangarori daban-daban, da wakilan ‘yan uwanmu daga Taiwan da Hong Kong da Macao, da wakilan Sinawa mazauna kasashen waje da suka dawo da dai sauran wasu bakin da aka ba su goron gayyata na musamman. (Mai zane da rubutu: MINA)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka
Ra'ayi Riga

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
Ra'ayi Riga

Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang

September 30, 2025
Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka

September 29, 2025
Next Post
Ramadan: Sanata Yari Ya Gwangwaje Magidanta 250,000 Da Tallafin Abinci A Zamfara

Ramadan: Sanata Yari Ya Gwangwaje Magidanta 250,000 Da Tallafin Abinci A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version