Connect with us

NISHADI

Wakokin Hausa Hiphop Sun Zagaye Duniya, In Ji Lil Topeeq

Published

on

Daya daga cikin shahararrun mawakan zamani na Hausa Hiphop, MUHAMMAD TOPEEQ, wanda a ka fi sani da LIL TOPEEK, ya samu tattaunawa da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, UMAR MUHSIN CIROMA, inda ya bayyana irin cigaban da wakokin nasu na Hiphop su ka samu a wannan zamani. Da fari Lil Topeek ya fara ne da rayuwarsa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

 

Za mu so mu ji kadan daga cikin tarihinka?

Ni dai an haife ni a garin Kaduna a unguwar Rimi a Emir Road. Na taso a Badarawa Kwaru Majalisa, sannan na yi karatuna a Birkindomin Nursery and Primary School, bayan na kammala karatun firamri na je SMC na yi sakandare dina junior da senior. A Kaduna Capital School na gama, amma duk da wannan abubuwan da na ke yi Ina harkar waka tuntini, saboda na taso a cikinta ne.

 

To, me ya sa ka zabi waka ta zama sana’arka?

Waka ni a gurina ba wani abu ba ne da don ka ji wani na yi ka ce kai ma bari ka je ka koya, ni kawai na taso na tsinci kaina a ciki ne, saboda ni tun asali mutum ne mai yawan sauraron wake-wake, wakokin da na ke yawan ji na Turawa a wancan lokacin na kan tsaya in yi ta bin bakinsu har in iya, to daga nan ne na fara gane cewa ni ma Ina da baiwar wakar, don a lokacin sai na hada sunayen mutane sai na ji na yi waka da shi. To, ta haka na fara yin wakata.

 

A wannan baiwar da Allah ya ba ka wadanne nasarori ka samu?

Gaskiya nasarorin su na da yawa, amma babbar nasarar da na samu iyayena sun ban goyon baya. mahaifiyata ta na ban goyon baya daidai gwargwado, don kuwa sanadiyyan addu’o’i da ta ke yi min da abokaina na samu nasarori sosai, na karbu a wajen al’umma, na kuma samu damar yin wakoki da manyan mawaka da a ke ji da su. Wadannan nasarori ne sosai, na je gurare da dama na alfarma, Ina samun yadda na ke so. Ni kaina sai na rika mamaki kaina, amma ba abin mamaki ba ne, saboda burina ne wannan.

 

Duk inda a ka samu nasara a na samun kalubale. To, wani irin kalubale ka fuskanta?

To, kalubale dai ya na cikin duk wani abu da mutum ya ke burin yi a rayuwarsa, amma duk matsalolin da za ka fuskanta ba za su hana ka zuwa inda ka ke son ka je ba. Don haka ni duk wata matsala da ta bijiro min Ina daukar ta a matsayin jarrabawa ce, kuma Ina kan cin jarrabawa. Don kuwa ni kullin ba na kallon baya, gaba na ke kallo kuma gaba na ke ci, don ni duk wanda ya ke min hassada, to ni ban ma san a na yi ba. Amma Ina ganin hakan ya na faruwa sosai. Don haka ni banda wata matsala a rayuwata.

 

Daga sanda ka fara waka kawo yanzu, ka na da wakoki kamar nawa?

Gaskiya wakokin da na yi ba su da yawa yadda ka ke tunani, don ni ban cika sakin wakoki koda yaushe ba. Na kan zauna ne na yi nazari, don na saki wakar da za ta girgiza duniya. Gabadaya dai ba su wuce 50 ba.

 

Idan mutum ya fara tasowa a irin wannan yanayin na waka, wasu kungiyoyin su kan dauke shi. To, kai ka na da kungiya ne ko ka na zaman kanka ne?

Akwai kamfanonin da su ka raine ni a baya kamar SMB, wadanda su ke aiki a karkashin Smb Nation Rigasa. Ka ga wadannan sun raine ni sosai, su na daya daga cikin wadanda su ka hangi baiwar da Allah ya yi min. Don haka sun janyo ni a jiki na yi aiki da su sosai, amma yanzu Ina aiki ne a kan kaina. Ni Ina cin gashin kaina ne, kullum har zuwa yanzu haka banda wani matsala da kowa.

 

Ka yi maganar ka yi wakoki da manya mawaka. Ko za ka iya lissafa ma na koda mutum uku ne da ka yi waka da su?

Na yi waka da Jigsaw YNS; wani babban artist ne da ya ke zaune a Kaduna. Na yi waka da Emma Nyra, na kuma yi waka da Smartkid.skd da dai sauransu.

 

Ka kan yi waka da Turanci ne ko ka fi yi da Hausa?

Ni Ina yin wakata a duk yadda ta zo min, amma na fi yi da Hausa, saboda akwai wani abu da na ke so al’umma su gane, jin dadinmu ne a ce wakokin Hausa Hiphop duniya ta yi na’am da su. Duk inda ka je ka ji a na maganar shi. Don haka ni Ina yin waka da Hausa da Turanci, amma Hausa na ke so na daga.

 

A na cewa, mawakan Arewa ba su da hadin kai. To, amma kai ya ka kalli lamarin?

Gaskiya ne akwai wannan, amma babban abinda ke janyo haka saboda kowa ya na tunanin ya isa ne ko ya kai. Don haka ni a kullum Ina kallon kaina ni Lil Topeek ne ni ba kowa ba ne. Ka ga da haka sauran mawakan su ke daukar kansu da ba a samu wata matsala ba. Don haka Lil Topeek ba komai ba ne, ba kowa ba ne.

 

Akwai wata wakar da ka yi mai suna Darasi. Ta karbu sosai a duniya. Ko za ka iya gaya ma na darussan da ta ke koyarwa?

Wato wakar Darasi tunatarwa ce, saboda duk wani yaro babba ko karami ya san me Kalmar Darasi yake nufi. Don haka na ke kara sanar da mutane da su ji tsoron Allah, komai za suyi ayi tsakani da Allah. Don haka ka ga duk wani wanda ya ji wannan abin, ba zai so ya yi wasa da ita ba.

 

Ka san ko wane mawaki ya na da wanda su ka fi shakuwa da shi ko kusanci da shi. Ko za mu iya sanin kai da wa ka fi kusanci?

Gaskiya ni duk ‘artist’ mu na tare da su sosai. Ka ga kamar Jigsaw abokina ne sosai, haka kuma su Ddough, su Smartkid da dai sauransu duk dai wani ‘artist’ da ka san cewa ya na ‘rapping’ a Arewa mu na tare. Gaskiya ni ba ni da matsala da kowanne.

 

Wane irin buri ko tunani ka ke yi wa Arewa daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa?

Wane irin shekara biyu a na yi ma ka maganar watanni ne ai, saboda ai yanzu Arewa ta riga ta kama da wuta ko’ina maganarta a ke yi. Ka ga kamar yanzu Kaduna duk inda ka je za ka ga ba wani wanda zai tsaya ma ya na sauraron wakokin Turawa. Ko’ina yanzu wakokin Hausa Hiphop a ke yayi. Saboda haka kenan ka ga an riga an rufe aikin; kadan ne ya rage, kuma ka ga ko Turawan ma su na bibiyar abubuwan su kansu, don kuwa ka ga yanzu maganar da mu ke da kai, akwai wani mawakki na China ta hanyar wakokin da na ke yi na Hausa Hiphop, ya zo yanzu ya na so mu yi waka da shi. Don haka wakar Hausa ta riga ta bi duniya.

 

A baya ka ce ko lokacin da ka ke karatu ka na waka. Ta yaya ka ke iya hada karatu da waka?

Eh, ba abu ba ne mai sauki gaskiya, amma ka san ita waka a iya ‘earpiece’ ne kawai. Don haka daga na sa kida a ‘earpiece’, to shikenan an wuce gurin. Don Ina da wadanda ke buga min sauti, zan gaya mu su taken waka za su yi mun kida. Saboda haka duk lokacin da na samu lokaci kamar irin Asabar da Lahadi zan je na yi wakata. Saboda haka ni dai na san Ina yi, ba kowa ba ne ya san hakan.

 

Kawo yanzu ka na da Album din wakoki kamar nawa?

Ni daya-daya na ke yi ban taba yin ‘midtape’ ba, saboda Ina gani midtape a na yi ne idan ka na waka a gida, ba a san ka a ko’ina ba. Ni kuma ka ga an san ni a ko’ina daidai gwargwado, saboda ni tunda na taso komai nawa a tsare ya ke. Ina da masu shirya min kidana, Ina da ‘studio’ da na ke yin wakata. Hakan ne ya sa na samu karbuwa.

 

Kwanakin baya a na ta fadin ka na aiki da KIngz Of Arewa na su Kabiru Adam Superstar. To, ya gaskiyar lamarin ya ke?

To, ba wai Ina aiki da su ba ne, mu na da kyakkyawar fahimta da su ne, su kan kira ni na yi mu su wani abu, ni ma idan bukatata ta taso Ina neman su, don ka ga ko wakar da ka ji na ce ma ka mun yi da Smartkid.skd, sunan wakar Tapashe, ta na nan fitowa kwanan nan. Ka ga ni na shirya kayata na kira shi ya dora min murya. Ka ga ko kai za ka iya kira na mu yi waka tare.

 

Kawo yanzu ka na da bidiyo kamar nawa?

Na yi aiki a kan bidiyo da yawa, amma fa ban sake su ba. Akwai tsarin da na ke yi ne.

 

Ko za ka iya gaya ma na sunayen wakokinka da su ka yi suna kuma sun karbu a duniya?

Eh, ka ga kamar wakar KWALELANKI, ka ga an san ta a ko’ina, a na son NI DAKE NE da UBAN DABA da DARASI da BULALA da kuma BARIRA, wata waka da ni a kan Matata da kuma wakata INA DA GAYU, wacce mu ka yi da Jigsaw. Yanzu ita a ke yayi, ita ke lokacinta.

 

Za mu so mu ji wasu daga cikin manya kyaututtukan da ka samu a harkar waka?

Gaskiya su na da yawa sosai. Ni ba zan iya tunawa ba, don ka ga akwai wanda Unibersity su ka mun wasu a guraren ‘shows’, wasu gwamnati su ka yi min. Gaskiya su na da yawa sosai. Za mu so mu ji sunayen wasu garuruwan da ka je ka yi wasa. Gaskiya ka ga a kullun Ina bala’in mutunta ’yan Katsina, don mutanen Katsina sun goya mun baya dari bisa dari, don ka ga na je garin Katsina wasa na tara mutane sama da 5,000 a cikin ‘hall’ daya, don da kyar na shiga da kyar a ka fitar da ni. Garuruwa da dama ma hakan ta faru. Ka ga na yi wasa a Abuja, na yi a Kaduna, jihar Nasarawa da dai sauransu.

 

Kwanakin baya akwai wani bidiyon waka da Classik ya yi da Rahma Sadau, mutane su na ta kushe abin har a ka kore ta daga Kannywood, wato masana’antar shirin fim din Hausa. To, kai ya ka kalli lamarin?

To, kamar yadda na gaya ma ka a baya ne kowa da irin fahimtarsa. Ka ga kamar Classik ba za ka ce ma shi Lil Topeek ba, haka kuma Lil Topeek ba za ka ce mai Classik ba, sai dai ka ce su na waka iri daya. Ka gane irin wannan abubuwan? To, ka ga kenan da ni da shi za mu iya yin wani abin, saboda irin wadannan abubuwan, amma kuma bayan mun yi wasu za su yi ma sa wata fahimta, sai ya zama kananan maganganu. To, ni dai ra’ayina a kan wannan shi ne idan ma an yi wani abu ba daidai ba ne, to yanzu an gyara, wasu sun so abin, wasu sun kushe, kuma da ma hakan duniyar ta ke; ba lallai na yi abu ba wasu su so abin. To, haka ne.

 

Za mu so mu ji irin abincin da ka ke so da kuma kasar da ka ke son zuwa a duniya?

To, ni dai Lil Topeek Ina son cin shinkafa da wake, kuma Ina son zuwa Saudiyya, Itali da Amerika, Malaisiya da dai sauransu.

 

Wane jan hankali za ka yi wa ’yan uwanka mawakan?

To, mu daina daukar kanmu a matsayin wani abu, sai duniya ta dauke ka da mahimmanci. Saboda haka mu sauke girman kai, mu zauna lafiya da mutane, kada a rika tada fitani a tsakani, ka tsaya ka yi abinda ya dace ka yi a lokacin da ya kamata.   Wacce irin shawara za ka ba wa sauran matasa masu ra’ayin yin waka? To, ni shawarata ita ce, su tsare mutuncinsu a duk halin da su ka tsinci kansu, kada ka yarda wani ya canza ma ka tunani ko ya sa ka rika waka ka na sa batsa a ciki. Wannan bai dace ba, mu kula mu kama kanmu gabadaya.

 

To, a karshe me za ka ce wa masoyanka?

To, ni Lil Topeek Ina son masoyana kwarai da gaske. Ina matukar kaunar su, kuma ba zan so na yi mu su abinda zai bata masu rai ba ko kadan ba. Ina nan Ina shirya mu ku wata zazzafa, ku tsammaci fituwarta kawai!

 

 

 

 

 

 
Advertisement

labarai