WALƘIYA: Matashiya Kan Shirin Bayar Da Tallafin Gwamnati

tare da: Ibrahim Mohammed Aboki

imaboki@yahoo.com

Makon da ya gabata gwamnatin tarayyar Nijeriya ta fitar da sakamakon waɗanda suka samu damar hayewa matakin farko na tallafin bashi da za a bayar ga matasan ‘yan kasuwa ƙarƙashin tsarin YouWiN Connect; daya daga cikin tsarukan da muka kafa misalai da su a rubutunmu na ‘Yadda Mutum Ke Iya Samo Tallafi’, makonni kaɗan baya.

Da yawan mutane waɗanda suka samu nasarar hayewa wannan mataki a shirin YouWiN Connect, ciki har da masu karatun wannan jarida, sun tuntube ni akan Karin bayani dangane da shirin na YouWiN Connect. Na fada masu maimakon bayar da amsa ga daidaikun mutane, zan amsa dukkan tambayoyinsu a cikin wannan rubutu, wanda kuma nayi alkawarin sanar da kowannensu domin neman kwafin jaridar don samun amsar tambayoyinsu.

Bincikena ya tabbatar min, a wannan matakin, an zaɓi mutanen da yawansu bai gaza dubu hamsin da biyar ba (55,000) jumlatan a Nijeriya, sannan kuma sun tura wa kowane wanda aka zaɓa cewa nan da ‘yan satikai masu zuwa zasu turowa mutum yadda zai samu horaswa ta yanar gizo (online), da kuma sauran abubuwan da zasu biyo baya. Kafin nan, zamu tashi masu karatu akan shi kansa shirin na YouWiN Connect, asalinsa, dalilin kirkiro shi da kuma natijar da ake so ya haifar a karshe.

Shirin ya samo asali a shekarar 2011, ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Goodluck Jonathan da hadin gwuiwar bankin duniya da wasu bankunan ƙasar nan da nufin tallafawa a bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan ta ɓangaren kanana da matsakaitan masana’antu. Shirin ya samu tagomashin ma’aikatun yada labarai, matasa, mata da kuma ma’aikatar kuɗi ƙarƙashin jagorancin minister Kuɗi ta lokacin; Ngozi Okwonja Iwela. Dalilin koirkiro shirin shine alkawarin samar da ayyukan yi da shi tshon shugaba Jonathan din yayi a lokacin yakin neman zabensa a shekarar 2011. Da kafa gwamnatin ba’ayi nisa ba, Ministar kuɗi ta lokacin, Ngozi Iwela, ta taso keyar shugaban da cewa to fa ya kamata a cika alkawarin samawa matasa aiki, tare da haska masa cewa ayyukan ba zasu zama ta ɓangaren gwamnatin ba, sai dai ta ɓangaren masa’antu- waɗanda sune zasu samar da ayyukan. Wannan ne ya zama tubalin dasa shirin na YouWiN.

Sun kira shirin da ‘Youth Enterprise with Innoɓation in Nigeria’ ko kuma ‘YouWiN’ a taƙaice. Da hausa yana nufin, ‘Zakakuran Matasan Yan Kasuwa a Nijeriya’. Anyi shi da nufin zaɓar matasa 1200 duk shekara, an kuma samu nasarar zaɓar wannan adadi a shekarun 2012 da 2013, yayin da a shekarar 2014 aka kara suka zama 1500. Gaba dayan mutanen da suka samu shiga wannan tsari kafin waccar gwamnatin ta kau, sun kai mutune 3900. Sannan kafin dai waccar gwamnatin ta kau, ta fitar da kiyasin cewa waɗannan mutane 3900 sun samarwa da mutane 26,000 ayyuka a fadin Nijeriya.

Dukkan wanda ya samu nasarar wannan shirin an biya shi kuɗi kimanin miliyan daya mafi karanci zuwa miliyan goma mafi yawa. Ya danganta da yawan kuɗin da manhajin kasuwancinsa, wanda ya gabatar a lokacin gasar, ke buƙata. An zaɓi mutane daga cikin masu sabbin fikirorin kasuwanci da suke buƙatar jari don aiwatar da su da kuma waɗanda suke cikin kasuwar, suke buƙatar Karin jari don sake bunƙasa kasuwancin ko sana’ar. Anyi kokarin tattaro tare da shigar da mutane daga kowane ɓangare na ƙasar nan, kudanci da arewaci. Illa dai wasu ɓangarorin sun fi yawa a ciki fiye da wasu, wannan kuma ba zai rasa alaka da yadda wasu ɓangarorin sukafi shiga gasar fiye da wasu ba. Ko kuma suka fi rubuta nagartattun manhajoji fiye da wasunsu.

Bayan an samu nasarar aiwatar da shirin ‘YouWiN’ a karo na uku, an sake bude na hudu a shekarar 2015, har ma masu nema sun tura manhajinsu na kasuwanci a matakin farko sun fara jiran sakamako; kwatsam sai gwamnatin da ta kirkiro shirin ta fadi zabe- lamarin da yayi sanadiyyar tuntsirewar shirin. Aka kasa gane makomarsa, domin gwamnati tana cikin sambatun zafin faduwar zabe, ita kuwa sabuwar gwamnati tana tsakiyar murna da kuma tunanin rushe duk wani tsari na wannan gwamnatin da sukayi imani komai na ta matsala ne.

Hawan sabuwar gwamnati ke da wuya, sai labari yazo cewa an kasha tsarin ‘YouWiN’, wasu majiyoyin kan ma suka ce wai anyi almundahana ne a ɓangaren. An zargi wasu manya a ɓangaren kula da shirin da kokarin cusa ‘yan uwansu ko uwan matansu a cikin shirin ta hanyar magudi. Har ma sun buga misalai da wasu kalilan a ciki. Bayan dogon Nazari, musamman kan rashin aikin yi da ke addabar matasanmu a Nijeriya, sabuwar gwamnatin tayi tuntuba akan yiwuwar cigaba da shirin ko akasin hakan. Karshe dai suka yanke shawarar cigaba da shirin, sukayi kwaskwarima a sunan ya zama ‘YouWiN Connect’.

YouWiN Connect kamar yadda suka kira shi, za a iya cewa cigaban YouWiN ne amma ya bambamta da YouWiN ta fuskoki da dama. Shirin YouWiN ya bayar da kuɗi ne kyauta ga waɗanda suka samu dacewa, shi kuwa YouWiN Connect bashi ne za a bayar. An yi YouWiN Connect ne don matasa, mata da maza, yan shekaru 18 zuwa 40, waɗanda ba ma’aikatan gwamnati ba, suka iya yin Magana da turanci, sannan kuma sunyi karatun gaba da sakandare.

Ita kuwa tsohuwar shirin YouWiN ba’a iyakance shekarun mutane ba, ba’a ce sai wanda yayi karatun gaba da sakandare ba, babu batun iya Magana da turanci, ba’a cire ma’aikatan gwamnati ba domin akan samu ma’aikata ‘yan kasuwa a wasu lokutan a wasu wuraren. Mutane 1200 aka zaɓa duk shekara a YouWiN in banda shekarar karshe da aka ƙara aka zaɓi 1500, shi kuma YouWiN Connect 5000 za a zaɓa duk shekara. Sai dai dukkan biyun sunyi kama ta fuskacin suna da kuma samar da ayyukan yi ga mutane.

Matakai guda hudu ne za a bi a shirin ‘YouWiN Connect’, waɗanda suka hada wanda ake kai yanzu haka, wato matakin farko da mutanen da aka zaɓa zasu samu horaswa ta yanar gizo (online training). Da na’urar kwamfiyuta ko manyan wayoyi kadai ne za a iya samun halartar wannan horaswar. Za a koyawa mutane ɓangarori na kasuwanci ne kama daga abinda akeyi, masu saya, abokan sayarwa da yadda za a tsrer masu, ma’aikata da kuma gogewarsu, kasafin kuɗi, talle da sauransu. A karshen kowane darasi akwai tambayoyi da kowa zai amsa, ana tsammanin kowa ya samu yaci abinda bai gaza maki hamsin ba akalla. A wasu lokutan akan bayar da aikin da mutuum zaiyi da kansa don auna fahimtarsa. Hakan shi ke nuna mutuum ya fahimci darasin. Za a baiwa kowane darasi kwanaki kafin a cire ko kawar da shi daga dandalin samun horo na yanar gizo (online training).

Mataki na biyu shine na horaswar gaba da gaba (Onsight training) wanda za ayi bayan an kamala horaswar yanar gizo (online training). Babu wanda zai halasci wannan horaswar sai wanda ya samu nasarar halartar waccar ta baya ba tare da wata tangarda ba. Ya zamanto ya faro tun farko, ya kuma yi duk wani abu da ya zama dole. A gane wasu kan fara su sare, wasu kanje har karshe amma sukan ki yin wasu abubuwan ko su tsallake; to duk wanda baka yi ba, matukar dole ne, to ba zaka samu goron gayyatar horaswar gaba da gaba ba.

Mataki na uku shine na amfani da ilimin da ka samu wajen horaswa guda biyu da aka baka sai ka rubuta manhajin kasuwanci ka bayar domin alkalan gasar su duba, su hukunta kasuwancinka. Idan sun duba sai su tura shi zuwa ga bankin masa’antu domin su zama maka garkuwar karbar bashi (collateral). Zaka rubuta shi tamkar kundi mai dauke da shafuka da yawa- waɗanda suka kunshi bayanai dangane da kasuwancinka tun daga farko har karshe.

Matakin karshe shine matakin hada ka da bankin masana’antu (Bank Of Industry) da YouWiN Connect zasuyi domin baka bashi da kuma sauran abubuwan da suka dace kamar yi maka saiti a kasuwa da kuma sa ido. Kamar sauran matakan, shi ma wannan matakin babu mai zuwansa sai wanda ya tsallake waɗancan matakan ba tare da wata matsala ba.

Kowanne daga cikin mutane dubu biyar din da za a zaɓa zai samu jarin miliyan daya zuwa goma, zai kuma biya kuɗin a tsawon shekaru biyar ta hanyar biya duk wata har tsawon watanni sittin. Allah Ya baiwa mai rabo sa’a.

 

 

 

Exit mobile version