Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Walimar Shan Ruwa: Sarkin Zazzau Ya Bukaci Hukuma Ta Tsaurara Tsaro

by
3 years ago
in LABARAI
2 min read

After Friday Prayer (Jumma)

WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

EFCC Ta Bankado Gidaje 17 A Nijeriya Da Kasashen Waje Na Akanta Janar

Mai Martaba SarkinZazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris, ya bukaci hukumomin tsaro a tarayyar Nijeriya da su kara tashi tsaye,domin kawo karshen matsalolin tsaro da suke faruwa dare da rana a sassan Nijeriya, musamman a Jihohin arewa.
Alhaji Shehu Idris, ya nuna wannan bukata ce, a taron walimar shan ruwan goma ga wata na watan Azumi da Mai Martaba Sarkin Zazzau ta saba shirya wa, inda al’umma daga sassan ciki da wajen Masarautar Zazzau ke halarta.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, ya nuna matukar damuwarsa kan yanda a duk rana, matsalolin tsaro da suke faruwa a sassan Jihohin arewa, ke zama sanadin rasa rayukan al’umma maza da mata, yayin da wasu kuma ke samun munanan raunuka da kuma asarar dukiyoyin da ba sa misaltuwa, a dalilan matsalolin tsaro da suke faruwa.
Tun da farko, a jawabinsa a matsayin babban bako mai jawabi a wajen walimar shan ruwan na goma ga watan Azumi, tsohon shugaban hukumar tsaro ta ‘’ OPERATION YAKI ‘’ a Jihar Kaduna, Kanar Yakubu Yusuf Soja, ya nuna matukar jin dadinsa ne na yanda Masarautar Zazzau ta ba shi damar gabatar da jawabi a wannan taro mai tarihi da Mai Martaba
Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya saba shiryawa a fadar ta shi ta Zazzau, tun shekaru da dama da suka gabata.
A kuma jawabinsa kan matsalolin tsaro da suke addabar Nijeriya a yau, Kanar Yakubu Yusuf Soja, ya bayyana matsaloli da yawan gaske da ya ce, su ne kan gaba da mahukunta ya kamata su dauki matakai, domin warware matsalolin tsaro a Nijeriya, musamman Jihohin arewa da kuma
Nijeriya baki-daya.
Cikin matsalolin da fitaccen masanin tsaron ya bayyana, sun hada da yin gyara kan yanda ake daukar jami’an tsaro aiki, musamman a cewarsa, yanda ake daukar kananan yara aikin samar da tsaro, kuma a basu makamai ma su karfi, wannan a cewarsa, babbar matsala ce da mahukunta ya dace su duba, domin kawo gyara a kan lokaci.
Wata babbar matsalar kuma, kamar yanda ya ce ita ce, na yanda ake sallamar kananan sojoji a dalilin aikata laifin da ya kamata a yi ma su hukunci da dokokin aikin soja ta tanada,‘’ amma a maimakin hakan sai a kore su daga aiki. Kuma ya koma ya shiga cikin al’umma, wannan ma kamar yanda Kanar Yakubu Soja ya ce, lokaci ya yi da mahukunta ya kamata su duba, domin wannan matsala ce, a dauki matakan ci gaba da faruwar wannan matsalolin na korar sojojin.‘’
A dai jawabinsa, Kanar Yakubu Soja, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya, da ta kara samar da tsaro a kan iyakokin Nijeriya, domin,
kamar yanda ya ce, akwai matsaloli masu yawan gaske da suke faruwa a kan iyakokin Nijeriya, da ke haifar da matsalolin tsaro da ke addabar Nijeriya shekaru da dama da suka gabata.
Hakanan, Kanar Yakubu Yusuf Soja, ya bayyana yawan cin hanci da karbar rashawa a tsakanin ma’aikatan Nijeriya da sauran al’umma, a matsayin babban kalubale, wanda a cewarsa, suke neman durkusar da tsaro, duk gwamnatin Tarayya da wasu gwamnonin Jihohi na bakin kokarinsu, kan dakile matsalar tsaro a Nijeriya, amma matsalar kamar yanda ya ce,
sai kara ruruwa take yi tamkar wutar–daji.
Domin warware matsalolin tsaro a Nijeriya, Kanar Yakubu Soja, ya shawarci gwamnatin tarayya, da ta kafa wani kwamiti mai karfi, da ya kunshi Sarakuna da kuma kungiyar Miyetti Allah, domin samar da hanya ta karshe da za ta kawo zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali ga al’ummar Nijeriya baki-daya.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Mace Ta Maka Mijinta A Kotu Kan Kin Daukar Dawainiyar Tagwayensu

Next Post

Kwadayin Mulki: Jami’an Gwamnati Mai Barin Gado Na Fafutikar Kamun Kafar Zababben Gwamnan Yobe

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

‘Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

by
5 hours ago
0

...

EFCC Ta Bankado Gidaje 17 A Nijeriya Da Kasashen Waje Na Akanta Janar

EFCC Ta Bankado Gidaje 17 A Nijeriya Da Kasashen Waje Na Akanta Janar

by
17 hours ago
0

...

Ana Kokarin Siffanta Kungiyar Dattawan Arewa A Matsayin Mai Zuga ‘Yan Tawaye A Nijeriya – Dr. Hakeem

Ana Kokarin Siffanta Kungiyar Dattawan Arewa A Matsayin Mai Zuga ‘Yan Tawaye A Nijeriya – Dr. Hakeem

by Abdulrazaq Yahuza Jere
1 day ago
0

...

Masarautar Zazzau Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Jama’atu Na Kai Karar Sarkinta

Masarautar Zazzau Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Jama’atu Na Kai Karar Sarkinta

by Abubakar Abba
2 days ago
0

...

Next Post
Kwadayin Mulki: Jami’an Gwamnati Mai Barin Gado Na Fafutikar Kamun Kafar Zababben Gwamnan Yobe

Kwadayin Mulki: Jami’an Gwamnati Mai Barin Gado Na Fafutikar Kamun Kafar Zababben Gwamnan Yobe

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: