Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
Gwamnan Neja Ya jawo hankalin sabon Shugaban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta gwamnatin tarayya, Farfesa Abdullahi Bala da ya zama mai jagoranta jami’ar akan gaskiya da amana a lokacin aiwatar da nauyin da aka dora masa
Ya ce, wannan nauyin da aka dora mai ya biyo bayan jajircewarshi da kwazo akan aiki da ya nuna a baya.
Bayanin hakan na kumshe a wata takardar taya murna ga sabon shugaban jami’ar da Jami’in hulda da manema labarai na mai girma gwamnan Jihar Neja, ya aikewa manema labarai.
Ya ci gaba da cewa; “Za ka bada gudunmawa na lokacinka ga shugabancin wannan jami’ar, don dawo da martabar ilimi a kasa, ta yadda tsarin ilimi a Jami’ar FUT da ke minna zai samu tagomashi da bunkasa don samun daidaito da tsarin kasa da ma duniya baki daya.
“Hukumar gudanarwar jami’ar ta yi farin ciki da hada hannu da kai wajen samar da zaman lafiya a Jami’ar wanda zai janyo hankalin dalibai daga ko ina a cikin kasa don sha’awar shigowa don cigaba da neman ilimi. Gwamnan ya cigaba da cewar ya kamata sabon shugaban jami’ar kasancewarsa cikakken dan jiha da ya tabbatar jihar ta cike gurabun da aka bar ma ta, tare da kirkiro gurabun ayyuka ga jama’ar jiha. Kasancewar ka dan kasa na gari, wanda ya kwatanta a ayyukansa na baya, lallai ka zama jakadar jiha ta yadda gwamnatin jiha za ta hada hannu da jami’ar don bunkasa tsarin ilimin jami’a.”In ji jami’in huldan
Farfesa Abdullahi Bala dai dan asalin jihar Neja ne daga karamar hukumar Suleja. Yayi mafi yawa na karantunsa a jami’ar Landan, kafin zuwansa kan wannan mukamin ma’aikaci ne a jami’ar ta Kimiyya da Fasaha (FUT) da ke Minna, ya taba rike mataimakin shugaban jami’ar kuma ya taba rike mataimakin shugaban jami’ar a bangaren gudanarwa, sannan memba a kwamitin gudanarwa na jami’ar. A na sa ran zai fara aiki 3 ga watan disamba na 2017, kuma shi ke rike da rawanin Walin Zazzau Suleja, yana da mata da yara.