Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

WALKIYA: Dogaro Da Kai: Kalubale Ga Arewacin Nijeriya

by Tayo Adelaja
September 12, 2017
in NAZARI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare da: Ibrahim Mohammed Aboki

Ko mu so ko mu ki, dole mu yarda da irin kalubalen da ke fuskantar arewacin kasar nan, duk da irin jin izza da al’ummar yankin keji bisa kasancewarta Bahaushiya musulma, sannan kuma mafi yawan al’umma a kasar. A fili yake yadda alkaluma ke nuna fifikon Arewar a kan Kudu dangane da talauci. Kila ma hakan ne dalilin da ya sa daya daga cikin manyan sarakunan gargajiya a yankin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II; ya tabbatar da cewa, “In da yankin kasa ce mai zaman kanta, to da ta fi kowace kasa talauci da kaskanci a duniya”.

samndaads

Da yawan mutane ba su ji dadin maganar ta mai martaba ba, yayin da wasu kuma ke ganin tsantsar gaskiya sarkin ya fada, amma ba a bakinsa ya kamata a ji ta ba. Duba zuwa ga mabambanta ra’ayoyi a kan zancen basaraken, babu wani da ya musa maganar, illa dai sun kawo wasu uzurorinsu, kila domin makauniyar soyayyarsu wadda ba ta barinsu su karbi gaskiya ko da kuwa ta zo musu ta fuskar da ba su so ba. Ko ma dai mene ne, dole mu yarda cewa Mai Martaba Sarki Sanusi ba kawai sarkin gargajiya ba ne, a’a, shi kwararre ne a fannonin ilimi da dama ciki har da ilimin tattalin arziki (Economics), fannin da ya zame wa yankin Arewacin kasar nan tilas a bunkasa shi matukar suna son dorewar cigaban yankin a gaba tare da tafiya kafada-da-kafada da ‘yan Kudancin kasar nan wadanda suka ba mu tazarar da ta kai ta tsakanin sama da kasa.

Jihar Legas ce ta fi kowace jiha a fadin kasar nan karfin tattalin arziki in da kashi tara bisa dari na ‘yan jihar ne ke fama da rashin aikin yi, yayin da jihohin Zamfara da Yobe a Arewacin kasar nan ke fama da rashin aikin yi da kaso 88% da 90% na al’ummar jihohin. Kila wani ya ce ai jihar Legas na bakin ruwa ne sannan sauran jihohin, irin su Neja-Delta da danginta akwai arzikin mai shi ya sa suka fi Arewacin kasar nan. Haka ne, to amma ai sauran jihohin Kudancin babu wadancan abubuwan. Kenan, Kudancin dai sun fi Arewacin.

Kodayake wasu kan alakanta matsalolinmu da yawan da muke da shi, idan na dubi kasar Sin da take da kusan kashi daya bisa uku na yawan mutanen duniya, sai in ji ban yarda ba. Na fi yarda da cewa rashin amfanin mutanen ne babbar matsala amma ba yawansu ba. Ma’ana mutanen ba su zama masu amfani ba, sun fi dogaro da wasu wadanda kuma a zahiri ba dole su iya samar musu mafita ba, ko kuma gazawa wajen nema wa kansu abin yi. Da kuma yadda mafi yawan mutane ke daukar aikin gwamnati da kasuwanci ne kadai abubuwan yi, musamman ma da rashin wutar lantarki ya haifar da durkushewar bangaren masa’antu a yankin.

A sanina any i nisa a karatun boko a Arewacin kasar nan, amma kuma abin takaici shi ne yadda muke daukar cewa iya amfanin karatun boko shi ne aikin gwamnati kadai, wanda kuma a zahiri ba haka lamarin yake ba. Karatun boko yana da amfani ga duk wanda ya same shi, kuma ko a harkar kasuwanci wanda ya yi karatu ya fi wanda bai yi ba morewa. Abin da haushi ganin yadda wasu da suka yi karatun boko mai zurfi, yayin da wasu nasu karatun bai wuce cikin cokali ba, duk da haka sai su ki neman sana’a su yi ta zaman kashe wando wai su aikin gwamnati suke jira, wanda kuma zai iya daukar lokaci kafin damar ta samu a gare su. Wasu lokutan har shekaru arba’in ko kusa kada haka, shekarun da idan Allah Ya yi ma nisan kwana, to su ne rabin rayuwarka, sannan a wasu lokutan aikin ma ba ya samuwa kwata-kwata.

Babu mai musun yadda matsalar rashin aikin yi ta addabi yankin Arewacin kasar nan fiye da Kudanci, sannan kuma albashin ma’aikatan gwamnatin da matasan yankin suka fi so, fiye da kashi casa’in ba ya isan su.

Ita ma kasuwar ta habu da irin nata matsalolin a wabannan shekarun, inda miliyoyin ‘yan kasuwar suka karye, samun riba ya ragu, karancin jari da sauransu, amma dai wadannan ba su isa su zama dalilan mutum na kauce wa kasuwancin ba domin neman rufa asirin kai. Tun da dukkan matsalolin ana iya magance su.

Wasu kan yi kuskuren fassara kasuwa da babban shago ko kuma saya da sayarwa, ma’anar kasuwa ta wuce nan; tana nufin duk wani nau’in saya da sayarwa komai kankantarsa da kuma sauran sana’o’in hannu dukkansu kasuwanci ne. Wanda kuma duk wanda mutuum ya rika ya ishe shi ya rufa wa kansa asiri. Ta yiwu wannan ne ya sa wasu masu dabarar ke hada abu biyu, wato kasuwanci da aikin gwamnati, ko aikin gwamnati da sana’a, ko kuwa noma da kasuwanci, ko kuma aikin gwamnati da noma. Na kuma kula duk da irin matsalolin da ake ciki a kasar nan, wadanda suka riki biyun sun fi zama lafiya, ma’ana sun fi samun rufin asiri. A wasu lokutan daya ma kan iya wadatar da mutum, amma dai ga mafi yawan mutane sai an hada biyu.

Mene ne laifin idan ma karatun bokon ne mu yi shi da gaske tamkar yadda kowa ke cire lalaci ya yi shi da kyau, ba kawai mu je aji mu zauna in an taso mu watsar da littattafanmu sai gobe ba, mu ba mu watsar da karatun baki daya ba, ba mu kuma tsaya mun yi shi da kyau ba? Mene ne amfanin hakan? Shin ba lokacinmu muke batawa ba? Abin da Malam Bahaushe ya fi sani shi ne, ‘yan kabilar Yarbawa sun fi kowa karatun boko a Nijeriya, sannan Inyamurai sun fi kowa sanin harkar kasuwanci; wane ne ya ce masa shi ma ba zai iya zama gwani a wadannan bangarorin ba, ko kuma an rufe kofar bai wa wani dama ya shiga? Ga shi kuma ayyukan kungiyoyin sa-kai ko kuma kungiyoyi masu zaman kansu shi ma Yarbawan ne a gaba? Mun kasa gane cewa ba nada mutuum ko kabila ake yi ba, a’a, in ce ko kokarin al’ummar ne ke kaita ga wannan matakin ba zancen baka ko mafarki ba?

Musamman ma a bangaren mata da kananan yara, wanda tarihin Malam Bahaushe ya dade da wofintar da su. Yake kallon mace a matsayin wani abu na biyan bukatar sha’awa da kuma dafa abinci kawai, ko kuma yara a matsayin su girma su taimake shi, wanda kuma a ma’anar farko ba haka abin yake ba. Ita mata abokiyar zama ko rayuwa, ya kamata a kalle ta su kuma yara a kale su a matsayin wani nauyi da Allah Ya dora wa iyaye na kula da tarbiyyarsu, sannan kuma za su iya amfanar mutum ko da bayan ransa ta hanyar addu’a, sadaka da sauransu.

Matukar al’ummar nan na son zama lafiya da kanta da kuma makomarta a gaba, wacce ita ce ta fi zama abin tsoro, idan muka yi la’akari da maganar da fitaccen masanin tattalin arziki, Rabaran Robert Malthus ya yi a kan cewa lallai fa duniya tana karuwa da rubanyawa sannan kuma abinci yana karuwa ta hanyar tarawa; dole ne ta farga daga walagigin barcin da take yi, ta yi wurgi da dabi’ar lalaci ko yawan kallon nesa a kusa, ta watsar da mafarkin jin dadi ba tare da an yi fafutuka ba sannan ta tallafa wa dukkan bangarorinta; domin a gudu tare, a tsira tare. Ba kawai wadansu ‘yan tsirarun mutane su zama su ne kadai masu yi mata tunani ba, wadanda kuma in aka yi rashin sa’a tunaninsu ya gaza ko kuma son zuciyarsu ya shiga, sai hakan ya shafi dukkan al’ummar. Shi tunanin mafita a cikin al’umma aiki ne na kowa, maza da mata, manya da yara. Watsar da bangare daya cikin wadannan sai ya yi wa al’umma raunin da za ta dade bai warke ba.

 

Za mu cigaba sati mai zuwa a kan tsarabar zuwana Amurka da kuma darussan da na koyo.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Zaben 2019: ‘Yan Kasuwa Za Su Tsaida ‘Yan Takarkarunsu A Kano

Next Post

An Bukaci Gwamna Lalong Da Ya Yi Garambawul A Shugabancin Jam’iyyar APC

RelatedPosts

Arewa

An Yi Wa Arewa  Nisa A Kasar Nan

by Sulaiman Ibrahim
2 hours ago
0

Har yanzu duniyar  Arewacin Nijeriya ba mu dauka duniyar kudu...

Bayanan Sirri

Rashin Tsaro: Shugaba Buhari, Monguno Da Aikin Tattara Bayanan Sirri

by Muhammad
4 days ago
0

Daga Gidado Ibrahim, Tsaro shi ne abu na farko kuma...

NIN

Yadda Za Ka Hada Lambar Wayarka Da NIN Dinka

by Muhammad
6 days ago
0

Daga Ibraheem El-Tafseer, A cikin shekarar da ta gabata ne...

Next Post

An Bukaci Gwamna Lalong Da Ya Yi Garambawul A Shugabancin Jam’iyyar APC

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version