Wanda Ya Fahimci Kasar Sin Ba Zai Ji Tsoron Ta Ba

Daga CRI Hausa,

“Me ya sa kasar Sin ke samun saurin ci gaban tattalin arziki?””Wasu na cewa, wai babu dimokuradiya a kasar, shin gaskiya ne?””Ko kasar Sin za ta haifar da barazana ga sauran kasashe?” Ko kai ma ka taba tunanin wadannan tambayoyi?

A birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, ana gudanar da wani taro mai taken “fahimtar kasar Sin”, inda na yi hira da wasu kwararru ‘yan kasashen waje, kuma dukkansu sun ce, kasar Sin wata dama ce ga duniya, ba barazana ba ce. Amma kafin a yarda da wannan ra’ayi, dole ne a fara fahimtar kasar Sin da farko.

Hakika akwai mutanen da suke tsoron zuwa asibiti, ko kuma yin amfani da wayar salula, saboda wasu na nuna shakku ga wani abu da ba su fahimce su ba. Wasu mutane daga yammacin duniya, na yiwa kasar Sin irin wannan bahaguwar fahimta. Malcolm Clarke, wani mai daukar fina-finai na kasar Birtaniya. Ya bayyana cewa, “mutanen yammacin duniya sun ga tasowar kasar dake nahiyar Asiya. Mutanen kasar ba su yi kama da mu ba, kana yadda suke magana da tunani ba irin namu ba ne. Amma kasar ta zama mai matukar karfin tattalin arziki, abun da ya sa su damuwa.”

Tsarin siyasa na kasar Sin shi ma ya ba mutanen yammacin duniya tsoro, inda suka ba ta taken kasa mai bin tsarin Kwaminisanci, har ma suna kallon tsarin Sin da tsarin tsohuwar tarayyar Soviet iri daya. Amma hakika kasar Sin na ta kokarin kirkiro dabarun mulki, da neman hanyar ta raya kasa da kanta.

Ban da wannan kuma, kasashen yamma na da al’adar shafawa kasar Sin kashin kaza. Wiliam Brown, wani farfesa na jami’ar Xiameng ne, kana dan kasar Amurka ne, wanda ya ce, tun shekaru fiye da 100 da suka wuce,Turawa ‘yan mulkin mallaka sun fara yada jita-jita game da kasar Sin, don neman ta da rikici a kasar, ta yadda za su mallaki kasuwanni da albarkatun kasar. Har zuwa yanzu, wasu Amurkawa, da na sauran kasashe, suna a kan wannan al’ada, inda suke yada karairayi cewa, wai babu dimokuradiya a Sin, wai kasar na keta hakkin dan Adam, da muzgunawa Musulmai. Hakika wadannan matsaloli ne da ake samu a kasashensu, amma sun ce a kasar Sin ne.

Idan har aka fahimci al’adu, da tarihi na kasar Sin, za a fahimci cewa, abun da ya sha bamban da sauran kasashe a cikin halayyar kasar Sin shi ne, dalilin da ya sa kasar ke samun saurin ci gaban tattalin arziki. John Whyte, shugaban asusun hadin gwiwar Amurka da Sin ne, wanda ya gaya mana cewa, tarihin kasar Sin ya haifar da wata al’ada a kasar: Idan mai mulki ya kula da moriyar jama’a, to, jama’a za su ba shi goyon baya. Wannan al’ada ta yi tasiri kan harkokin siyasan kasar na yanzu, inda gwamnatin kasar ke kula da aikin ba da nagartaccen jagoranci, yayin da jama’ar kasar suke baiwa gwamnati cikakken goyon baya, kana kowa da kowa zai yi kokarin gudanar da ayyukansu. Dalilin da ya sa kasar Sin ke samun ci gaba, shi ne domin dukkan mutanen kasar na kokarin janyo kasar zuwa bangare daya, wato zuwa gaba.

Wani dalili da ya sa kasar ta samu saurin ci gaba shi ne, kasar Sin ta yarda da manufar zama tare da sauran kasashe cikin lumana. Ba ta taba koyon dabarun kasar Amurka na jibge sojoji a kasashen fiye da 100 ba. Kana a lokacin da kasashen yammacin duniya ke kokarin yayata tsarin dimokuradiyarsu, kasar Sin ba ta ce tsarinta ne kawai daidai, kuma na saura yana kuskure ba. Yayin da wasu kasashe masu sukuni suke yin amfani da fifikonsu a fannin kimiya da fasaha, da hada-hadar kudi, wajen kwace kudi a kasashe daban daban, kasar Sin tana kokarin aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, da raya al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta daukacin dan Adam, inda take raba damammakin samun ci gaban tare da sauran kasashe.

Kafin a fahimci ma’anar tasowar kasar Sin, kasar Amurka ba za ta ji dadi ba, domin ta riga ta saba da matsayinta na yin babakere a duniya, yayin da kasashen Turai su ma suke bukatar daidaita tunaninsu, don fuskantar wannan kasar dake nahiyar Asiya, wadda ke iya takara ko kuma hadin gwiwa da su. Kana game da kasashen Afirka, tasowar kasar Sin wata dama ce ta samun ci gaban tattalin arzikinsu. (Bello Wang)

Exit mobile version