Ahmad Fagam Na CRI">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Wane Alheri Takardar Bayanan Sin Ke Dauke Da Shi Game Da Huldarta Da Kasa Da Kasa?

by Ahmad Fagam Na CRI
January 11, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Wane Alheri Takardar Bayanan Sin Ke Dauke Da Shi Game Da Huldarta Da Kasa Da Kasa?
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Masu hikimar magana na cewa, “zo ka ci abinci ya fi abincin dadi”. A lokuta da dama gwamnnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta sha nanata kudirinta na kyautata cudanya da kasa da kasa, da ci gaba da taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, gami da bayar da babbar gudunmawa ga ci gaban al’ummar duniya. A karshen wannan mako ne gwamnatin Sin ta fidda takardar bayanai game da batun ci gaban huldarta da kasa kasa. Takardar bayanan, mai taken “Ci gaban huldar kasar Sin da kasashen duniya a sabon karni,” ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ne ya fidda takardar. Mai kunshe da babi takwas, takardar bayanan ta fayyace ra’ayoyin kasar Sin game da ci gaban hadin gwiwarta da kasa da kasa a sabon zamanin da muke ciki, da matakan da kasar ta riga ta dauka, da kuma shirye-shiryenta dake tafe a nan gaba.

A cewar takardar, kasar Sin tana ci gaba da kara matsayin hadin gwiwarta da kasashen duniya, tana kara bayar da fifiko ga kasashen dake da karancin ci gaba a nahiyoyin Asiya da Afrika, da kuma kasashe masu tasowa dake karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”. Tun bayan gabatar da shawarar“ziri daya da hanya daya”, kasar Sin take cigaba da bunkasa kulla alakarta da bada gudunmawa ga fannonin tsara manufofin ci gaban bil adama, da samar da kayayyakin more rayuwa, da cinikayya, da hada hadar kudi, da kyautata alaka a tsakanin mutum da mutum bisa ga bukatun dake shafar kowane bangare na kasashen duniya, da samar da yanayi da damammaki don bunkasa ci gaba da samar da makoma mai haske ga dukkan bil adama a karkashin hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”. Ko da yake, wannan ba bakon al’amari ba ne domin kuwa, a lokuta da dama shugaba Xi Jinping ya sha nanata yin kira da a hada hannu domin gina duniya mai wadata. Shugaban ya sha bayyana cewa kasar Sin ta shirya yin aiki da sauran kasashen duniya wajen gina duniya mai wadata da cin gajiyar cigaba na bai daya don samar da makoma mai kyau ga dukkan bil adama. (Ahmad Fagam)

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Matasan Kauyen Dake Kan Hayi Sun Koma Garinsu

Next Post

Gobarar NIS Ba Ta Shafi Muhimman Bayanai Ba—Babandede

RelatedPosts

Kyautata Alakar Sin Da Amurka Zai Taimakawa Gwamnatin Biden Wajen Shawo Kan Manyan Kalubale

Kyautata Alakar Sin Da Amurka Zai Taimakawa Gwamnatin Biden Wajen Shawo Kan Manyan Kalubale

by Ahmad Fagam Na CRI
24 hours ago
0

Kamar yadda muka sani, shugaban Amurka na 46 Joe Biden,...

Jarin Waje Da Aka Zuba A Sin Ya Kafa Wani Sabon Matsayi

Jarin Waje Da Aka Zuba A Sin Ya Kafa Wani Sabon Matsayi

by Ahmad Fagam Na CRI
24 hours ago
0

Jiya Laraba, ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ta fidda bayanin...

Akwai Tabbaci Ga ‘Yancin Bin Addini Na Al’ummar Kabilu Daban Daban Na Jihar Xinjiang

Akwai Tabbaci Ga ‘Yancin Bin Addini Na Al’ummar Kabilu Daban Daban Na Jihar Xinjiang

by Ahmad Fagam Na CRI
1 day ago
0

Kakakin ofishin watsa labaru na gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur...

Next Post
Gobarar NIS Ba Ta Shafi Muhimman Bayanai Ba—Babandede

Gobarar NIS Ba Ta Shafi Muhimman Bayanai Ba—Babandede

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version