Kwamared Sunusi Mailafiya,
alimailafiyasunusi@gmail.com – +22790806197
“Zamu kulle tashoshin jiragen sama da na kasa, zamu rufe iyakokin kasar mu, sannan zamu hana zirga-zirga da duk wani taron al’umma na zuwa wani lokaci”. Wannan sune kalaman da suka fi jan hankali a shekarar data gabata daga kasashe da dama, hakan kuwa ya faru ne sakamakon ɓarkewar cutar Covid-19, cutar data game duniya, kuma ta yamutsa tattalin arzikin duniya. Cuta ce wacce aka fara samunta a kasar Sin, wacce a hankali ta kewaye duniya, ta kuma zamo dalilan da suka takaita zirga-zirga a kasashen duniya, hakan ya zamanto dalilan kulle makarantu, guraren shaƙatawa, guraren sana’o’i, da sauran guraren shige-da-fice wanda shine abu mafi muni da ya zamanto harkokin kasuwanci, da kudaden shiga na kasashe da dama ya girgiza.
Tabbas akwai darussa masu yawa daya kamata Nijeriya ta amfana, musamman saboda wannan annoba tazo a dede lokacin da kasar ta amince da mafi karancin albashi na dubu talatin, kwatsam kuma sai ga cutar da ta janyo wasu jihohin ba zasu iya cigaba da biyan wannan albashi ba. Wannan ya nuna mana yadda dogaro da man fetur zai iya bawa tattalin arzikin Kasar nan matsala nan gaba. Wannan yar manuniyace dake nuna cewar man fetur bai kamata ya kasance shine kadai dogaron arzikin kasarmu ba, domin karyewar sa a kasuwar duniya ya janyo rikicewar abubuwa da dama.
Darasi na biyu daya zama dole Kasar nan ta ilmanta a shekarar data gabata itace harkar ilimi. Tun daga makarantun Firamare har Jami’o’i sun kasance a rufe, wanda hakan ke nufin manhajar karatun ta canza, kowa ya zauna a gida, ga matasa da yawa na gaba da sakandare babu sana’a, hakan ya nuna dole ne Gwamnatin Kasar nan ta mayar da ilimin Kasar nan bisa tsarin karatun tafi-da-gidanka ta amfani da na’ura mai kwakwalwa. Wannan ya zama wajibi idan har ana son samar da ilimi mai nagarta, sai an koyawa ɗalibai tun daga firamare amfani da na’ura mai kwakwalwa (computer), ko da ace irin wannan yanayin ne, wanda zai bada damar amfani da tsarin a matsayin kar-ta-kwana, wanda hakan zai dakile rashin cigaba da tsarin karatun da aka dauko, wanda hakan ya janyo rikicewar karatun fannoni da dama. Kasashe da dama sunci gaba da daukan darussan su a gida, duk da kullen korona da ake a Kasashen, wanda hakan ya bawa ɗalibai dama wajen cigaba daga inda aka tsaya, kuma ko kadan hakan bai shafi kwazon su ba, to amma abin bakinciki mu anan Nijeriya yadda hakan ya janyo ɗalibai sukai ta gararamba a gari, batare da wani tudun dafawa ba. Dole ne Ma’aikatar ilimi ta kasa (Ministry for Education), ta samar da wannan tsarin, musamman a makarantun Firamare da Sakandare.
Darasi na uku mafi mahimmanci shine yadda tsaro ya sukurkuce matuka a wannan lokacin na kulle (Lockdown), sakamakon yadda matasa suke zaune ba aikin yi, wanda hakan ya janyo zanga-zangar #EndSars. Dole ne Gwamnati ta samar da ingantaccen tsaro wanda zai iya kula da shige-da-fice kowa a irin wannan lokaci. Ba kuma kawai samar da jami’an tsaro ba, amfani da matasa wajen dakile duk wani laifi a cikin al’umma, umguwanni da kuma jihohi. Dole ne Gwamnati ta sanya matasa a cikin kwamitutuwa na tsaro da dama wanda hakan zai dinga samar da wani bayanan sirruka na masu kokarin aikata ta’addanci, amma rashin jan matasan a jiki, ga kuma yajin aikin Jami’o’i, zai kuma zama ingiza mai kantu ruwa ga matasan wajen kokarin aikata laifuffuka, musamman adede lokutan da ta’addancin Boko haram, masu garkuwa da mutane da kuma tasirin adawar siyasa ke karuwa a Kasar.
Yanzu dai mun ga shekarar Corona wacce ta kasance hantsi leka gidan kowa, kuma ta janyo durkushewar tattalin arziki. Yanzu lokaci ne na ganin duk wasu matsaloli an kawar dasu. Duk da cewa a yanzu haka cutar ta kuma dawowa a karo na biyu, amma kuma batada tasirin shekarar data gabata. Gwamnati ya kamata ta karanci abubuwan da suka faru a baya, ta samu hanyoyin kariya da suka dace a wannan lokacin. Babu maganar lockdown, kulle makarantu da yanzu haka an rasa gane takamaimai lokutan komawa, ta kuma san hanyoyin da zata bi wajen yin allurar rigakafin wannan cuta ta Covid-19.
Allah Ubangiji Ya cigaba da kare Kasarmu da dukkanin wani mugun nufi. Ya kawo mana zaman lafiya mai ɗorewa, ya kuma kawo mana karshen wannan ibtila’in cuta na Coronabirus. Ameen.