Wane Ne Arda Guler Mai Lakabin ‘Sabon Messi A Real Madrid’?
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wane Ne Arda Guler Mai Lakabin ‘Sabon Messi A Real Madrid’?

byAbba Ibrahim Wada
2 years ago
Messi

Za a iya cewa a baya an ga Messin Iran da Messin Jamus da Messin Scottland da wasu masu yawa amma yanzu lokaci ne da za a ce barka ga Messin Turkiyya, wato Arda Guler.

Yaron da ake kwatantawa da gwarzon Argentina Lionel Messi yanzu ya sha kan mafi yawan matasan ‘yan wasa, musamman wadanda suka kware wajen yanka da wasa da kwallo, wani abu da dan wasan mai shekara 18 ya kware a kai.

  • Yau Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Emefiele Ya Shigar
  • Cire Tallafin Fetur: Tinubu Na Neman Sahalewar Majalisar Wakilai Don Samar Da Kudaden Rage Radadi

Kawo yanzu babu wani dan wasa da ya kai inda matashin ya kai, cikin wadanda suka gabace shi kamar su Sardar Azmoun da Marko Marin da kuma Ryan Gauld. Duka babu wanda ya yi kusa.

Akwai kwarin gwiwar matashin dan wasan mai basira Guler zai iya zama daya daga cikin fitattun ‘yan wasan da za su yi suna a duniya, a yanzu kuma kaddara na neman kai shi gasar da mutumin da ake kwatanta shi da shi ya buga a kungiyar da ya yi adawa da ita.

Tun daga lokacin da ya fara buga wa tawagar Fenerbache wasan farko, manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai suka fara bayyana maitarsu a fili kan matashin dan wasan.

Kungiyar da Messi ya buga wa kwallo Barcelona ta nuna muradinta a fili na daukar dan wasan, kuma shugaban kungiyar Joan Laporta ya aika daraktan wasannin kungiyar Deco domin ya tattauna kan batun.

Sai dai abu ne mara dadi ga kungiyar ta Barcelona ganin yadda dan wasan ya zabi babbar abokiyar hamayyarta a matsayin wadda yake so maimakon ita, ya koma Real Madrid a matsayin mafi basira daga yankinsu da ya buga kwallo a Bernabeu.

Wani abu da ya burge masu dillancin dan wasan shi ne yadda kungiyoyi suka yi ca a kan dan wasan – irin su Bayern Munich da Borussia Dortmund da Paris St-Germain da kuma uku daga Premier Ingila Arsenal da Manchester United da Newcastle.

Rahotanni sun bayyana cewa an ta taya shi yuro milyan 17.5, abin da ya sanya ba shi damar kara buga wasanni masu yawa a kungiyarsa, kuma wannan wani dan wasa ne da aka amince ya fara yi wa babbar kungiyarsa wasa a shekaru 16, inda ya shiga a matsayin canji a minti na 66 a wasan da Fenerbache ta yi nasara a HJK Helsinki 1-0 a wasan farko na neman shiga gasar Europa a ranar 19 ga watan Agustan 2021.

Yaron da ya bayar da kwallo aka ci a wasan Super Lig na farko, ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci kwallo a wasan 5-2 a ranar 13 ga watan Maris 2022, kwana 16 daga shigar sa shekara ta 17.

Duka dai, yana da kwallo bakwai ya kuma ba da bakwai an ci a minti 1,187 na Super Lig da ya buga, ma’ana ya yi wani abu na cin kwallo a kowanne minti 85 na wasan kamar yadda kididdiga ta nuna.

Ba shi lamba 10 da aka yi a Fenerbache na nuni da yadda ya samu shiga cikin kungiyar sosai saboda rigar da a baya manyan ‘yan wasa irin su Tuncay Sanli da Robin ban Persie da kuma Mesut Ozil, mafi mahimmanci shi ne Aled gwarzon kungiyar ta Istanbul wanda ya ci kwallo 171 ya ba da 136 aka ci a wasa 344 tsakanin 2004 zuwa 2012 kuma aka yi mutum-mutuminsa a wani wuri a garin.

Idan har za’a iya kwatanta Guler da wani dan wasa shi ne tsohon dan Brazil din, a karshe, ba ya fargabar gwada wani abu, misali shi ne kwallo da ya ci daga wajen yadi na 20 a wasan da suka ci 5 -1 a watan Janairu da Kasimpasa.

Ya yi wasansa na farko a kasa a wasan sada zumunta da suka yi da Jamhuriyar Czech a ranar 19 da watan Nuwamba 2022, ya ci kwallonsa ta farko a watan Yunin nan da ya gabata, a wasansa na hudu.

Abin tambayar a nan shi ne, wannan lokacin shi ne mafi dacewa ga dan wasan ya tsallaka mataki na gaba a rayuwar kwallonsa? Tsohon dan wasan gaban Fenerbache, Ozil, wanda Guler ya gada, wanda ya tafi Real Madrid, yana da shekara 21, ya shawarci matashin da ya kara shekara guda a Turkiyya domin kara samun gogewa.

Da alama dai wannan cinikin da Real Madrid ke yi tana kara neman hada wasu sabbin zubi na Galacticos saboda akwai ‘yan wasan gaba masu tashe, Binicius Jr da Rodrygo da suke a kungiyar dama.

Idan har shirin Real Madrid ya tafi yadda take so kungiyar za ta cika da matasa kuma hazikan ‘yan kwallo, irin su Aurelien Tchoumameni da Eduardo Camabinga da Jude Bellingham a tsakiyar kungiyar sai kuma watakila Kylian Mbappe, idan har ya koma kungiyar a yanzu ko kuma a karshen kakar nan da za’a fara wato shekara ta 2024.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane
Wasanni

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

October 7, 2025
Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni
Wasanni

Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni

October 6, 2025
Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar
Wasanni

Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar

October 6, 2025
Next Post
Wang Yi Ya Bukaci Amurka Da Ta Dauki Kwararan Matakai Don Dawo Da Alakar Sin Da Amurka Kan Turbar Da Ta Dace       

Wang Yi Ya Bukaci Amurka Da Ta Dauki Kwararan Matakai Don Dawo Da Alakar Sin Da Amurka Kan Turbar Da Ta Dace       

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version