Connect with us

SIYASA

Wane Ne Hon. Mal Samaila Suleiman (Dujiman Zazzau)?

Published

on

Hon. Malam Sama’ila Sulaiman (Dujiman Zazzau) an haifeshi ranar 03/02/1981, a Garin Zazzau dake Jihar Kaduna. ya yi karatun Firamare a makarantar ‘Kaduna Capital School’ daga shekarar 1988 zuwa 1993, sannan ya zarce zuwa makarantar sakandire ta ‘Kaduna Capital School’ daga 1994 zuwa 1999.

Dujiman Zazzau ya yi karatun gaba da Sakandire a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake Jihar Bauchi, inda ya kammala digirinsa na farko daga shekarar 2001 zuwa 2006 a fannin Kere-Kere wato ‘Mechanical Engineering, ya kuma zarce zuwa jami’ar Ahmadu Bello (ABU) dake Zaria, daga 2008 zuwa 2009, inda ya hada digiri na biyu a fannin Ilimin/Nazarin Sulhu, Zaman Lafiya da Dangantaka Tsakanin Kasashe (MCPSS.

Dujiman Zazzau, ya kasance mutum mai hazaka matuka hakan yasa ya rike mukamai masu muhimmancin gaske a mabanbantan wurare, daga cikin mukaman da ya rike akwai:-

Ya rike matsayin mai horarwa, a ma’aikatar matatar man fetur ta Kaduna (K.R.P.C) daga 2005 zuwa 2006.

Ya rike matsayin mai horarwa a ma’aikatar N.L.N.G a 2007-2008.

Ya rike matsayin manaja a ma’aikatar ‘Prime Studios’ dake Abuja daga 2008 zuwa 2009.

Ya yi aiki da ma’aikatar ‘Energy Commission of Nigeria’ daga 2009 zuwa 2010.

Basaraken bai tsaya ga aikin gwamnati kadai ba, ya fantsama cikin harkar kasuwanci, inda ya kasance shugaban katafaren kamfanin nan na ‘Guda Bision & Associate Ltd’, kamfanin da ya zama zakara a bangaren zuba hannayen jari a masana’antun da suka shafi harkar noma da kiwo.

Baya ga harkar kasuwanci, Dujiman Zazzau, ya kasance gawurtaccen Dan siyasa mai kishin al’ummar sa, ya yi takarar Shugaban Karamar hukumar Kaduna ta Arewa a karkashin Inuwar tsohuwar jam’iyar ‘Congress for Progressibe Change’ (CPC) a shekarar 2010, inda yayi nasarar cin zabe a shekarar 2012, bayan samun gagarumar rinjayen kuri’un al’umma.

Dujiman Zazzau, yayi takarar Dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa a Jam’iyar APC, a shekarar 2014, inda ya samu nasarar lashe zabe, ya rike mukamin mataimakin shugaba kwamitin kula da miyagun kwayoyi, kafin daga bisani aka nada shi shugaban kwamitin kula da ma’adanan kasa a majalissa.

Dujiman Zazzau, ya kuma sake samun nasarar lashe zaben kujerar dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa a babban zaben 2019. A wannan karon, shi ne shugaban kwamitin kula da aiyuka na musamman, kwamitin da ke kula da fadar shugaban kasa, kwamitin kula da iyakoki da kula da shige da ficen albarkatun kasa.

Gwagwarmayar da Malam Sama’ila Sulaiman, yayi da kuma himdamar sa ga al’umma, hakan yasa ya tsere ma sauran takwarorin sa ta fannin himdatawa al’umma da kuma kwarewa wajen sauke nauyin jama’ar da yake wakilta.
Advertisement

labarai