Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Wane Ne Mawallafin Littafin Bari-Biba?

by
2 years ago
in Bincike
4 min read
Wane Ne Mawallafin Littafin Bari-Biba?
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Al-Arabiyyatul Jadeeda fi Najeriya (wanda aka fi sani da Bari-Biba) fitaccen littafin lugga ne da ya shahara a kasar Najeriya da kewayenta. Abu ne mai matukar wuya, mutum ya ta shi a Najeriya (musamman a yankin Arewa) kuma ya yi karatun addini a Islamiya amma bai san wannan littafi ba.

Mutane da dama da su ka karanta littafin ba su san wane ne mawallafin wannan littafin ba, illa dai kawai sunan littafin da su ka sani. Hatta a kafafen sada zumunta na soshiyal midiya, hankali jama’a ba ya kai wa ga tambayar kansu shin wane ne wannan babban gwarzon da ya hidimtawa addini musulunci ta hayar rubuta wannan littafin? Sai dai kawai wasu da su ke sanya hoton littafin da cewa, “Ko Bari da Biba sun yi aure zuwa yanzu?”
Duk da cewa a bangon littafin babu sunan mawallafin, amma a shafin farko na cikin littafin an sanya sunan. Wanda kuma hakan bai ja hankali daliban ilimi wajen bincikar tarihin wanda ya wallafa littafin ba. Yau kimanin sama da shekaru Arba’in da samuwar wannan littafi mai albarka (domin an fara buga shi a 1979), cikin yardar Ubangiji ga shi yau zan yiwa ‘yan uwana almajiran ilimi da mana sauran al’ummar Najeriya da kewayenta dan takaitacce bayani game da tarihin mawallafin wannan littafi mai albarka.

Wane Ne Mawallafin Bari-Biba?

Labarai Masu Nasaba

Bincike: Shin Da Gaske An Kama Limamin Makkah, Shaikh Sudais?

Cin Hanci Da Rashawa Ya Zama Ruwan Dare Gama Duniya A  Najeriya

ADVERTISEMENT
Sarkin Kazaure, Mai Martaba (Marigayi) Alhaji (Dr.) Hussaini Adamu (mahaifin Sarkin Kazaure na yanzu). Mawallafin littafin Bari wa Biba

Wanda ya wallafa wannan littafin na Al-Arabiyyatul Jadeeda fi Najeriya shi ne, Sarkin Kazaure, Mai Martaba (Marigayi) Alhaji (Dr.) Hussaini Adamu (mahaifin Sarkin Kazaure na yanzu).
Watakila mai karatu ya ce, ai sunan mawallafa uku ne a shafin farko na cikin littafin. Hakika haka ne cewa, a shafin farko an sanya sunayen mutane gudu uku, wato Dakta Ahmad Hakiyulhaliyu da Salim Hakim da kuma Alhaji Hussaini Adamu, amma duk da haka, bincikena ya tabbatar mana da Hussaini Adamu ne ya fara rubuta littafin. Bayan ya rubuta littafin ya shiga cikin al’umma, Doktor Ahmad da Salim su ka ba shi shawarar ya kamata a fadada littafin ta yadda zai zama mafi sauki ga wajen koyon harshen Larabci (musamman ga yara kanana). Wannan yasa su ka hadu su uku su ka sake fadada littafin har ya zama daga na daya zuwa na shida. Amma bugun fari da aka aka yi, Hussaini Adamu ne shi kadai ya rubuta. Duk da haka kofa a bude ya ke ga duk wanda ya ke da wani karin gaske ko wata masaniya ko karin bayani akan ba Hussaini Adamu ba ne ya fara rubuta littafin shi kadai, zai iya tura mana bayanan da ya ke da shi ta email din Mohammedbalagarba2018.com ko kuma ta lambar wassap 08098332160)
An haife Hussaini Adamu a garin Roni da ke gundumar masarautar Kazaure (ba mu samu sahihin shekarar da aka haife shi ba). Amma wasu sun ce a shekarar 1933 aka haife shi. Ya yi karatun Furamare a Elementary ta Kazaure, daga nan ya tafi Middle da ke Kano. Bayan nan, ya halarci makarantar nazarin harshen Larabci, wato School of Arabic studies (S.A.S) da ke nan Kano.
Daga nan ya tafi Ingila domin karo karatu da yin nazari a jami’ar London. Bayan ya dawo gida Najeriya ya fara aiki a jihar Arewa a matsayin jami’i mai kula da fannin ilimi, daga bisani kuma ya koma koyarwa a makarantar (S.A.S).
Ya rike mukamin mai kula da makarantun Furamare da Kwalejojin ilimi na Arewa a 1963 zuwa 1968. Bayan littafin Al-Arabiyyatul Jadeeda fi Najeriya, ya rubuta litattafai kamar su:
1. Jagoran Musulunci
2. Fassarar littafin ibada da hukunce-hukunce (Daga harshen Hausa zuwa Larabci).
Ya zama Sarki a shekarar 1994. Sarki Hussaini yana daya daga cikin mafi soyuwar sarakunan da su ka mulki masarautar Kazaure. Domin ya kasance sananne malamin addinin musulunci da kuma kwarewa musamman a bangaren Fikhu da lugga. Bayan haka, shi shugaba ne a fanni ilimi, raya karkara, wanzar da zaman lafiya da ayyukan addini. Yana daya daga cikin manyan marubuta wadanda su ka yi zamani da su Isa Kaita da Sa’adu Zungur da Abubakar Imam da dai sauransu. Malumtarsa ta yi gaggarumar taimakawa gurin cigaban addinin musulunci da ilimin zamani a kasar Hausa.
Shi ne sarki na tara a jinsin Fulani cikin sarakunan da su ka mulki Kazaure. Kamar yadda ya zo cikin jadawalin sarakunan Kazaure, kamar haka:
1. Ibrahim dantunku. Shi ne sarki na farko a jinsin Fulani. Ya yi sarauta daga shekarar 1819 zuwa 1824.
2. Dambo dan dantuku. Ya hau karagar mulki a 1824, an kashe sa a 1857.
3. Muhamman Zangi dan Dambo. Ya hau karagar sarauta a 1857, ya rasu 1886.
4. Muhamman Mayaki dan Dambo. Ya hau karagar sarauta a 1886, ya ajiye sarautar saboda tsufa a 1914.
5. Muhammadu Tura dan Muhamman Mayaki. Ya hau karagar sarauta a 1914, ya rasu 1922.
6. Ummaru Na’uka dan Muhammadu Tura. Ya hau karagar sarauta a 1922, ya rasu 1941.
7. Adamu dan Abd Al-Mumini. Ya hau karagar sarauta a 1941, ya rasu 1968.
8. Ibrahim dan Adamu. Ya hau karagar sarauta a 1968, ya rasu 1994.
9. Hussaini Adamu (mawallafin Bari-Biba). Ya hau karagar sarauta a 1994, ya rasu 1998.
10. Najib Hussaini Adamu (sarkin Kazaure na yanzu). Ya hau karagar sarauta a 1998 bayan rasuwar mahaifinsa, kuma shi ne sarkin Kazaure har zuwa yau.
Marigayi Alhaji Hussaini yana daga cikin wadanda su ka samar da Jama’atul Nasril Islam. Hakan ya na bayyana mana abubuwa da dama game da martabar sa cikin jerin Khalifofin Sakkwato.
Shi shugaba ne da sunansa ya zama abin martabawa sakamakon kwazonsa da kuma kasancewarsa gagara misali a cikin al’umma.
Ya rubuta littafin Al-Arabiyyatul Jadeeda fi Najeriya ne domin karfafawa al’ummar Arewa gwiwa (musamman matasa da yara kanana) wajen koyon harshen Larabci a saukake. Domin ya rubuta littafin tun yana matashi. Ya mulki masarautar Kazaure na tsawon shekarau hudu (daga 1994 zuwa 1998). Ya rasu a daren Asabar da misalin karfe biyu cikin watan Oktoba, a shekarar 1998. Ya bar mata uku, da ‘ya’ya goma sha shida da jikokin Ashirin da biyar (a lokacin).
Daga cikin ‘ya’yansa akwai Sarkin Kazaure na yanzu, Maimarta Alhaji Najib Hussaini Adamu, da Hajiya Rabi Hussaini Adamu Ishak (tsohuwar kwamishiniyar ilimi ta jihar Jigawa) da Dokta Hassana Hussaini Adamu (tsohuwar kwamishiniyar muhalli) da Hajiya Amina Bala Zakari (tsohuwar shugabar rukon kwarya a hukumar zabe ta kasa) da ministan albarkatun ruwa Suleman Hussaini Adamu.
Hakika Sarki Hussaini ya yi matukar kokarin da za a dade a na tunawa da shi bisa gudunmawar da ya bayar don karfafan al’ummar kasar Hausa a fannoni da dama. Wannan yasa a shekarar 1998 aka sauyawa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kazaure suna izuwa Hussanin Adamu Federal Polytechnic Kazaure.
Mu na addu’ar Ubangiji Allah ya saka masa da mafifincin alheri shi da wadanda su ka ka yi wannan jan aikin, ya gafarta masu, ya albarka bayansu, ya kara karfafa gwiwan masu irin wannan tunanin nasu a yankin Arewa, yasa Arewa ta zauna lafiya, Amin.

Daga dan uwanku Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 08098331260.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Ina Mafita Forum Ta Tallafa Wa Marayu Da Iyayen Marayu A Zariya

Next Post

Najeriya Ta Fita Daga Kangin Mulkin Mallaka Ta Fada Na ’Yan Boko – Sani Brothers

Labarai Masu Nasaba

Bincike: Shin Da Gaske An Kama Limamin Makkah, Shaikh Sudais?

Bincike: Shin Da Gaske An Kama Limamin Makkah, Shaikh Sudais?

by
9 months ago
0

...

Cin Hanci Da Rashawa Ya Zama Ruwan Dare Gama Duniya A  Najeriya

Cin Hanci Da Rashawa Ya Zama Ruwan Dare Gama Duniya A  Najeriya

by
2 years ago
0

...

Matakai Da Yanayin Cutar Korona

Matakai Da Yanayin Cutar Korona

by
2 years ago
0

...

’Yan Mowa Da ’Yan Bora A Rukunin Kofin Zakarun Turai!

Binciken Shekaru 10: Abubakar Buhari Bai Kashe Mahaifinsa Ba

by
2 years ago
0

...

Next Post
Najeriya Ta Fita Daga Kangin Mulkin Mallaka Ta Fada Na ’Yan Boko – Sani Brothers

Najeriya Ta Fita Daga Kangin Mulkin Mallaka Ta Fada Na ’Yan Boko – Sani Brothers

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

 

Loading Comments...
 

    %d bloggers like this: