Abba Ibrahim Wada" />

Wane Ne Sabon Kociyan Chelsea, Thomas Tuchel?

Chelsea ta nada tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain Thomas Tuchel a matsayin sabon kocinta inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar watanni 18 bayan doguwar tattaunawa da wakilan mai koyarwar.

Tuchel, mai shekara 47, ya lashe kofin League biyu, da kofin kalubale na Faransa da a shekaru biyu da rabi da ya yi a PSG kuma Chelsea ta kori Frank Lampard bayan watanni 18 yana jan ragamar inda har wasan karshe ya kai kungiyar na gasar cin kofin kalubale na FA.
Tuchel ya kasance koci na 11 da mai Chelsea attajirin Rasha Roman Abramobich ya nada tun da ya sayi kungiyar a shekarar 2003 kuma Tuchel Shi ne ya jagoranci wasan Chelsea a Stamford Bridge a jiya Laraba da ta yi da Wolbes a gasar Premier.

kungiyoyin da Tuchel ya horar
FC Augsburg II 2007-2008
Mainz 05 2009-2014
Borussia Dortmund 2015-2017
Paris Saint-Germain 2018-2020
Sannan Tuchel ya fara fito da kansa a shekarar 2009 lokacin da ya maye gurbin Jurgen Kloop a kungiyar Mainz a gasar Bundesliga haka kuma shekara shida tsakanin ya kara maye gurbin Kloop a Borussia Dortmund a shekarar 2015.
Aikin da Tuchel ya yi ne a Dortmund ya sa aka san shi da kokarin da yake a fagen horar da kwallon kafa kuma matashi da ta kai Paris St Germain ta bashi aiki a shekarar 2018 inda a nan ya lashe kofuna.

Salon Tuchel a kwallon kafa
Tuchel ya yi amfani da salon 4-3-3 a kungiyar Borussia Dortmund da kuma kungiyar PSG, idan ta kure masa yakan koma wa salon 3-5-2 ko kuma 5-3-2 sannan kawo yanzu Tuchel idonsa ya bude a salon horar da kwallon kafa, har da gasar zakarun Turai duk da cewa bai taba lashewa ba sannan duk kungiyar da ta dauke shi ya zama wajibi ta yi hakuri ta kuma bashi lokacin da zai samar da sakamakon da ake bukata.

Shin wane ne Thomas Tuchel?
An haifi Thomas Tuchel ranar 29 ga watan Agustan shekarar 1973 a Krumbach, dake kasar Jamus sannan tsohon mai tsaron baya ne, ya fara buga wasa a matashi a kungiyar TSb Krumbach a shekarar 1979 zuwa 1988 sannan ya buga wasa a kungiyar FC Augsburg a shekarar 1988 zuwa 1992
Tuchel ya ci gaba da wasa a matakin kwararren dan kwallo a kungiyar Stuttgarter Kickers a shekarar 1992 zuwa 1994 da kuma kungiyar kwallon kafa ta SSb Ulm, wadda itama ya buga mata wasa a shekarar 1994 zuwa 1998.
Tuchel bai dade yana buga kwallo ba, sakamakon rauni da ya yi a gwiwarsa da ta kai ya yi murabus yana da shekara 25 a duniya kuma daga nan ne ya fada sana’ar horar da kwallon kafa, wanda ya fara da karamar kungiyar Stuttgart.

Bajintar da Tuchel ya yi a kungiyar PSG:
Mai koyarwa Thomas Tuchel ya ja ragamar kungiyar Paris St Germain wasanni 127, wanda ya yi nasara a wasanni 95 da canjaras 13 aka doke shi a fafatawa 19 sannan a lokacin da ya ja ragamar PSG ta ci kwallo 337 aka zura mata 103 a raga.
A kakar wasa biyu da rabi da Tuchel ya yi a PSG ya taka rawar gani, wanda ya lashe kofuna shida har da gasar rukuni-rukini ta kasar Faransa wato Ligue 1 guda biyu da gasar Coupe de France da Coupe de la Ligue da kuma Trophees des Champions biyu a Faransa.
Sannan a kuma kakar wasa ta 2019 zuwa 2020 Tuchel ya kai PSG wasan karshe a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League, wanda Bayern Munich ta lashe bayan ta doke su daci daya babu ko daya.
Cikin watan Disamba aka salami Tuchel daga aiki a lokacin da PSG ke ta biyu a teburin gasar Faransa da tazarar maki daya tsakaninta da Lyon mai jan ragama wanda hakan yasa ya dauki lokaci bashi da aiki sannan kuma PSG din tam aye gurbinsa da tsohon kociyan Tottenham, Mauricio Pochettino.

kwazon da Tuchel ya yi a Borussia Dortmund:
Tuchel ya ja ragamar wasanni 107 ya yi nasara a wasanni 67 da canajaras 23 aka doke shi sau 17 sannan a lokacinsa Dortmund ta ci kwallo 251 aka zura mata guda 115 a raga bugu da kari kakar wasa biyu da ya yi a Dortmund ya ci kofi daya DFB Pokal a shekarar 2017.
Har ila yau Tuchel ya kuma yi na biyu a gasar Bundesliga a kakar farko da ya ja ragamar kungiyar sannan ya kuma kai wasan kuarter final a Europa League da kuma Champions League a Dotmund.

Shin ko zai kai labari a gasar Premier League kuwa?
Gasar Premier tana cike da kalubale ta ko ina tun daga horarwa da ‘yan wasa da wasannin hamayya a kowanne mako ga kuma cutar korona da ta maida hannun agogo baya sai dai za’a iya cewa rike kungiyar kwallon kafa ta PSG zai taimaka masa wajen iya buga babban wasa saboda ya buga da manyan kungiyoyi a gasar cin kofin zakarun turai.
Duk da cewa babu wasannin hamayya da dama a kasar Faransa wanda hakan zaisa ya kasa jure yawan wasannin adawa da manyan wasanni idan akayi la’akari da kungiyoyin da suke neman lashe gasar firimiyar Inagila yanzu wadanda sun kai kungiyoyi shida sannan kuma ko gasar Europa ma yanzu a Ingila ana kai ruwa rana kafin a samu kungiyar da zata samu tikitin zuwa.

Exit mobile version