Wane Ne Sabon Madakin Zazzau, Muhammad Munir Jafaru?

Madakin Zazzau

Daga Idris Umar,

Sabon Madakin Zazzau, Alhaji Muhammed Munir Ja’afaru, OFR, mni, an haife shi ne a ranar 25 ga Maris, 1956, a garin Zariya, da ke Jihar Kaduna. Mahaifinsa kuwa shine Malam Ja’afaru Dan Isyaku, Sarkin Zazzau na 16.

Ya yi karatun firamare dinsa a makarantar L.E.A Primary School Anchau dake Takalafia daga shekarar 1962 zuwa 1968, sai kuma makarantar sakandiren gwamnati ta Zariya daga 1969 zuwa 1973. Daga nan sai College of Art and Science da ke Zariya daga shekarar 1974 zuwa 1976, Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya karanci sashen shari’a daga shekarar 1976 zuwa 1979, Makarantar Shari’a da ke Legas daga shekarar 1979 zuwa 1980 sai kuma National Institute of Policy and Strategic Studies (NIPPSS) dake Kuru a Jos a shekarar 1991.

Tsohon Yariman Zazzau ya yi aikace-aikace da dama a wurare daban-daban da suka hada da koyarwa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga shekarar 1981 zuwa 1983, mai bada shawara kuma mai kula da tsarin doka na Kaduna Co-operative Bank Ltd, ya yi aiki da gwamnatin Jihar Kaduna daga shekarar 1987 zuwa 1990 a matsayin Kwamishinan Kananan Hukumomi da cigaban al’umma, Kamishinan Tattara Bayanai, Harkokin Cikin Gida da Al’adu, Kwamishinan Aikin Gona da Albarkarun Kasa, Amirul Hajj, sannan kuma Shugaban na Kwamitin Jinkai na Prerogatibe and Mercy na jihar.

Ya kasance Sakataren Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Nijeriya daga shekarar 1990 zuwa 1992, Daraktan Nigeria Hotel Limited daga shekarar 1990 zuwa 1992, Babban Daraktan National Maritime Authority dake Legas daga shekarar 1992 zuwa shekarar 1996, Daraktan Kaduna State Property and Debelopment Company daga shekarar 1992 zuwa 1995, daraktan FSB International Bank PLC a Awolowo Road da ke Legas daga shekarar 1993 zuwa 1996.

Ya kuma rike mukamin Daraktan Leasing Company of Nigeria daga shekarar 1994 zuwa 1996, ciyaman na Nigeria Unity Line Abuja daga shekarar 1995 zuwa 1996, ciyaman din Alliance & General Insurance Company daga shekarar 1995 zuwa 1998, ciyaman din NEM Insurance PLC Legas daga shekarar 1998 zuwa 2007.

Sai kuma Mataimakin Shugaba na farko na Kaduna State Chamber of Commerce, Industry, Mines & Agriculture daga shekarar 1998 zuwa 2001, daraktan First Atlantic Bank Limited a Legas daga shekarar 2000 zuwa 2005, shugaban Kaduna State Chamber of Commerce, Industry, Mines & Agriculture daga shekarar 2001 zuwa 2005, Daraktan Apex Bank PLC, Legas daga shekarar 2001 zuwa 2005, ciyaman I.T.C.C Limited Kaduna daga shekarar 2000 zuwa yanzu, ciyaman din National Export Processing Zones Authority, Abuja daga shekarar 2001 zuwa 2004, Sarkin Hanwa, karamar hukumar Sabon Gari daga shekarar 2001 zuwa 2018, Sarkin Basawa, karamar hukumar Sabon Gari daga shekarar 2018 zuwa yau.

Ya rike mukamin mamban gudanarwa na Nigerian Inbestment Promotion Commission daga shekarar 2003 zuwa 2004, daraktan Spectrum Broadcasting (Nig) Abuja daga shekarar 2004 zuwa yau, mamba a taron National Political Reform Conference a shekarar 2005, mataimakin ciyaman na kwamitin amintattu na A.B.U Endowment Fund, daraktan Transnational Corporation of (NIG) Plc daga shekarar 2006 zuwa 2008.

Haka nan ya yi Daraktan NITEL & MTEL daga shekarar 2007 zuwa 2008, ciyaman din Gambo Sawaba Hospital & Dental Centre daga shekarar 2007 zuwa 2008, mamba a majalisar tattalin arzuki ta jihar Kaduna daga shekarar 2008 zuwa 2012, mamba a Nigeria Bision 20:2020 ‘Business Support Group’ a shekarar 2009, mamba a Nigeria Vision 20:2020 ‘Technical Working Group’ a shekarar 2010, mamba a Presidential Committee of Prerogatibe for Mercy daga shekarar 2011 zuwa 2016, mamba a Kaduna State Peace & Reconciliation Committee a shekarar 2012.

Ya yi Amirul Hajj na Jihar Kaduna a shekarar 2012, ciyaman na Peugeot Automobile (PAN Nig Ltd) daga shekarar 2013 zuwa 2020, darakta a Great-Bar Alliance Ltd a shekarar 2014, darakta a Aptics Nigeria Limited a shekarar 2014, darakta a ELYSIUM DIEM Nigeria Limited a shekarar 2014, darakta Enugu DISCO a shekarar 2015, darakta a Directorate of University Advancement, A.B.U Zariya a shekarar 2016, ciyaman Adbisory Council Sir Ahmadu Bello Mem. Foundation daga shekarar 2018 zuwa yau.

Sabon Madakin Zazzau, Muhammed Munir Ja’afaru, ya karbi lambobin yabo da kuma girmamawa da dama da suka hada da National Distinguish Merit Award in Transport (NDMT), Fellow of the Centre for Transport Studies (FCTS) Ogun State University a shekarar 1996, Maritime Chief Executive of the Year a shekarar 1994, Fellow of the Institute of Industrial & Corporation Administration a shekarar 1998, Honourary Life Member-Law Society University of Ibadan a shekarar 1997, Chattered Institute of Transport in Nigeria (Transport Admin. Of the Year) a shekarar 1996.

Ya kuma samu Fellow Nigerian Institute of Purchasing & Supply Management 2002, National Honourary Award ‘Oficer of the Federal Republic’ (OFR) a shekarar 2003.

A yanzu haka Alhaji Muhammad Munir Jafaru (OFR) Majalisar Masarautar Zazzau karkashin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ambasada Ahamed Huhu Bamalli, ta nada shi a matsayin Madakin Zazzau ranar 1 ga Janairu, 2021.

Exit mobile version