Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RA'AYI

Wane Tallafi Matasa Ke Bukata A Siyasance ?

by Tayo Adelaja
September 14, 2017
in RA'AYI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Kwamared Sunusi Mailafiya

Siyasar Nijeriya na daya daga cikin siyasun duniya masu zafi da zazzafar akida, wannan ya sanya siyasar take samun tagomashin mabiya, wasu kuma na gefe suna kallon abin da ke faruwa, sannan su tofa albarkacin bakinsu, duk saboda dai siyasar kasar ta mu akwai abin kallo, akwai abin bibiya da kuma sauraro. Ba kamar sauran kasashe ba, da za ka ga al’umma da yawan su ba ruwansu da siyasa sai lokacin zabe ya zo, daga sun kada kuri’unsu shike nan, sai kuma wata shekarar zaben ta dawo.

Amma mu kuwa a nan ba haka abin yake ba, musamman saboda wayewarmu, ganin cewa rayuwa gabadaya ta kunshi asalin ‘SIYASA’ Domin kuwa a Addinance, da Kabilance duk akwai Shugabanci. Wannan ya taka rawa matuka wajen wayewa da harkokin siyasar. Sannan matasanmu suna ba da matukar gudummowa wajen kara kaifi da gishirin siyasar, musamman wajen nuna soyayya ko sabanin haka, ‘yansiyasa na kara samun tagomashi saboda yanda matasan ke kafe wa kai da fata sai su, suke kuma makalkale wa tare da kafa wa da tsarewa don kare wadanda suke so ko kuma iyayen gidansu a siyasance.

Shi ya sa tun daga 1999 kawo zaben da ya wuce na 2015, ake kashe rayuka ta hanyar bangar siyasa, wadanda matasan ke kashe kawunansu saboda sabanin jam’iyya ko ra’ayi, su ‘yansiyasa ba su da kamar matasa, yayin da su kuma matasan suka ba da kawunansu a kan ‘yansiyasar. Amma abin tambaya a nan shi ne; shin idan ‘yansiyasar sun cim ma nasara, me matasan ke amfana da su, ko kuma wane alfanu suke yi wa matasan dasuka kare kuri’unsu, cikin ruwa da iska da zafi da sanyi?

Wannan kuwa ba sabon abu ba ne a siyasar kasarmu, wanda hakan ya faru kwanan nan cikin hawan bikin Sallah a garin Kano, inda aka samu sabani tsakanin mabiyan darikar  Kwankwasiyya da kuma Gandujiyya, duk da dai har kawo yanzu ba za mu ce ga mai laifi ba, amma dai abin duba wa a nan shi ne, Bangar siyasa ita ce ta taka mahimmiyar rawa wajen dawo da tashe-tashen hankula musamman a garin Kano.

Hausawa na cewa wai don tuwon gobe ake wanke tukunya, wannan kalami shakka babu haka yake, amma fa bin da a kasarmu Nijeriya. Na kuma kalubalanci ‘yansiyasarmu, da yawansu, musamman daga matakin gwamna zuwa har kan kansila, daga sun samu nasara, shike nan sun yi ban-kwana da yaransu, Domin kuwa sun gama musu aikin dasuke bukata, sun yi tallansu, sako da lungu, birni da kauye. Fakat, iya aikinsu ke nan, amma duk wani romon dimokaradiyya da ake samu a gwamnatance, ba kowane dansiyasa ne yake morarawa ‘yansiyasar sa ba, ko kuma kai tsaye na ce ‘yanbangar siyasa, walau ta fannin kasuwanci ko ilimi, dansiyasa nawa ka sani wanda ya sayi katin jarrabawar shiga jami’a ya raba wa matasan unguwarsu? Mutum nawa ka sani a unguwarku ‘yanbangar siyasa da dansiyasa ya dauki nauyin karatunsu (idan masu son karatun ne)?  Aiki nawa ka ga wani dansiyasa ya ba wa wadanda suka wahalta masa? Ba za ka taba ganin haka ba, sai dai ya ci gaba da siya musu kayan maye da bugarwa. Wannan fa kusan ita ce kalar siyasar da muka tsinci kanmu, musamman a Arewa, mun kuma kasa yi wa kanmu fada ballantana mu gane gaskiya, a kan dansiyasa aboki ya kashe abokinsa, Musulmi ya kashe dan’uwansa Musulmi, haka ma Kirista ya kashe dan’uwansa a addini. Alhalin babu wani addini da yai kira da mutum ya kashe dan’uwansa da gangan.

Wani abin takaici yanda za ka ga wasu ‘yansiyasar da kansu ke saya wa ‘yanbangar siyasar kayan mayen, su kuma ba su makamai, wadanda za a illata abokin adawa. Abin tambaya ya dan’uwana matashi shi ne, a lokacin da ya ba ka wannan makamin da kayan mayen, a motar akwai dansa ko kanensa, na san in za ka waiwaya sau dubu ba za ka ga wani ahalinsa cikin ku ba, idan ma ka gani to lalle yana cikin motarsa me numfashi, yana shan rabar injin sanyaya mota, yana ta latse-latsen wayarsa ba tare da wata damuwa ba, amma kai kuma kana nan kana biye wa aikata mummunan laifi a Addinance da kuma Dokar kasa, idan an ci mulki kuma ganin sa ma ya gagare ka, ba zai kuma memanka ba sai bayan shekaru lokacin da zai kuma neman kuri’un al’umma, zai zo da dadin bakinsa da sulallansa don ya san za su sayi imaninka da kuma lokacinka.

A kasashen da suka san ainihin darajar siyasa, sun dauki rayuwar matasa da mahimmanci, Shiyasa har kawo yau kasashe irinsu Faransa da Jamus da kuma Amurka matasan kasar suka fi kowa mutunta siyasa, saboda yadda Shuwagabannin kasar suke mutunta muradunsu, ta hanyoyin ilimi,

tattalin arzikin kasa da kuma samar da kayan more rayuwa, idan muka kwatanta hakan da irin kasata abin sai ya ba ka takaici, abin tambaya shi ne, shin yaushe ne matasan kasata za mu waye da Bangar Siyasa? Yaushe ne kuma za mu zamo masu mutunta muradun kawunanmu?

Shwarata a gare mu ‘yan’uwana matasa, tun kafin lokaci ya kure mana lalle ne mu canza tunaninmu, mu hakura da bangar siyasa, mu koma makaranta, domin mu wuce wulakancin ‘yan siyasa, mu nemi na kanmu don tada komadar rayuwarmu. Babu abin da ya fi ilimi mahimmanci awannan lokaci, tun dansiyasan da ya kasa tallafa maka a hanyar karatunka, lalle ya kamata ka gane shi ba masoyinka ba ne. Wannan shi ne HANGEN NESA. Idan kunne ya ji, hausawa na cewa jiki ya tsira.

SendShareTweetShare
Previous Post

Dubun Wasu Barayi Ta Cika A Jihar Bauchi

Next Post

Jami’an Tsaro Na Bukatar Hadin Kan Jama’a -Shugaban ‘Yan Sintiri

RelatedPosts

Ayyukan Gwamna Inuwa Sun Burge Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo

Ayyukan Gwamna Inuwa Sun Burge Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Daga Ismaila Uba Misilli daya daga cikin bangarorin kyakkyawan shugabanci...

Jamhuriyya

Lokaci Ya Yi Da Arewa Za Ta Koma Wa Akidun Siyasar Jamhuriya Ta Farko

by Muhammad
3 weeks ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Allah Sarki masu iya magana sun...

Tallafi

Kokarin Jihar Katsina Wajen Raba Tallafin Cutar Korona

by Muhammad
2 months ago
0

Daga Ibrahim Musa Kallah, Jihar Katsina na daya daga cikin...

Next Post

Jami’an Tsaro Na Bukatar Hadin Kan Jama’a -Shugaban ‘Yan Sintiri

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version