Wannan tambaya ce mai matukar sarkakiya, saboda tarihin motar hawa ba abu bane na nan kusa, an yi wasu Kekuna na hawa wadanda suke da fasaha irin ta motar hawa, duk da ba z aka ce musu motar ba, amma tuka su ake yadda ake tuka mota.
“Motowagen” mota mai kafafu uku kirar kamfanin ‘Benz’ ana ganin itace mota ta farko wacce duk fasahar tuka ta ya dace da yadda ake tuka motar ta wannan zamanin, tana da wasu abubuwa da kowacce mota take da misali, giya, kaburetor, da birki.
Amma kafin “Motogen” akwai wasu abubuwan hawa da za a iya kiransu motar hawa, misali Leonardo Da Binci ya tuka wani Keke mai siffar mota, ba tare da taimakon doki ba a shekara ta 1500, Simon Steben dan kasar Holand ya kera wata mota mai amfani da karfin iska a shekarar 1600. Ita wannan motar tana daukar mutum har 28, tana kuma tafiyar kilomita 68 a cikin awa biyu.
Nicholas-Joseph Cugnot, dan kasar Faransa ya kera wata mota mai amfani da tiririn ruwan zafi a shekarar 1769, wacce ake amfani da ita wajen safarar kayan yaki na lokacin.