CRI Hausa" />

Wang Webin Ya Gabatar Da Hotunan Wasu Kagawa Kasar Sin Karairayi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce mahukuntan kasar Sin sun jima suna tattaunawa da babbar kwamishinar kare hakkin bil Adama na MDD, bisa gayyatar ta ya ziyarci jihar Xinjiang ta kasar Sin, domin kara fahimtar halin da yankin yake ciki.

Wang wanda ya bayyana hakan a yau Alhamis, yayin taron manema labarai da ya gudana, ya ce kasar Sin na maraba da zuwan al’ummun kasashen waje, wadanda suka amince da yin komai bisa tsari da adalci wannan yanki na Xinjiang, don kara fahimtar yanayin da yake ciki.
A lokaci guda kuma, Sin na matukar adawa da duk wani mataki na tsoma baki cikin harkokin gidan ta, daga wasu kasashe ko mutane, dake fakewa da kare hakkin bil Adama, ko ma masu bincike dake yayata manufar nunawa duniya cewa ana aikata wasu laifufuka a Xinjiang.
Bugu da kari, Wang Wenbin ya ce a baya bayan nan, wasu na ta yada jita jita, da shafa kashin kaji ga jihar Xinjiang da Sin, game da batutuwa masu nasaba da jihar.
Ya ce cikin irin wadannan mutane, akwai wata mace mai suna Zumrat Dawut, ’yar asalin kabilar Uighur da ta zanta da kafar watsa labarai ta BBC, a shirin News Night na ranar 17 ga watan Yulin 2020. Wang ya ce wannan mace ta sha bayyana wasu kalamai, wadanda Sin ke da tabbacin kagarsu ta yi bisa radin kanta, ta zama tamkar wata ’yar wasan kwaikwayo da masu son bata sunan kasar Sin ke amfani da ita, wajen kushe ayyukan mahukuntan jihar Xinjiang. (Saminu)

Exit mobile version