Wang Yi: Ba Zai Yiwu Sin Ta Amince Da Matakin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Ba

Daga CRI Hausa,

Yau Asabar 20 ga wata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da wani jawabi yayin babban taron masanan kasa da kasa ta kafar bidiyo, inda ya jaddada matsayin kasar Sin kan batun Taiwan.

Wang Yi ya bayyana cewa, game da yunkurin neman ‘yancin kan Taiwan bisa dogara da kasar Amurka da hukumar yankin Taiwan ta yi, da makarkashiyar wasu ‘yan siyasar Amurka ta kakkabawa kasar Sin takunkumi bisa fakewa da batun Taiwan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kashedi da kakkausar murya yayin da yake ganawa ta kafar bidiyo da takwaransa na Amurka, kuma ya sake nuna matsayin kasarsa, wato kasar Sin daya tak a duniya, kana Taiwan wani yanki ne nata.

A don haka, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarin cimma burin dunkulewar kasar cikin lumana. Haka kuma, ba zai yiwu ta amince da matakin neman ‘yancin kan Taiwan ba, kuma ba za ta yarda a yada manufar “kasashen Sin biyu” ko “kasar Sin da kasar Taiwan” ba.
Wang Yi ya kara da cewa, bisa matsayinsu na kasa mai tasowa mafi girma, da kasar da ta samu ci gaba mafi girma a duniya, huldar dake kasashen Sin da Amurka tana shafar makomar duk duniya, don haka, dole ne su daidaita huldar dake tsakaninsu yadda ya kamata.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version