Daga CRI Hausa
Memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya bayyana cewa, a halin yanzu, taimakawa kasashen Afirka daban-daban wajen yaki da cutar COVID-19, gami da farfado da tattalin arzikinsu, abu ne mafi muhimmanci ga hadin-gwiwar Sin da Afirka.
A wajen taron manema labarai na zama na hudu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13, Wang Yi ya nuna cewa, a bara, shugaba Xi Jinping ya jagoranci taron koli na musamman na hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen dakile cutar COVID-19, inda ya sanar da wasu sabbin matakai na tallafawa Afirka. Kawo yanzu, kasar Sin ta turawa kasashen Afirka kayayyakin yaki da cutar cikin gaggawa har sau 120, gami da rukunonin kwararrun likitoci zuwa kasashe 15, tare kuma da samar da alluran riga-kafin cutar ga kasashen Afirka 35 da kungiyar tarayyar Afirka wato AU. Har wa yau, yanzu kasar Sin na samar da taimako wajen aikin gina babbar hedkwatar cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka ko kuma Africa CDC a takaice, da gaggauta gudanar da hadin-gwiwa tsakanin wasu asibitocin Sin da Afirka 30.
Minista Wang ya kara da cewa, a bara ne aka cika shekaru 20 da kafuwar dandalin hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC. Hadin-gwiwar Sin da Afirka ta zama abun koyi ga hadin-gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa. Kuma a shekarar da muke ciki, Sin da Afirka za su gudanar da sabon taron dandalin tattauna hadin-gwiwarsu a kasar Senegal, inda kasar Sin take sa ran amfani da wannan dama don marawa Afirka baya wajen ganin bayan cutar COVID-19, da gaggauta raya masana’antu, da kokarin dunkulewar nahiyar baki daya, da kuma taimaka mata wajen warware matsaloli bisa hanyar siyasa. Inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kara raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakaninsu, zai samar da sabon kuzari ga ci gaban nahiyar Afirka mai dorewa. (Mai Fassara: Murtala Zhang)