Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da takwaransa na kasar Morocco Nasser Bourita jiya Juma’a a nan birnin Beijing. Yayin tattaunawar tasu, Wang ya ce a shekara mai zuwa za a yi bikin cika shekaru 10 da kulla huldar diflomasiyya bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Morocco, kuma Sin a shirye take ta yi aiki tare da Morocco, wajen goyon bayan ainihin burin kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin sassan biyu, da wanzar da musaya bisa matsayin koli, da tsara hadin gwiwa a fannoni daban daban, da hada hannu wajen bude sabon babin alakoki tsakanin Sin da Morocco, da Sin da kasashen Larabawa.
Wang ya kara da cewa, Sin a shirye take ta yi aiki da sassan kasa da kasa ciki har da Morocco, wajen ingiza ci gaban odar kasashen duniya, bisa karin adalci kuma kan turba ta gari.
A nasa tsokaci kuwa, mista Bourita ya ce Morocco na nacewa munufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan Sin a fannin kare ikonta na ‘yancin mulkin kai da tsaro.
Ya ce Morocco, ta sha alwashin zurfafa hadin gwiwa tare da Sin, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, da fadada musaya a fannoni irinsu yawon bude ido, da ilimi, da al’adu, da ci gaba da yayata kawance bisa matsayin koli tsakanin kasashen biyu. A daya bangaren kuma, Morocco na maraba, da kuma goyon bayan shawarar inganta tsarin shugabancin duniya da Sin ta gabatar. (Saminu Alhassan)