CRI Hausa" />

Wang Yi, Ya Yi Jawabi Ta Bidiyo A taron Shawarwari Kan Kwance Damara Na Geneva

A yau ne, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, a taron shawarwari kan kwance damara na Geneva. Cikin jawabin na sa ya ce, ra’ayin bangarori daban daban ra’ayi ne da ya dace, kuma ya kamata kasa da kasa su bi wannan ra’ayi, tare da bin sabon ra’ayin kiyaye tsaro na bai daya, da yin hadin gwiwa da kuma wanzar da hakan, da yin kokarin sa kaimi ga aiwatar da aikin kwance damara, da hana yaduwar makamai a duniya.

A cikin jawabinsa, a madadin kasar Sin, Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda hudu, game da yadda za a sa kaimi ga aiwatar da aikin kwance damara da hana yaduwar makamai a duniya, inda ya jaddada cewa, ya kamata a nemi zaman lafiya da tsaro, ta yin hadin gwiwa, da tabbatar da an aiwatar da manyan tsare-tsare a duniya, da bin yarjejeniyar sa ido kan yawan sojoji da makamai ta kasa da kasa, da warware batun hana yaduwar makamai ta hanyar yin shawarwari, da kuma kyautata tsarin kiyaye tsaro na sabbin fannoni a duniya. (Zainab)

Exit mobile version