Wang Yi Ya Yi Tir Da Matakin Nancy Pelosi Na Ziyartar Yankin Taiwan
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Yi Tir Da Matakin Nancy Pelosi Na Ziyartar Yankin Taiwan

byCMG Hausa
3 years ago
Wang Yi

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi Allah wadai da ziyarar da kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan. Yana mai cewa, hakan keta manufar “kasar Sin daya tak a duniya” ne, kuma mataki ne da ya keta alfarmar ’yancin cin gashin kai na Sin, ya kuma haifar da rashin jituwa a siyasance, tare da fusata al’ummar kasar Sin, da Allah wadai daga sassan kasa da kasa.
Wang ya kara da cewa, abun da Pelosi ta yi ya nuna yadda wasu ’yan siyasar Amurka suka rungumi akidar gurgunta alakar Sin da Amurka, yayin da Amurkar ke kara zama babbar mai lahanta zaman lafiya a zirin Taiwan, tare da gurgunta yanayi na daidaito a shiyyar.

A daya hannun kuma, Wang ya gargadi Amurka, da ta kawar da mafarkin ta na dakile dunkulewar yankunan kasar Sin, kasancewar Taiwan bangare na kasar, kuma yanzu lokaci ne na dunkulewar Sin da ba wanda zai iya dakatarwa.

Ministan wajen na Sin ya ce, za a tabbatar da toshe duk wata kafa ta yunkurin samun ’yancin yankin Taiwan, da yunkurin duk wasu sassa na waje dake taimakawa hakan.

Ya ce duk irin yadda Amurka ta taimaka, ko ta yi hadin kai da masu burin ganin ’yancin kan Taiwan, ba za su yi nasara ba. Maimakon hakan, Amurka za ta bar tarihi ne na mummunan aikin tsoma hannu cikin harkokin gidan sauran kasashe.

Batun Taiwan ya bijiro ne yayin da kasar ke da rauni, take kuma fama da tashe-tashen hankula, amma a yanzu farfadowar kasar Sin zai kawar da dukkanin wadannan kalubale.

A nasa bangare, mataimakin ministan harkokin wajen Sin Xie Feng ya kira jakadan Amurka a Sin Nicholas Burns a daren jiya Talata, inda ya gabatar da korafi mai karfi, da rashin amincewar Sin da ziyarar Nancy Pelosi a yankin Taiwan na kasar Sin. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 2.6 Domin Tsaron Abuja

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 2.6 Domin Tsaron Abuja

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version