Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da fashewar wani abu da ba a kai ga gane menene ba, a Unguwan Mongoro dake karamar hukumar Igabi dake jihar. A rahoton na gwamnatin jihar, wasu yara ne suka dauko wani abu da basu san mene bane don yin wasa da shi; amma sai abun ya fashe inda ya raunata mutane da dama.
A sanarwar, mutanen da abun ya raunata suna asibitin Shika suna samun kulawa daga likitoci, kuma kawo babu rahoton rasa rai daga gwamnatin.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-rufai ya bukaci al’umma dasu kwantar da hankalinsu, sannan jami’an tsaro su gaggauta gudanar da bincike don gano musababbin afkuwar wannan fashewar.