Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Rahotannin daga kasa mai tsarki sun bayyana cewa wani Alhaji daga jihar Katsina ya sake rasuwa a can bayan kammala aikin hajjin bana, sakamakon wata gajeruwar rashin lafiya a garin Makka.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Katsina, Malam Badaru Bello Karofi ya tabbatar da wannan labari ga wakilin LEADRESHIP A Yau ta hanyar wayar Salula.
Inda ya bayyana cewa Alhajin da ya rasu sunansa Alhaji Saminu Kofar Bai, sannan dan uwa ne ga matar Gwamna jihar Katsina, Aminu Bello Masari, kuma tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada a can kasar mai tsarki.
Ya bayyana cewa akwai wata Hajiya da ta rasu wanda ‘yar asalin karamar hukumar Bakori ce, sai kuma wani Alhaji da ya rasu shi ma daga karamar hukumar jibiya, duk a jahar ta. Katsina.
Ya ce an gudanar da addu’o’I na musamman ga wadanda suka rasu da kuma daga jihar Katsina da shuwagabannin da kuma kasa baki daya.