Wani Alhajin Jihar Katsina Ya Sake Rasuwa A Kasa Mai Tsarki

Daga El-Zaharadeen Umar,  Katsina

Rahotannin daga kasa mai tsarki sun bayyana cewa wani Alhaji daga jihar Katsina ya sake rasuwa a can bayan kammala aikin hajjin bana, sakamakon wata gajeruwar rashin lafiya a garin Makka.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Katsina, Malam Badaru Bello Karofi ya tabbatar da wannan labari ga wakilin LEADRESHIP A Yau ta hanyar wayar Salula.

Inda ya bayyana cewa Alhajin da ya rasu sunansa Alhaji Saminu Kofar Bai, sannan dan uwa ne ga matar Gwamna jihar Katsina, Aminu Bello Masari,  kuma tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada a can kasar mai tsarki.

Malam Badaru Bello ya kara da cewa yanzu jimlar Alhazai uku ke nan jihar Katsina ta rasa, inda ko kwanakin baya wasu biyu sun rasu a can kasa mai tsarki kuma acan din aka yi masu sutura kamar yadda shar’a ta tanada.

Ya bayyana cewa akwai wata Hajiya da ta rasu wanda ‘yar asalin karamar hukumar Bakori ce, sai kuma wani Alhaji da ya rasu shi ma daga karamar hukumar jibiya, duk a jahar ta. Katsina.

Ya ce an gudanar da addu’o’I na musamman ga wadanda suka rasu da kuma daga jihar Katsina da  shuwagabannin da kuma kasa baki daya.

Exit mobile version