Rabiu Ali Indabawa" />

Wani Hari A Mogadishu Ya Hallaka Mutane Sama Da Goma

An kai hari a Mogadishu babban birnin Saomaliya cikin wata mota da ya yi sanadiyyar halaka sama da mutum bakwai. Motar dake dankare da bama-baman ta tarwatsa kanta ne a kan hanyar Maka al-Mukarrama dake kusa da Majalisar Dokoki yayin da jami’an tsaro ke kokarin tare motar domin a bincike ta.

Nan da nan kungiyar ‘yan bindigar al-Shabab ta dauki alhakin kai harin. “Motar taki saurarawa harbin gargadi ta kuma kutsa a guje a cikin tarin jami’an tsaro da suke kula da shingen da dakarun fadar gwamnatin Kasar suka kafa, inda bam din ya tashi mu kuma muka ci gaba da zubawa mator harshashai”, inji wani jami’in tsaro Aden Mohammed yana fadi bayan harin.

Rahotanni sun bayyana cewa, an ga gawarwaki akalla bakwai, kuma ya ga mutane da dama sun jikkata a lokacin da motocin daukar marasa lafiya ke kwasar su. Asibitoci sun tabbatar da mutuwar mutane uku da suka ji munanar raunuku.

Wakilin Muryar Amurka ya ce ginegine da dama dake wurin sun lalace wasu ma sun rushe, lamarin da ya ta da kura da hayaki da suka turnuke sama.

Exit mobile version