Rabiu Ali Indabawa" />

Wani Harin Jiragen Saman Sojan Afghanistan Ya Hallaka DalibaI Masu Saukar Kur’ani

Mutane da dama ne ke cike da fargaba sakamakon wani harin jiragen sama da jiragen saman sojojin Afghanistan suka kai kan wata makarantar karatun al Kur’ani dake Kunduz, Arewa maso Gabashin kasar, inda aka bai wa daliban takardar shaidar kammala karatu a gaban wasu shuwagabanin Taliban da dalibai da dama.

A cewar shugaban asibitin yankin Dr. Na’im Mangal, mutane da dama sun rasa rayukansu a yayin da wasu sama da 15 suka jikkata, wadanda kuma suka hada da kananan yaran da aka kwantar a asibitinsa mai tarazar kilo mita 50 daga lardin Dashte Archi inda harin ya wakana.

Majiyoyin tsaro da na shaidun gani da ido sun ce, fararen hula da dama ne dai suka halarci shagululanan saukar karatun kur’anin mai tsarki a lokacin da abin ya faru.

Muhammad Is’hak wani ganau ne, ya sanar a tashar TB Tolo News ta kasar Afghanistan cewa, suna cikin masallacin Akundzada inda saukar karatun ta gudana ne, wanda kuma ya samu halartar dalibai da fararen hula da yawa, da kuma wasu mambobin kungiyar ‘yan tawayen Taliban da aka gayyata ne, suka ji karar jiragen sama nan take kuma ‘yan Taliban suka tsure, hankalinsu ya tashi kafin ka ce me tuni bamabamai sun fara sauka a ginin wannan masallaci, nan take kuma mutane da dama suka rasa rayukansu da kuma jikkata.

Wani mai daukar Hoton AFP ya ce, ya ganewa idonsa kankanan yara da matasa da dama daga cikin wadanda suka jikkata kwance a kasa da kuma cikin lungunan da kwanonin asibitin.

Sai dai a ta bakin kakakin ma’aikatar tsaron kasar ta Afghanistan, Muhammad Radmanish, ya musanta cewa harin ya rutsa da yara da fararen hula a masalacin, illa shugabanin Taliban a kalla su 20 da suka hada da kwamandansu, da aka kashe tare da jikkata wasu da dama.

Exit mobile version