Wani Kamfanin Chana Zai Gina Masakar Da Ba Irinta A Nijeriya

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

A ci gaba da ziyarar da gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar ke yi a halin yanzu a kasar China, tawagar gwamnan ta ziyaraci wani katafaren kamfani da ya kware wajen gina manyan Hanyoyi, Gadoji, titin jirgin kasa masu saurin gaske, da ma sauran abubuwan da kamfanin ke aiwatarwa a China da kuma sauran kasashen duniya.

Wannan kamafani ne kuma ya gina gadar ta fi kowacce gada tsawo a China, yanzu haka kuma kamfanin na aikin gina wacce za ta shafe ta farko.

Kamfanin Shandong na tattaunawa da gwamnatin Kano domin samar da tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai karfin 100 GWT, za a hada hannu wajen samar da kashi 60% na kudadedan aiwatar da wannan aiki a Kano a cikin shirin Kamfanin na fadada hannun jarinsa a kasashen afrika.

Haka kuma an zaga da tawagar gwamnan na Kano domin ganewa idonsu ire-iren ayyukan da wannan kamfani ke aiwatarwa a China da sauran kasashen duniya.

A dai wannan ziyarar tawagar gwamna Ganduje sun ziyarci kamfanin ‘Ruyin Group’ wadanda suka shahara ta fuskar samar da kayan tufafi, kamfanin na cikin kamfanonin da suka fi girma a China wadanda ke samar da kalolin tufai sama 30 a duniya, kamfanin na samar da murabba’in mita miliyan 1.2 na kayan tufafi a duk shekara, Haka kuma kamfanin na da rassa a China da sauran kasashen duniya.

Yanzu haka tattaunawa ta yi nisa na samar da wani kamfanin masaka wanda zai zama mafi girma a Nijeriya, Masakar da ake sa ran lakume Dala Miliyan 600.

Kamfanin ya yi alkawarin fara aikin cikin wannan shekarar, ya  kuma yi alkawarin samar da wuta mai amfani da hasken rana domin aiki a kamfanin.

A lokacin ziyarar Gwamna Ganduje ya ziyarci mataimakin Gwamnan Shandong, Madame Wang Suilian, inda ya bayyana masa dalilin ziyarar tasa zuwa kasar China. Ya ce, mun ziyarci Kamfanin ‘Ruyin Group’ wanda muka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimta ta samar da Masaka wadda aka tsara za ta lakume Dala Miliyan 600.

Gwamna Ganduje ya ce bayan wadannan kamfanoni ma mun ziyarci wurare daban-daban wadanda ke kwadayin zuba Jari a Jihar Kano.  Ya ci gaba da cewa Kamfanonin da Jihar Kano duk za su amfana da wannan ziyara.

 

 

Exit mobile version