Akwai dai zarge-zarge da ke ganin da hannun Yarima mai jiran gado na Saudiyya a kisan na Khashoggi wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar gidan sarautar.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce yana da yakinin cewa an bayar da umarnin kisan Fitaccen dan jaridar Saudiyya Jamal Khasgohhi ne daga babban Ofishin gwamnatin Saudin a Riyadh ba wai kai tsaye mutanen da ake zargin suka aikata kisan ba.
Cikin kalaman shugaban Turkiyyan na baya-bayan nan game da kisan Khashoggi ya ce dole ne wani babban kusa a gwamnatin Saudin ne ya yi umarnin kisan amma ba zai taba zama Sarki Salman ba.
A cewar Erdogan ko kadan dai dai da dakika daya ba zai taba amincewa Sarki Salman ne ya yi umarnin kisan ba, haka zalika bashi da masaniya a batun, amma dai tabbas wani na jikinsa ne da ke da ikon fada aji a mulkin kasar.
Akwai dai zarge-zarge da ke ganin da hannun Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman a kisan na Khashoggi wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar gidan sarautar, ko da dai manyan jami’an gwamnatin kasar na ci gaba da nanata cewa babu hannun yariman na su a ciki.