Yarinya ‘yar shekara bakwai ta shaida wa jami’an ‘yan sandan jihar Ogun yadda mahaifinta Nasiru Adeyemo, da kishiyar mahaifiyarta, Idayat, suka datse mata yatsa, suka kuma daure ta a cikin buhu suka yasar da ita a gefen hanya da nufin kasheta.
Rahotanni sun bayyana yadda aka yasar da yarinyar a wani jeji dake gefen hanya bayan sun datse mata karamin dan yatsa. Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana yadda suka kama mahaifin da matar sakamakon sanarwar mazauna yankin.
Oyeyemi, yace, a binciken hukumar ‘yan sanda sun gano wani buhu da ba su gane menene a cikinsa ba a gefen titin hanyar Asabala dake Papalanto zuwa Sagamu duk a jihar Ogun.
Oyeyemi , ya kara cewa, sanarwar mazauna yankin ta sa suka yi gaggawar zuwa wajen, jami’in ‘yan sanda na Owode Egba CSP Shehu Alao ya jagoranci jama’arsa zuwa wajen, lokacin da aka kwance buhun abin al’ajabi sai ga yarinya mai shekara bakwai da yatsan ta a datse, tun ranar Juma’a aka yasar da ita a wajen. Da aka fahimci yarinya da ranta sai aka yi sauri aka garzaya da ita asibiti.
A yanzu haka hukumar tsaro na tsare da wadanda ake zargin aikata laifin da ake zarginsu da aikatawa.