Mista Emmanuel Matambo, masanin dangantakar Sin da Afirka, na jamiar KwaZulu-Natal ta Afirka ta Kudu, ya jinjinawa kasar Sin bisa dimbin nasarorin da ta samu a fannin kandagarkin annobar COVID-19 a shekara ta 2020, tare kuma da gode mata saboda cikakken goyon-bayan da take ba kasashen Afirka wajen inganta kwarewarsu a fannin yaki da annobar.
Emmanuel Matambo, ya bayyana haka ne yayin zantawarsa da babban rukunin gidan talabijin da rediyo na kasar Sin CMG.
Bazuwar annobar COVID-19 na babbar illa ga tattalin arzikin duniya, amma alkaluman kididdiga sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba a cikin wasu manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.
Dangane da haka, masanin ya yabawa kasar Sin saboda kirkire-kirkiren da take yi da kuma kuzarinta na raya tattalin arziki, inda ya bayyana Sin a matsayin abar koyi ga kasashen Afirka.
Ya kara da cewa, idan aka waiwayi abubuwan da suka wakana a shekara ta 2020, ana iya ganin cewa, kasar Sin da kasashen Afirka sun fadada hadin-gwiwa ta fuskar tattalin arziki, inda har suka rika goyon bayan juna da himmatuwa tare domin yaki da annobar COVID-19.
Ya ce, kasashen yammacin duniya sun saka siyasa a cikin batun annobar, da rura wutar rikicin kabilanci a cikin hadin-gwiwar Afirka da Sin. Amma kasar Sin tana marawa Afirka baya wajen ganin bayan annobar, da taimaka mata gina cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa wato Africa CDC, alamarin da ya shaida irin zumunci mai karfi dake tsakaninsu. Mista Matambo ya kuma ce, akwai dadaddiyar alakar abota tsakanin Sin da Afirka, abun dake da muhimmancin gaske ga nahiyar Afirka. (Mai Fassara: Murtala Zhang)