Rabiu Ali Indabawa" />

Wani Mutum Ya Daba Wa Dan Sanda Wuka

He was found at the crime scene

a Faransa mai tsatsauran ra’ayin addini ne

Wani mai gabatar da kara kan a bin da ya shafi ayyukan ta’addanci a Faransa ya ce mutumin nan da ya farmaki abopkan aikinsa da wuka a shelkwatar ‘yan sanda har ya yi sanadin mutuwar mutum 4 a cikinsu yana riko ne da akida irinta masu ‘tsatsauran ra’ayin addinin Islama’.

Dan shekara 45 din wanda kwararre ne a sha’anin komfuta yana dasawa da ‘yan Salfiya, wadanda ake wa kallon masu tsatsauran ra’ayi daga cikin ‘yan Sunni, kuma ya sha kare ta’asa da ake aikatawa da sunan addinin Musulunci.

Jami’en ‘yan sanda 4 ne ciki har da mace guda suka mutu a harin na ranar Alhamisa shelkwatar ‘yan sanda kusa da majami’ar Notre Dame a tsakiyar birnin Paris. ‘Yan sanda sun harbe maharin, mai suna Mickael Harpon har lahira.

Wanna lamari dai ya razana illahjirin rundunar ‘yan sandan Faransa wanda tun dafarko suke korafi kan rashin ba su kwarin gwiwa.

Exit mobile version