Wani Soja Ya Hallaka Kwamandansa Ya Kuma Bindige Kansa Da Wasu Sojoji 2 A Sokoto
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wani Soja Ya Hallaka Kwamandansa Ya Kuma Bindige Kansa Da Wasu Sojoji 2 A Sokoto

byKhalid Idris Doya
3 years ago
Soja

Wani sojan Nijeriya ya dauki bindiga ya kashe Kwamandansa, wasu sojoji biyu daga baya ya kashe kansa da kansa a sansanin ‘Forward Operating Base’, Rabah da ke jihar Sokoto.

Sojan da aka gano shi da Lance Corporal Nwobobo Chinoso yana aiki a karkashin bataliya ta 223 da ke Zuru ta jihar Kebbi, an kuma tura shi aiki sansanin Forward Operating Base Rabah, kana lamarin ya faru ne a gidan Kwamandan sansanin a ranar Lahadi.

  • Sojan Fadar Shugaban Kasa Ya Bude Wa ‘Yan Acaba Wuta, Ya Kashe Fasinja
  • ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Tsohon Kanal Din Soja Da ‘Ya’yansa 2 A Zamfara

Ya bude wuta inda ya kashe Kwamandan FOB, Lt. T.I. Sam-Oladapo, da wasu sojoji biyu ciki har da Sajen Manjo (CSM), Iliyasu Inusa da Private Attahiru Mohammed, daga bisani ya juya bindigar zuwa kansa kuma shi ma haka ya mutu.

A wani bayanin faruwar lamarin da LEADERSHIP ta ci karo da shi, ya yi nuna da cewa hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi 5 ga watan Maris na 2023 wajajen karfe 5 na yamma, sannan har zuwa yanzu ba a iya gano musabbabin bude wutar ba, amma an kaddamar da bincike kan lamarin.

An ce Kwamandan runduna ta 8 Garrison da Kwamandan bataliya 26 sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, ana kan kokarin kwasan gawarwakin zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin koyarwa ta jami’ar Usman Danfodio (UDUTH) da ke Sokoto.

An yi kokarin jin ta bakin daraktan sashin yada labarai na rundunar sojin Nijeriya, Birgediya Janar, Onyema Nwachukwu, amma haka ba ta cimma ruwa ba, sai sai wasu majiyoyin soja sun tabbatar wa LEADERSHIP da faruwar lamarin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya
Labarai

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba
Labarai

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci
Labarai

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Next Post
Sin Na Ci Gaba Da Dukufa Kan Bude Kofa Ga Ketare

Sin Na Ci Gaba Da Dukufa Kan Bude Kofa Ga Ketare

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version