Abubakar Abba" />

Wanne Abinci Ne Ya Dace Da Tsofaffi?

Sakon a kullum da ya zamo jiki shine, cin abinci mai lafiya yana kara doguwar rayuwa, amma wanne irin ingantaccen abinci ne dake taimawa wajen cimma wannan burin?

A wannan sharhin, zamu yi bayani dalla-dalla akan irin abincin da sukafi dacewa kuma masu dauke da ababen gina jiki.

Wanne abinci ne yafi dacewa  wajen kara lafiya ga dan Adam? Zamu yi bincuke akan hakan.

A bisa kididdigar da Jamiai suka yi a yanzu haka,kasa uku dake akan gaba a duniya wadanda kuma dije akan babban buri na rayuwa sube,Monaco, Japan, da kuma  Singapore.

A kafar yada labarai muna jin yadda ake yin magana akan abinci na kwarai wanda kuma yake dauke da sanadarai masu gina jiki.

Amma masana a fannin abinci basu yi ammana da wannan kalmar ta abinci na kwarai ba akan cewar hakan ba zai sanya mutane su mayar da babban mahimmanci akan cin abinci mai gina jiki ba shine mafita kawai ba.

Duk  da hakan, akwai wasu nauuka na abinci dake dauke da sanadarai masu gina jiki fiye da sauran nauuka na abinci wadanda kuma bincike ya tabbatar cewar suna taimakawa wajen yakar wasu cututtuka.

Anan, ga wasu mahimman abinci da muka yi nazari akan su harda wadanda kake bukata zasu saka farin ciki da kuma kara maka kiwon lafiya.

Waken Soya:

Baya ga sunan sa na Waken Soya ana kuma kiransa da Edamame, har ila yau alumar nahiyar Asiya suna yin amfani dashi ana kuma sanya shi a cikin abinci da sauran nau’I na abinci yana  kuma dauke da sanadarin dake yakar kansa.

Har ila yau, yin amfani dashi yana taimakwa wajen yin maganin kansa ta Nono haka yana taimakwa wajen samar da sanadarin (protein) yana kuma dauke da sanadaranminerals, calcium, iron, manganese, selenium, phosphorous, magnesium, zinc, da kuma na  copper.

Karas yana taimakwa wajen kaucewa damejin idanu:

Acewar cibiyar kiwon lafiya (NIH) karas yana taimakawa jind an adam samun sanadarin Bitamin A da taimakawa garkuwar jiki da karfin ganin ido kuma jikin ba zai iya samar da sanadarin Bitamin A ba dole sai ta hanyar abinci mai gina jiki.

Bugu da kari, baincike ya kuma nuna cewar, abincin dake dauke karas mai yawa yana taimakwa karfin ganin ido musamman idan mutum ya tsufa.

Wasu ire-iren na karas basu dauke da sanadarin lemo amma sunadauke da sanadarin falcarinol, wanda kuma bincike ya nuna cewar, yana taimakwa wajen yakar kansa.

Yin amfani da zanllan karas yafi sanya lafiya kuma akwai hanyar da za’ a iya yin girki dashi, ba tare da an rasa sanadaran dake a cikn sa ba.

Kayan lambu:

Wannan suma suna cikin ire-ire na abinci da suke cikin wannan sahun kuma yana taimakwa lafiyar dan adam.

Yana kuma dauke da sanadarai musamman na Bitamin C, E, K, folate, potassium, calcium,  selenium,  carotenoids  da kuma  zeadanthin da kuma na glucosinolates har ila yau, sunataimakwa lafiyar jiki.

A wani bincike da aka gudanar a kwanan baya da MNTfound ta yi ta gano cewar, koren ganye da kuma wasu kayan lambu irin na kale da collard, suna taimakawa wajen cushewar ciki, har ilka yau, masu bincike sun bayar da shawawar da a dinga cin koren ganye a kullum don karawa kwakwalwa lafiya.

Har ila yau, sanadarin Kale, broccoli, da cabbage suna karawa zuciya lafiya kuma muna godiya ga Bitamin K.

A karashe, kayan lambu hanya ce ta samun sanadarin soluble fiber,wanda yake taimakawa wajen daidaita Siga da kuma rage kiba.

Kifin Salmon:

Binciken da aka gudanar a baya ya nuna cewar, cin Nama musamman jan Nama da wasu nau’oin na Nama suna shafar lafiyar mutum a nan gaba.

Amma yin amfani da kifi da salmon, suna dauke da sanadarin dake kara lafiya.

Salmon yana dauke da sanadaran protein,omega-3 fatty acids, wadanda kuma suna taimakwa karfin ido har ila yau, sanadarin omega-3 yana bayar da kariya daga kafewar ruwan ido haka sanadarin yana da alaka da lafiyar kwakwalwa

Bugu da kari, Salmon yana dauke da sanadaran potassium, autumn, potassium wadanda suke bayar da kariya daga kamuwa da cututtukan zuciya.

Har ila yau, irin wannan Kifi, yana dauke da sanadaran selenium, wanda yake taimakwa lafiya musamman wajen gudanar da ayyuka.

Kayan Marmari:

Kayan marmari suna taimakwa lafiyar jikin dan adam musaman a cikin abinci kuma ana samun su a ko ina a fadin duniya kamar su Lemon zaki da sauran su

Sanadarin he flabonoids dake a cikin kayan marmari, sauna sanya doguwar rayuwa kuma da jimawa masana a fannin abinci sun shawarci tsofaffi dasu dinga yin amfani dashi dominsuna dauke da sanadarin Bitamin C har ila yau, masana suna ganain amfanain ya wuce na Bita C kawai

Kayan marmari suna kunshe da sanadaran siga, dietary fiber, potassium, folate, calcium, thiamin, niacin, bitamin B-6, phosphorus, magnesium, copper, riboflabin da kuma na  pantothenic acid.

Bincike ya nuna cewar, sanadarin flabonoids dake a cikin kayan marmari yana taimakwa wajen kare kamuwa da cututtuka har da cutar kansa.

Mazauna kasar Japan suna yin amfani da kayan marmari na shikuwasa akoda yaushe kuma shan sa yana kara lafiya sosai.

 

Exit mobile version