Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RA'AYI

Wanne Sauyi Farfesa Dahuwa Azare Ya Kawo Hukumar NTI?

by Tayo Adelaja
October 4, 2017
in RA'AYI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Babangida Kakaki

Kamar yadda masu iya magana ke cewa, ‘Da tsohuwar zuma a ke magani,’ abin da ya faru a Hukumar Horadda Malamai ta Ƙasa, watau National Teachers’ Institute NTI a Kaduna na nadin Farfesan ilmi, kuma dattijo, Garba Dahuwa Azare a matsayin Babban Darekta mai gudanarwa ba wai dace ba ne, har ma dora Hukumar ne a turbar ci gaba da cimma manufofin kafa ta.

Halin da Hukumar Horadda Malamai ta Ƙasa, watau NTI ta samu kanta a ciki a shekarun baya, abin takaici ne. kamar yadda bincike ya nuna, al’adar rashin bin Ka’idar aiki da halin kashe-mu-raba da rib-da-ciki akan harkokin ma’aikata da shugabancin girman kai da dagawa su ne abin da aka sanya a gaba.

Bincike ya nuna cewa, jagorancin Farfesa Azare ya ƙirƙiro da tsarin manhajar shugabanci watau Organogram wanda ya dace da Hukumar da kuma mayar da kowane abu a muhallin da ya dace, wanda a baya aka harmutsa da yin gamin-gambiza domin cimma wata manufa ta ƙashin kai. Wannan sabuwar tsarin shugabanci Ma’aikatar ilmi ta amince da shi. Kuma har ya fara aiki tuntuni. Daga cikinsa ne aka samar da sashen Tabbatar da Nagartar kwasa-kwasai da ilmi na’urar komfuta, wanda a baya babu shi.

Shugabannin dauri haka suka assasa tsarin na dauki-dorar da ta haifar da gunaguni da kyeshi da raunana guyagun ma’aikata. Zuwan FarfesaAzare, duk wannan ya zama tarihi. “Ci gaba ne babba wanda kowane ma’aikatan ke farin ciki da alfahari da shi,’ in ji wani Ma’aikaci, Salihu Mahmud a tattaunawa da shi.

Batun kuɗ aɗ en hutu da kwanan-daji, wanda shugabannin da suka ki aiwatarwa, Farfesa Azare ya aiwatar da shi, da kuma bayar da umurnin ya rika ba dukkan ma’aikata hakkokinsu a lokaci ɗ aya, wasu tun kafin su bar ma’aikatar su tafi wuraren ayyukan da aka tura su. A da sai ma’aikaci ya tafi aiki, ya dawo ko da kwanaki nawa ya yi, sannan a ba shi kuɗ aɗ ensa su ma ba duka ba, abin da shugabannin suka ga dama, bayan sun zaftare wani kaso daga ciki. Amma a yau, ma’aikatan Hukumar NTI su na cikin farin ciki da gamsuwa da yadda Farfesa ya kawo sauyi a wannan janibin.

Kafin FARFESA ya kama aiki, Hukumar NTI tana da matsala da Hukumar jami’o’i ta Ƙasa, matsalar da ta yi kamari ta yadda Jaridar harshen Turanci ta Daily Trust ta rubuta ra’ayinta a ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2016, inda ta ce Hukumar NTI tana bayar da takardun shaidardigiri da babbar difloma watau post graduate diploma wadda ba a amince da su ba. Amma daga zuwa Farfesa Azare, Hukumar Jami’o’in ta bayar da sanarwar cewa, ta amince da takardun digirin da babbar diflomomin da Hukumar NTI ta bayar a baya da waɗ anda za su bayar a gaba. Wannan gagarumar nazara ce, wadda wajibi ne a dangana ta da salon jagorancin Farfesa a matsayinsa na mai cikakken ilmi da dattaku da sanin-makamar-aiki.

A cikin shekara ɗ aya da ya yi, ofisoshin Hukumar ta NTI sun samu ‘yan gyare-gyare da sabbin tebura da kujeru a shiyya-shiyya na ƙasar nan, da ma inda a da babu su. Sannan da yake cikakken malamin jami’a ne wanda ya san amfani da tasirin ilmi, ya kawo tsarin tura ma’aikata kwasa-kwasai da cibiyoyin ƙaro ilmi, da shan alwashin biyan dukkan kuɗ in kwas din da ma’aikata suka nemo, idan har ya dace da wurin aikinsa. Daga ciki ne, wasu suka tafi Ƙasar Isra’ila.

 

A lokacinsa ne Hukumar ta hada hannu da Cibiyar Ilmin Kare Muhalli wadda ke birnin Ahmadabad a Ƙasar Indiya aka ƙirƙiro ilmin kare muhalli ta hanyar tsarin karatun mai tsawo na manya. Wannan kwas ya karbi bakuncin masana biyu, Dokta Shiɓani da Dokta Pandya Prathesh waɗ anda suka zo ƙasar nan domin taron kara wa sani domin samar da manhajar ilmin kare muhalli abin da ake kira Green Teacher (GT) aturance wanda aka yi daga ranar 11 zuwa 15 ga watan Satumba a Hukumar tare da hadin guiwar Cibiyar Koyarwa ta Ƙasashen Rainon Ingila da Ma’aikatun Ilmi da Kare Muhalli na ƙasa.

 

 

Hukumar NTI ba ta filin da za ta gina ofisoshin shiyya da na yanki da ofisoshin tuntuba, wanda Ministan ya dauki alkawalin bai wa Hukumar wani filin a DutsenAlhaji dake Abuja. Wani abin burgewa shi ne a lokacin ziyarar ne, Farfesa ya shaida wa Ministan Abuja cewa, Hukumarta NTI za ta fara gudanar da karatun difloma a fannin ilmin kare muhalli tare da hadin guiwar Cibiyar Koyarwa ta Ƙasashen rainon Ingila, watau Commonwealth of Learning (COL).

 

Bugu da kari, Faresa Azare ya ƙirƙiro wani tsarin ci gaban ma’aikatan da ba a taba yi ba a Hukumar NTI, shi ne na daukar dawainiyar ƙarin neman ilmin ma’aikata wanda ya fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumbanwannan shekara ta 2017. A takardar sakula da Rajistara kuma sakataren Majalisar gudanarwar Hukumar, Malam Mahmud Muhammed Usman, Shugabancin Hukumar ya sake duba yanayin daukar nauyin ma’aikatan Hukumar domin Karin neman ilmi don haka ya amincewa da biyan kuɗ aɗ en makarantar kowane ma’aikaci.

 

Daga yanzu, ma’aikata masu karatun dokta a fannin fasaha za a basu naira 200,000, su kuma masu karatun kimiyya naira 300,000 domin kammala bincikensu. Masu karatun digiri na biyu watau Master kuwa, za a basu Naira 100,000 a fannin fasaha, a fannin kimiyya kuwa naira 150,000. Sai masu karatun babbar diflomar Ƙasa, watau Higher national diploma a fannin fasaha ko dabarun koyarwa za su samu naira 20,000, su kuma masu karatun a fannnin kimiyya naira 50,000.

 

Hukumar ƙarƙashin Farfesa Azare za ta dauki nauyin ma’aikatan zuwa Manyan tarurruka da kara-wa-juna-ilmi da kwasa-kwasan kwarewa a fannonin da ma’aikata suke. Abin da ba a taba yi ba a tarihin Hukumar. Waɗ annan kadan ke nan daga ciki ayyukan alherin da Farfesa Azare ya shimfiɗ a a cikin shekara ɗ aya rak da kama aikinsa, waɗ anda ma’aikatan hukumar suke cike da farin ciki da Allah-san-barka. Wannan nuni ne cewa, juma’a mai kyau daga laraba ake gane ta.

Kakaki ɗan jarida ne, ya aiko wannan muƙala daga Kaduna.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Batun Tserewar Kanu Landan: Ƙungiyar IPOB Ta Ƙaryata Orji Kalu

Next Post

Muna Kiyaye Wa Wurin Ɗaukar Ma’aikata -Kwamanda Joshua

RelatedPosts

Tallafi

Kokarin Jihar Katsina Wajen Raba Tallafin Cutar Korona

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Ibrahim Musa Kallah, Jihar Katsina na daya daga cikin...

Almajirci: Ya Kare Zai Kashe Ragon Layya?

Almajirci: Ya Kare Zai Kashe Ragon Layya?

by Sulaiman Ibrahim
1 month ago
0

Kalmar 'Almajiri' balarabiyar kalma ce da aka kankareta daga kalmar...

Hon. Bello

Abinda Ya Sa Hon. Bello Kumo Ya Ciri Tuta A Siyasar Gombe

by Sulaiman Ibrahim
2 months ago
0

Irin girman tasirin da Jagorori suke yi a fannonin rayuwa...

Next Post

Muna Kiyaye Wa Wurin Ɗaukar Ma’aikata -Kwamanda Joshua

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version