Wanzanci Da Farauta Abu Guda Ne – Wazirin Kasar Bade

ALHAJI ABDULMUTALLIF, WAZIRIN KASAR BADE, guda ne cikin wanzaman da su ka yi shuhura a Jihar Yobe, sannan a halin yanzu shi ne ke rike da sarautar Wanzaman Sarkin Kasar Bade na Jihar Yobe a garin Jakuskus. A wata tattaunawa da ya yi Wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA, ya bayyana cewa, sanin kowa ne wanzamai na daya daga cikin wadanda ke ba da gudinmawa a wannan nahiyar tamu, tun kafin a waye da samuwar asibiti, domin kuwa sun sha bayar da tasu gudinmawar, musamman wajen haihuwa, kaciya da aski irin na gargajiya, sannan ya na daya  daga cikin wadanda su ka hada taura biyu; ga shi mafarauci kuma wanzami. Ga yadda hirar tasu ta kasance:

 

Ko za ka bayyana wa masu karatu sunanka?
Sunana Dakata Abdulmutallif, Wazirin Sarkin Askar Kasar Bade, kuma Wanzami ne.

 

Ko me ya kawo Wazirin Sarkin Askar Kasar Bade Jihar Kano?
Kafin zuwana nan Kano, Jigawa na fara zuwa wajen Mahaifiyata, sannan akwai wani nadin sarauta da aka yi wa wasu mutanena a nan Kano, wannan ne yasa na zo kuma wadannan mutane da suka rabauta da wannan sarauta, bakidayansu Wanzamai ne kuma Maharba. Haka nan, na zo wurin wannan nadin sarauta ne a matsayin wakilin mai girma Sarkin Askarmu ne, Abubakar Rugum Sarkin Askar Kasar Bade na garin Jakusko.

Mene ne tarihin wannan gari na Bade?
To shi dai Sarkin Askarmu na Bade, na da tarihi sosai kasan Sarkin Macina an haife shi ne tare da maciji, shi kuma Sarkin Bade an haifi kakansa tare da Aska. Don haka, duk fadin Jihar Yobe babu Wanzami kamarsa, sakamakon cewa dan gado ne shi, ba dan na gada ba. Sannan ka san yanzu ilimi ya fadada, da can akan zarki Wanzamai da yin jifa ko asiri, amma yanzu wannan zargi ya kau babu shi bakidaya.

Haka zalika, muna da Shugabanci a wannan sana’a tamu ta wanzanci, domin kuwa mun fi aikin soja biyayya. Shi yasa duk wanda ya yi biyayya a wannan tsari namu za ka ga Allah (SWT) Ya daukaka shi, sai a yi ta mamakin yadda ya samu wannan daukaka, ba kuwa wani abu ba ne illa cewa wani ya fi ka sanin lakani iri daban-daban.

Tun asali da ma Wanzamai ne ke zuwa farauta ba Kauraye ba?
A da can, Maharba da Mafarauta da kuma “Yanbori duk abu daya ne, sannan tafiyarmu daya da wasu daga cikin Malaman azure. Kazalika, da dama daga cikin wasu hatsabibai da akan samu Masarauta wadanda ke kan gaba, mafiya yawansu Wanzamai ne, wadanda suka shahara a sana’ar wanzanci, amma yanzu haka wasu rana tsaka, suka tsinci kansu a wannan harka tamu ta Wanzanci.

 

Yaya ku ke kallon irin wadannan mutane da suka shigo wannan harka taku kai tsaye?
To magana ta gaskiya dai ka ga kamar ni gado na yi gaba da baya, domin sunan garin da aka haife ni Baka, kuma duk harkar wanzanci a bangaran Mahaifiyata da Mahaifina gado na yi. Sannan duk da haka, ina da iyayen gida masu mutunci musamman a nan Jihar Kano, wadanda nake zama tare da su, nake kuma samun karuwa a wajensu.

Ka san bai kamata Wanzami ya yi alfahari da kayan gado ba, duk dai da cewa ana gadonsa, ana kuma yin alfaharin da shi, amma yin biyayya shi ne komai idan ban da ma yanzu da abubuwa ke neman tabarbarewa. Kodayake, yanzu haka ma muna ta faman yin kokari wajen kawo gyara, sakamakon kafa kungiyoyi da ake yi a duk fadin wannan kasa, domin samun masalaha.

A lokutan baya, Wanzami kokari yake yi ya ga sawun kafar dan’uwansa, domin ya yi amfani da shi ya jefe shi, amma yanzu abubuwa sun canza da zarar na tafi Zuru ko Jigawa ko kuma Zamfara, na samo wata karuwa; zuwa zan yi na samu wani daga cikin ‘yan’uwana Wanzami na ce da shi, na samo maganin ciyo kaza na kuma ba shi, shi ma ya je ya gwada don cigaba da yin amfani da shi. Don haka, ka ga daga nan muka samu babbanci da na da kenan, amma kuma mun san babbanci a bangaran biyayya yana da dadi.

Yaya tsakaninku da Ma’aikatan Lafiya, musamman a Jihar Yobe sakamakon sauyin zamani da aka samu?
Gaskiya a halin yanzu, ba mu da wata matsala da Ma’aikatan Lafiya, domin kuwa ko a wannan makon da ya wuce, an zauna a Gashuwa tare da su kuma zaman da aka yi duk abin da ya shafi irin wadannan abubuwa aka tattauna akansu. Da ma kuma, mukan zauna da su domin samun fahimtar juna, ko yanzu haka ma babu wanda yake turawa Likitoci aiki sama da ni.

Haka nan, duk yayin da aka kawo min yaro na duba na ga ba aikina ba ne, nan take nake cewa a yi maza a garzaya da shi Asibiti. Don haka, ko shakka babu muna da alaka mai kyawun gaske da su, su ma kuma idan aka kai musu suka ga cewa ba aikinsu ba ne, sai su ce a kawo gurinmu.

Amma abin haushi da takaici, sai ka samu wasu Likitocin suna yin kishi ko gaba da Wanzamai da sauran masu maganin gargajiya, wanda hakan ko kadan bai dace ba, domin duk Likitan da ya ga wata hanya da zai iya taimakon al’umma, kamata ya yi ya bi ta. Misali, akwai maigidana Dakta musa Abdilkadir Eriya, Sarkin Fada na Nasarawa a nan Kano, idan ka zo gurinsa ka yi masa bayanin matsalarka, nan take zai nemi takarda ya rubuta maka magani ya ce ka je ka nema, saboda mu a namu tsarin, babu mugunta a ciki ko kadan; da ma a nan Kano iyayen gidana su biyu ne, shi da Dankulu Baushe, sannan duk wadanda suka shigo ba tare da sanin komai ba, sai dai kawai mu ce a yi a hankali da su, musamman masu yawo akan tituna.

 

A matsayinka na Mafarauci kuma Wanzami yaya kuke shiga farauta duba da halin da ake ciki yanzu na rashin tsaro?
Ko shakka babu, muna zuwa farauta babu abinda ke samunmu, duk rigimar nan ma da ake yi muna can sai dai ‘yan gudin hijira da suka cika mana guri, kuma mun karbe su. Sannan akwai kwazazzabo sosai adajin ana samun kamar namun daji irin su Barewa, Gada da Maraya Gwanki da kuma Bauna, sai dai da ke ina zuwa Jihar  Taraba, a can ba a rasa duk irin wadannan namun dajin, akwai a Yankari sai dai wajen akwai doka akan taba irin wadannan namun dajin.

A matsayinka na Wanzami, bisa la’akari da aune-aune da Likitoci kan yi kafin su bayar da magani, kuma akwai wani gwaji da kuke yi kafin ku kai ga bayar da naku magungunan?
Babu shakka, muna da mutane wadanda suka yi karatu a bangaran magungunan gargajiya, kamar  Dakta Musa Abdulkadir Eriya, ya yi karatu a wannan bangare, sannan ire-irensu ne Malamanmu. Sannan sun dora mu akan wannan hanya baya ga abubuwan da muka gada daga wajen iyaye da kakanni, muna kuma yi musu bayani, su ce lallai haka abin yake. Kazalika, ni din nan da kake gani na jima ina yin aikin Aljani, shi yasa ko sunana ya ji nan take sai ya arce.

Akwai wasu Malaman lafiya wadanda ba sa son turo marasa lafiyar da suka lura cewa cutar tasu ba ta Asibiti ba ce wurinku, yaya kuke yi da irin wadannan?
Magana ta gaskiya a wannan zance akwai rashin fahimta, kamar mu a wajemu duk Likitan da ya auna ya ga ba aikinsa ba ne, suna turo mana su, domin duk kasashen da suka cigaba na duniya, suna amfani da maganin gargajiya, sannan Likitocinmu idan sun tashi abinda suke kushe wa shi ne, masu maganin gargajiya duk dai da cewa, ba a taru an zama daya ba.

 

Ko kuna da Cibiyar masu magani gargajiya a Jihar Yobe?
Kwarai da gaskiya muna da ita, domin kuwa ni kaina ina da Kamfani wanda muke yin magunguna na zamani, wasu magungunan na shafawa, wasu kuma na sha.

Kai mafarauci ne Wanzamai ko Wanzami Mafarauci?

To ai tafiyar kusan daya ce, misali Maharbi ne ni kuma Wanzami to duk yawanci haka muke yin kama.

Wane kira za ka yi ga Gwamnatin Jihar Yobe?
Kirana a nan shi ne, Gwamnatin Jihar Yobe ta cigaba da tallafawa kungiyoyinmu, domin a kwanakin baya Gwamnan Jihar ya bude wata kasuwa a garin Damaturu, daga ciki har da ofishinmu na masu maganin gargajiya.

Exit mobile version