Wanzar Da Zaman Lafiya: Shugaban Ohaneze Ya Ziyarci Sakkwato

Daga Musa Muhammad, Abuja

Kamar yadda shugabanni a kasar nan suka dukufa wajen ganin sun dawo da zaman lafiya da fahimtar juna a duk sassan kasar nan, musamman a tsakanin Kudancin kasar nan da Arewaci, ranar Alhamis da ta gabata ne shugaban kungiyar ’yan kabilar Igbo ta Ohaneze Ndi’gbo, John Nnia Nwodo ya ziyar jihar Sakkwato don bunkasa wannan aniya ta samar da zaman lafiya a kasar.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan jihar Sakkwato, Imam Imam ya raba wa manema labarai, Shugaban na kabilar Igbo ya jagoranci mutanen kungiyar tasa a wata ziyarar sada zumunci da ya kai wa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a Sakkwato, inda ya yi kiran cewa kada ’yan Nijeriya su sake a sake jefa su cikin wani mummunan yakin.

Mista John ya ci gaba da cewa duk da kasar nan na fuskantar ’yar barazana a ’yan watannin nan, amma dai bai kamata a yi sake da zaman lafiyar da aka jima ana jin dadinsa ba, “bai kamata mu sake son zuciyarmu ya hana mu hada kan kasar mu ba,” in ji shi.

Daga nan sai John Nwodo ya yaba wa Mai alfarma Sarkin Alhaji Sa’ada Abubakar bisa kyakkyawan

jagorancin da yake nuna wa wajen samun zaman lafiya a kasar nan, musamman inda a ’yan kwanakin nan ya bayyana cewa duk wanda ke son auka wa Igbo, to ya fara da shi. “Ni ma haka na zo da irin wannan sako daga Gwamnonin Kudu maso Gabas, cewa duk mai son auka wa al’ummar Arewa da ke yankin, to ya fara da su Gwamnonin,” kamar yadda Nwodo ya bayyana.

Da yake mayar da jawabi, Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana cewa Allah ya albarkaci kasar nan da yaruka da kabilu da dama don su samu hanyar samar da zaman lafiya, amma ba rarraba ba.

Gwamnan ya ce, “yara ne matasa, wadanda ba su san inda ke masu ciwo ba ke haddasa tashin-tashinar da ke faruwa yanzu, musamman a yankin Kudu maso Gabas, maimakon su nemi hanyar da za su samar da zaman lafiya da ci gaba.”

Daga nan Gwamnan ya tabatar wa da shugaban na Ndibo cewa su a Sakkwato suna zaune lafiya da kowa da kowa. Ya ce, “ina tabbatar maka da cewa mu a Sakkwato muna zaune lafiya da kowa da kowa, kuma haka za mu ci gaba.”

Exit mobile version