Wasu masu bincike daga kasar Sweden sun gano cewar daya daga cikin halittun da sauro yake gudunsu shine kaza, abinda ke nuna cewar watakila kwanciya kusa da kaza na iya kare mutum daga cizon sauro.
Ga al’ummar dake zaune a kasashen bakar fata na Afirka, kwanciya ko yin barci a kusa da kaji suke ba wani bakon abu ba ne, musamman a yankunan karkara.
Masana sun gano cewar akwai jinsunan sauro masu yawa wadanda sun tsani warin kaji, abinda ke nufin cewar watakila za a iya samo wata hanya mai sauki da kuma arha ta yin rigakafin cutar maleriya da sauron ke sanadiyar kamuwa da ita.
Mafi yawan sauro, ciki har da wadanda ke dauke da kwayar cutar maleriya, su na cizon mutane, ne su sanya musu cutar ta hanyar zuba musu jinin da suka dauko mai kunshe da kwayar cutar.
Masanan sun kira tarurruka masu yawa domin kama sauro a wasu gidaje guda 11 a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia, domin neman wani jinsin sauro da ya fi yawa a wurin, wato Anopheles arabiensis.
Daga nan sai masanan suka gwada jinin dake jikin wadannan sauro, inda suka gano jinin dabbobi da yawa, amma kusan dabbar da babu jininta a jikin su ita ce kaza, duk da cewar kaji su na da yawa a wurin.
Daga nan sai wani Farfesa mai suna Rickert Ignell na Jami’ar Kimiyyar Aikin Gona ta kasar Sweden ya roki mutane 11 a wadannan gidaje 11 da su rika kwana a cikin gidan sauron da ba a sanya masa wani magani ba, amma kuma a kusa da shi an sanya wani abu mai warin kaza. A wani gwajin kuma, kazar aka sanya kusa da gidan sauron.
Masanan sun yi mamaki da suka ga cewar yawan sauron da suka kama a wannan wurin ya ragu da kashi 95 cikin 100 daga wuraren da babu warin kaza ko kuma kaji a kusa.
Yanzu dai masanan suna son su gwada ko za a iya samar da wani abu mai warin kaza da za a rika kunnawa kamar kyandir domin korar sauro daga gidaje.
An wallafa sakamakon wannan binciken ne a wata mujalla mai suna “Malaria Journal.”