Wariyar Launin Fata: Ya Kamata Mu Manta Da Komai – Lukaku

Dan wasan gaba na Manchester United Romelu Lukaku ya ce yana son magoya bayan kulob din su mayar da hankali kan wani abu daban, su daina yi masa ihu.

Wata kungiyar da ke yaki da nuna wariyar launin fata mai suna (Kick It Out) ta bayyana irin ihun da ake yi wa Lukaku a matsayin abin kyama, kuma nuna wariyar launin fata ne.

Shafin Twiter na United ya ambato Lukaku na cewa wannan ihun da magoya bayan kulob din suke masa shi ne goyon baya mafi girma da ya samu tun da ya koma kungiyar.

Ya kara da cewa wakar da magoya baya ke yi mai dauke da ihu suna yi ne da nufin fatan alheri amma ya kamata su daina. Ya kamata a rika mutunta juna.

Ita kuwa kungiyar ta Kick Out, a wani sako da ta wallafa a farkon makon nan, ta ce ba za a lamunci yin kalaman nuna wariyar launin fata ba ko da kuwa ana yin hakan ne domin nuna goyon baya ga dan wasa.

United ta wallafa sakonta ne gabanin wasan da suka doke Burton Albion a ranar laraba daci 4-1 inda dan wasan kasar Belgium din, wato Lukaku ya zauna a benci, cewa za a dauki mataki kan duk wani mutum da ya yi kalaman nuna kyama, ana tunawa magoya baya cewa kulob din ba zai yarda da nuna wariyar launin fata ba.

An dai ji magoya bayan suna yin ihu irin wanda suke yi wa Lukaku a filin wasa na Old Trafford ko da yake sun dan boye wasu kalamai daga ciki.

Exit mobile version