Wasan Kwallo Da Sana’a: Kamfanin Bizi Da Gwamnatin Kano Za Su Dauki Matasa 2,000 Aiki

An kiyasta cewa kimanin Matasa 2,000 ne za su samu gajiyar aikin Banki da Gwamnatin Jihar Kano, tare da Kamfanin Bizi Mobile, kamfanin da yake da lasisin hada-hadar kudi ta zamani a fadin kasar nan, wanda a turance ake kira da agency banking.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Kamfanin Bizi Mobile da Bizi pay, Alhaji Dakta Aminu Bizi, a yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna.
Dakta Aminu Bizi, ya bayyana cewa, tuni kamfanin Bizi bisa ga hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano, da babban Bankin Najeriya, sun cimma wata matsaya na ganin sun inganta rayuwar matasa da magance matsalar zaman banza, mussaman a Jihar Kano. Sannan kamfanin na Bizi zai fi bayar da fifiko sosai a yankin Arewacin Najeriya, kasancewar yankin na koma baya ta wajen tattalin arzikin kasa.
Hakazalika, Kamfanin na Bizi da Gwamnatin Jihar Kano sun shirya tsaf domin tallafawa akalla matasa 2000 ta bangaren wasan ƙwallon kafa da na kwando, wanda akayi ma lakabi a turance da “work and play”. Ma’ana sana’a da wasa, domin samar masu da sana’ar dogaro da kai, da kara jawon su a jika, sannan Bankuna da Gwamnatin Jihar Kano.
A cewar Shugaban kamfanin na Bizi mobile, su dai wadannan matasa ‘yan wasan kwallon kafa da na kwando kimanin 2000 da za su ci gajiyar wannan shiri, zasu kasance a matsayin wakilan bankuna a unguwaninsu, ma’ana shi ne, a duk lokacin da suka dawo gida daga filin wasa, za su kasance suna zuwa suna bude ma masu kanana da manyan sana’oi asusun ajiya na banki, wato adashen gata, musamman ga masu sana’ar tuyar kosai, waina, mai rake, mai shago, dan a caba(Mai adaidaita) da dai sauransu.
Sannan kuma, wadannan matasa da kamfanin bizi mobile zai dauka aiki, daga cikin su akwai wadanda suka kammala karatun jami’a babu aikin yi, sannan akwai masu shaidar karatun NCE, da masu sakandari, da dai sauransu.
Sannan za su sami horo na musamman, da kuma ba su kayan aiki domin bude ma Al’umma lambar ajiyan banki na BbN nan take, da yi masu katin banki na ATM da dai sauransu.
A bisa wannan yunkuri na kamfanin Bizi mobile, akalla kowane matashi Mai kwazo zai iya samun ladan kwamishon aikinsa akalla zai iya kamawa daga naira dubu 80 zuwa dubu 100 a duk wata, wanda yin hakan zai yi matukar rage ma matasan Jihar Kano, zaman kashe wando, da kuma jiran aikin yi daga bangaren Gwamnati, sannan zai rage ma dubban matasan Jihar Kano radadin talauci da suke fama da shi. A cewarsa.

Exit mobile version