Daga Taofeek Lawal, Abuja
Mutanen kasar Saudiyya mutanene masu son wasanni musamman wasan linkaya da wasan takwando, sannan suna yin wasu wasannin wadanda suke taimakawa wajen motsa jiki da wasan da yake taimakawa wajen kariya.
Har ila yau wasan kwallon kafa yanada tasiri sosai a kasar ta Saudiyya domin lokuta da dama zaka dinga ganin yara kanana a filayen wasanni suna wasa kuma tare da iyayensu, sai dai wasan kwallon kafa baya hanasu zuwa domin gudanar da sallolinsu idan har lokacin sallah yayi.
Wani abin burgewa zakaga yara yan shekara uku zuwa hudu suna wasan kwallon kafa a kusa da babban masallacin harami, kuma zakaga yara da rigunan kungiyoyi irinsu PSG Bayern Munchen, Arsenal da Chelsea da ragowar kungiyoyi.
A yanzu haka wasan kwallon kafa babu wasan daya fishi farin jini a kasar ta Saudiyya sannan kuma hukumar kasar ce take kula da harkar kwallon kafa a kasar tun lokacin da aka kafa hukumar kwallon kafa a kasar a shekarar 1956, kuma hukumar itace take kula da kungiyoyin kwallon kafa a kasar da kuma tawagar yan wasan da suke wakilyar kasar a wasanni daban daban na duniya.
Prince Abdalla bin Faisal Al-saud shine ya kirkiri hukumar kwallon kafar kasar a shekarar 1956, kuma kasar Saudiyya tana cikin manyan kasashen da suka hada da kasar Iran da Japan a matsayin kasashen da sukafi wacce kasa samun nasara a nahiyar tasu duk da cewa kasar japan itace akan gaba amma Saudiyya ma tana buga abin azo agani a yankin idan har ana maganar kwallon kafa.
Kasar Saudiyya ta lashe kofin nahiyar ta Asia sau uku sannan ta halarci gasar cin kofin duniya sau hudu, kasar dai tafara zuwa gasar cin kofin duniya ne ashekarar 1994 wanda aka fafata a kasar Amurka.
Dan wasa Saeed Al-Owairaan shine yaci kwallon da masu sharhi sukace tafi kowacce kwallo kyau a gasar cin kofin duniya da aka fafata a kasar amurka a karawar da kasar Saudiyya tayi da kasar Belgium a wasan rukuni da suka buga.
A shekarar 1970 ne aka fara buga wasan firimiya na kasar Saudiyya wanda ake kira kofin kwararru na kasar Saudiyya wanda kamfanin Abdul-latif jameel ya fara daukar nauyi, kungiyoyi 8 ne dai suka fara fafatawa a gasar a shekarar da aka fara bugawa.
A shekarar 1981 ne hukumar kwallon kafa ta kasar ta yanke shawarar kara adadin wadanda zasu cigaba da fafatwa a gasar inda aka kara kungiyoyi goma suka koma sha takwas, goma daga ciki zasu dinga buga babbar gasar ta rukuni na daya yayinda 8 daga ciki zasu dinga fafatawa a rukuni na biyu.
A kakar wasa ta shekara ta 1984 zuwa 1985 hukumar kasar ta kara adadin kungiyoyin da zasu dinga bugawa a rukuni na daya.
Kasar Saudiyya ta samu nasarori da dama a harkar kwallon kafa inda a shekarar 1996 takai zagayen kungiyoyi 16 a gasar cin kofin guje-guje da tsalle –tsalle ta duniya, sannan ta samu kyautar silba a shekarar 1992 a gasar cin kofin comfederation na hukumar kwallon kafa ta duniya inda ta kare a matsayi na hudu,Sannan a shekara ta 2002 ta lashe kofin kungiyoyin da suke yankin gulf.
Yan wasan kasar kuwa sun samu kyaututtuka sosai inda a shekarar 1994 dan wasan kasar Saeed Al-Owairan wanda ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Al-Shabab ya lashe kyautar dan wasan dayafi kowanne dan wasa bajinta a nahiyar.
Yan wasa irinsu Nawaf Al-Temyam da Hamad Al-Muntashiri da Yaseer Al-Kahatani da kuma Naseer Alshamrani dukkaninsu sun lashe irin wannan kyautar a shekarun 2002 da 2005 da 2007 da kuma 2015.
Sai dai mata suma ba’a barsu a bay aba a kwallon kafa akasar Saudiyya, sai dai an kebance inda zasu dinga bugawa tunda kasar Saudiyya ta dukufa wajen inganta kwallon kafa a kasar.
Sannan akwai tashoshin talabijin da suke haska kwallon kafa inda a duk sati ake haska wasa sannan kuma suna sharhi akan wasannin kwallon kafa kamar yadda akeyi a kasashen ingila da spaniya da ragowar kasashe.
Hakan yana nufin kasar Saudiyya sunada babban tarihi a kwallon kafa wanda kuma ba abun mamaki ba ne a wannan lokacin.