Wasan Liverpool Da Man City Ya Bar Baya Da Kura

Na’urar tantace kwallo wato BAR na’urace da aka kirkirota domin yin amfani da ita wajen tantance kwallon da taci da kuma wadda bata ciba domin a daina tauyewa wasu kungiyoyin kwallon kafan hakkinsu.

Wannan na’ura anyi amfani da ita a gasar cin kofin duniya da akayi a kasar Russia a shekarar data gabata ta 2018 kuma tayi anfani a gasar a lokuta da dama inda har  a wasan Najeriya ta kasar Argentina tayi aiki

Domin da yawa za ayi wani laifin da alkalin wasa da mataimakansa basu gani ba amma daga baya sai wannan na’ura ta bayar da shedar ga abin da ya faru shikuma alkalin wasa sai ya yanke hukunci na gaskiya.

Rashin shigo da BRA cikin gasar firimiya ta Ingila ana tauyewa wasu kungiyoyin hakkinsu, domin a wasan da aka fafata a ranar Alhamis tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da Liverpool hakan ta faru, inda kungiyar kwallon kafan ta Liverpool ta jefa kwallon da ake ta cece kucen cewa taci, wasu suna bata ciba amma rashin wannan na’ura yasa aka hana Liverpool kwallon.

Tuni aka fara amfani da wannan na’ura ta tantance kwallo a gasar Laliga ta kasar Sipaniya da Siriya A ta kasar Italiya da French league 1 na kasar Faransa da sauran kasashen da suka rungumi sabon tsarin..

Ita kuwa hukumar dake shirya gasar ta firimiya tace zata yi amfani da ita a kakar wasa ta 2019 zuwa 2020, hasali da sunce zasuyi amfani da ita na dan wani lokaci a wannan kakar amma maganar tasha ruwa, inda sukace sai a gasar kofin kalu-bale zasuyi amfani da ita wato F.A wanda za a fara zagaye na uku a yau a kasar.

Shin rashin amfani da wannan na’ura shine yaci Liverpool? Kokuwa Manchester City ce tafi karfin Liverpool ta cinyesu a wannan wasa? Shin gasar firimiya bazata zama koma baya ba Idan basu shigo da BRA cikin gasar ba?

Wannan ne karon farko da Liverpool din tayi rashin nasara a gasar ta firimiya tunda aka fara gasar, kuma har yanzu akwai tazarar maki 4 tsakanin Liverpool da Manchester City duk da sun doke su.

Exit mobile version