CRI Hausa" />

Wasan Nuna Wake-wake Da Raye-raye Na Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Diplomasiyya A Tsakanin Sin Da Najeriya

Yau Laraba, ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin da ma’aikatar al’adu da yada labarai ta kasar Najeriya sun shirya bikin nuna wake-wake da raye-raye don murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Ministan al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Hu Heping, da wakilin musamman na ministan al’adu da yada labarai na Najeriya, kuma shugaban hukumar kula da al’adu ta Najeriya sun gabatar da jawabai na taya murnar bikin ta kafar bidiyo.
Gidan shirya wasan kwaikwayo na kasar Sin ne ya karbi bakuncin wannan wasan ta yanar gizo da ya kunshi babi uku, inda fitattu a fannin wake-wake da raye-raye na Sin da Najeriya suka nuna al’adun kasashen biyu ta hanyar rera waka, kide-kide da raye-raye.
Ta wannan bikin, kasashen biyu sun waiwayi abubuwan da suka faru a baya, da yin hangen nesa kan makoma a nan gaba, tare kuma da bayyana fatan jama’ar kasashen biyu kan tabbatar da zaman lafiya, da makomarsu ta bai daya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Exit mobile version