Tsohon dan wasan Newcastle kuma dan asalin kasar Ibory Coast, Cheik Tiote ya rasu yana da shekaru 30 bayan ya yanke jiki ya fadi a yayin atisaye da kungiyarsa ta Beijing Enterprise da ke China. Sakamakon wannan rasuwa ta Tiote, mun yi dubi game da wasu ‘yan wasa da suka mutu a lokacin da suke ganiyar sana’arsu ta kwallon kafa.
A cikin watan Yunin shekarar 2003 ne, dan wasan tsakiya na Kamaru Marc Bibien Foe ya rasa ransa sakamakon bugun zuciya a lokacin wasansu da Colombia a gasar FIFA ta cin kofin kalubale a Faransa da aka fi sani da Confederation Cup.
Foe ya rasu yana da shekaru 28 kuma ya buga kwallo a Manchester City da West Ham da kuma Lyon.
Akwai kuma Antonio Puerta na Spain da ya rasu a watan Agustan 2007 bayan kwanaki uku da ya yanke jiki ya fadi a daidai lokacin da ya ke buga wa kungiyarsa ta Sebilla gasar La Liga da Getafe.
Sai kuma dan wasan Motherwell Phil O’Donnell da ya rasu a watan Disamban 2007 sakamakon bugun zuciya da ya ritsa da shi a yayin buga wa kungiyarsa wasa a gasar Firimiya ta Scotland.
Dan wasan mai shekaru 35 ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin da ake shirin sauya shi da wani dan wasan.
A cikin watan Agustan shekarra 2009 ne, dan wasan Espanyol Daniel Jarkue ya gamu da ajalinsa bayan zuciyarsa ta buga a wani dakin Otel gabanin wasansu na share fagen kaka da Coberciano a Italiya.