Khalid Idris Doya" />

WASH Ta Bukaci Gwamnati Ta Ilimantar Da ‘Yan Bola-Jari Kan Tsafta

Wata kungiya mai zaman kanta da ke fadi tashi kan tsaftar ruwa da ta muhalli (WASH) bangaren ‘yan jarida na shirin reshen jihar Bauchi, sun bukaci gwamnatin jihar Bauchi da kungiyoyi masu zaman kansu da su tashi tsaye don kaddamar da gangami wayar da kai da ilmantar da ‘Yan Bola-Jari masu tsince-tsince kan tsafta da suturce kayyakin sawa na kariyar lafiyarsu.

Mista David Ayodele, shugaban kungiyar WASH Media Network reshen jihar, shine yayi kiran a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a jiya, yana mai fadin cewar kiran na da matukar muhimmanci domin kula da kiwon lafiya da kuma tsafta a tsakanin masu sana’ar lura da yanayin sana’arsu wadanda ya misalta mafi yawansu yara kanana ne da ke fuskantar barazanar kamuwa da rashin lafiya.

Ayodele yayi bayanin cewar sana’ar Bola-Jari wasu ke amfani da shi wurin bin kwararo-kwararo da wuraren zubar da shara domin tsintar karafu da wasu ababen da ka iya saidawa domin neman kudi wanda hakan ke matukar jefa rayuwarsu cikin hatsari ta rashin lafiya.

Daga nan sai ya nemi gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su ilmantar da ‘yan bola jarin muhimmancin tsaftar muhalli da na kayyakin sanyawa.

Yana mai fadin cewar akwai bukatar jagorori da su fitar da tsare-tsaren da zasu taimaki ‘yan bola jarin ta hanyar shirya musu tarukan kara wa juna sani da zai kai ga taimakonsu don su sauya dabi’unsu.

“Mutane da dama musamman matasa da suke tsakanin shekaru 6 zuwa sama, suna rayuwa ta hanyar tsince-tsince bola jari domin samun ababen da aka watsar da za a iya sake sarrafasu zuwa ga masu amfanin wasu ababen na daban.

“Maza da mata ana samun ‘yan bola jari a cikinsu don haka suna da bukatar a ilmantar da su matuka,” A cewar shi.

Mista Ayodele ya kara da cewa masu bola jarin suna fadawa cikin matsalar mura, jin ciwo ko yankewa, ciwon kai, ciwon kai amai da gudawa da sauran cutuka da suke kwasowa a sakamakon sana’arsu ta bola jari.

“An kuma gano mafi yawan ‘yan bola jari ba su amfani da rugunan kariya daga cutuka ko wasu ababen da ka iya illata su,”

“Karancin samun ilimi kan barazanar lafiyarsu da hatsarin da ke tattare da bola jarin na kara haifar da cutuka a tsakanin jama’a, A bayanin shi.

Shugaban sashin ‘yan jaridu masu fadakarwa kan tsaftar muhalli da ruwan, ya ce don haka akwai matukar bukatar gwamnatoci da masu ruwa da tsaki su ilmantar da ‘yan bola jari muhimmancin kula da lafiyarsu da amfani da ababen kariya a lokacin da suke tsince-tsincensu.

“Akwai muhimmancin da ke akwai masu sana’ar bola jari su samu rugunan kariya na musamman da za su ke tafiyar da sana’arsu da shi don kula da kiwon lafiyarsu,” Kamar yanda Ayodele ke cewa.

Daga bisani shugaban ya jawo hankalin ‘yan Bola Jari da su sanya safar hannu lokacin da suke tsince-tsincen ababen da suke neman kudi da su domin kaucewa cutuka da ke bazuwa ta hanyar ta’anmuli da shara ko datti.

Exit mobile version