Connect with us

NOMA

WASH Ta Nemi Jama’a Su Yi Amfani Da Kuri’unsu Don Samun Tsaftacaccen Ruwa

Published

on

Shirin nan mai hankoron samar da tsaftacaccen ruwa da tsaftar muhalli wato ‘Water Sanitation and Hygiene’ (WASH) a takaice, na ci gaba da gangamin wayar da kan jama’a a jihar Bauchi dangane da muhimmancin yin amfani da katin zabe wajen samun ruwan amfanin yau da gobe mai tsafta da tsaftar muhalli, kungiyar ta sanar da cewa jama’a za su tabbatar da hakan ne ta hanyar  kulla yarjejeniya a tsakaninsu da ‘yan takarasu domin samun ruwa mai tsafta.

Shirin wanda aka kaddamar bayan zagayen da ya yi zuwa gun sarakuna da masu ruwa tsaki kan wannan batun a cikin shirin kungiyar na ‘Bote for Wash’ wato ‘ ka yi amfani da kuri’arka don a inganta maka sha’anin ruwa’.

Da yake jawabi ga ‘yan karamar hukumar Misau da Dambam da Giade da kuma Darazo, Manaja a kungiyar ci gabantar da mata wato ‘WDAS’ Mista Sukumun Ezekiel ya bayyana cewa, manufar shirya wannan taron fadawarkar shi ne don a tattaro matsalolin da jama’a suke fuskanta kan sha’anin ruwa da kuma tunkarar ‘yan siyasa masu neman darewa kan karagar mulki a kujeru daban-daban domin samar da ruwa da tsaftar muhalli, “Yau mun wayi gari ‘yan siyasa da masu zabe sun fi bukatar a ba su dan wani abu su jefa a aljihunsu ba tare da la’akari da an kawo musu wasu ababen da za su kyautata rayuwarsu ba.

“Don haka ne wannan shirin na WASH wanda ya kunshi kungiyoyi daban-daban suka fitar da wani shiri na ‘Bote4Wash’ domin ilimantar da jama’a kan muhimmancin bukatar kyautata sha’anin ruwa daga ‘yan siyasa gabanin da kuma bayan zabensu,” In ji shi

Ya kara da cewa, ta irin wannan hanyar ne jama’a za su samu cin gajiyar shugabaninsu, don haka ne ya nemi jama’a a kowani bangare su tabbatar da kulla yarjejeniya a tsakaninsu da ‘yan siyasa don kyautata sha’anin ruwa, “Idan dan siyasa ya zo muku ya nemi ku zabe shi ya shaida muku manufofinsa; a maimakon ku tsaya amsar kudinsa sai ku shaida masa cewar kuna da bukatu; ga takarda ya yi alkawarin zai inganta muku sha’anin ruwa da tsaftar muhalli. Idan ya yi muku wannan alkawarin ku zabe shi, idan ya ki ku bar shi,” In ji daya daga cikin masu jawabi a wajen taron

Ya kara da cewa, shirin WASH ya kudiri aniyar tsayuwar daka domin cim ma burin kyautata sha’anin ruwa a tsakanin al’umma, a bisa haka ne shirin ya nemi jama’a su tabbatar da shigar da bukatar samar da ruwa ga ‘yan siyasa domin kyautata rayuwarsu.

Jami’in ya yi tilawar cewar ruwa da shi ne ake gudanar da al’amuran rayuwa da daman gaske don haka ne ya nemi kowa ya tashi tsaye domin tabbatar da samar da ruwa da muhalli masu tsafta don kyautata rayuwar jama’a.

Sukumun Ezekiel ya shaida wa masu ruwa da tsakin cewa, idan aka kyautata sha’anin ruwa tamkar an yi riga-kafin kamu wa da cutttuka ne, yan kuma ci gaba da cewa ta hanyar rashin ruwa mai tsafta, ana iya kamuwa da cutattuka da dama, haka zalika ga rashin tsaftace muhallai, a bisa haka ne ya nuna gayar muhimmacin da ruwa mai tsafta ke da shi a tsakanin al’umma.

Taron ya hada fuskokin shugabanin addinai, masu fama da bukata na musamman ‘nakasassu’ da ‘yan jarida da sarakunan gargajiya da kungiyoyin al’umma daban-daban, da suka fito daga kananan hukumomin hudun don tattauna yadda za su ilimantar da jama’a dangane da amfani da kuri’arsu wajen kyautata musu sha’anin ruwa, inda suka fitar da matsayar cewar za su tabbatar da kulla yarjejeniya da masu neman kujerun siyasa a lokacin da suka zo gare su don neman kuri’a.

Bayan tattaunawar, an bai wa dukkanin masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin damar su kebe da masu ruwa da tsaki a garinsu domin fito da irin matsalolin da suke fuskanta, inda kuma kowace karamar hukuma ta kawo nata sakamakon.

Da suke bayyana matsalolin da suke fuskantar a karamar hukumarsu, masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Darazo wanda sakatarensu a wajen zaman, Abduljalal Abdullahi Hamza ya sanar da cewa, suna da matsalolin kan sha’anin ruwa da suka kunshi karancin fanfonan tuka-tuka a cikin makarantu da massalatai da asibitoci da sauran wuraren hidimar jama’a, ya kara da cewa, suna kuma fukantar matsalar rashin bayan gida a wuraren da jama’a suke hada-hada, ya ci gaba da cewa, suna neman a gina musu hanyoyin wucewar ruwa kwalbati-kwalbati.

A Yankin karamar hukumar Misau kuwa, Alhaji Yahaya Iliyasu shi ne ya karanto nasu bukatun, inda ya ce suna da famfunan tuka-tuka guda 390 a cikin karamar hukumar, amma guda 200 ne kadai suke aiki, inda 190 ba sa aiki, wanda a halin yanzu suke neman a samar musu da tuka-tuka guda dubu 2,000; sannan kuma suna da taskar ruwa mai amfani da hasken rana guda 19 amma 18 ne kadal suke aiki, inda 31 suka jima da lalacewa, inda suka shaida cewa, suna bukatar a samar musu da guda 100 a halin yanzu wanda hakan zai kai ga kyautata sha’anin ruwa da tsaftar muhalli.

Ita kuma karamar hukumar Giyade, cewa suke yi suna neman a samar musu da karin bayan gida da bohol-bohol a dukkanin wuraren hada-hadar jama’a, sannan kuma, suna neman a gina musu magudanar ruwa wanda hakan zai ke bai wa rowan zarafin wucewa kan tsaye; sannan kuma suka nema a samar da masu fadakarwa dangane da muhimmancin tsafar muhallai da kuma sha’anin ruwa, hakan ya fito daga cikin sakamakon zaman wanda Hafsat Abdullahi ta karanto.

A karamar hukumar Dambam suka ce, ta bakin Saratu Adamu a madadinsu; kawo yanzu suna da makarantu 125 a cikin garin amma makarantu 58 ba su da bayan gida  a cikinsu; suna da kuma asibiti guda 45 amma 38 babu masai a cikinsu, ta kuma shaida cewa karamar hukumar na neman karin wuraren zubar da shara, bayan gida, da kuma hanyoyin wucewar ruwa.

A karshen zaman dai, masu ruwa da tsakin sun amince kan cewar ba za su sake zaben dukkanin wani dan siyasa da ya gaza cika musu alkawari kan sha’anin ruwa ba, suna masu shaida cewa za su tabbatar dukkanin alkawarun da suka kallafa da ‘yan siyasar sun cika musu.

Abudllahi Rabi’u wani mai fama da bukata ta musamman ‘gurgu’ daga karamar hukumar Dambam ya shaida cewar suna neman a samar musu da bayan gida wanda ya yi daidai da irin tasu bukatar, yana mai shaida cewar babu yadda za a yi suke iya amfani da bayan gidan da ake ginawa domin amfanin mutane masu kafa, don haka ne suka nemi a samar musu da hakan.

Sukumun Ezekiel ya sanar da cewar za su karade dukkanin kananan hukumomin da suke Bauchi da irin wannan bukatar da zimmar kyautata sha’anin ruwa ta hanyar amfani da kuri’a wajen zabin wanda suka tabbatar zai kyautata musu sha’anin ruwa.

Shi dai shirin WASH yana gudana ne a karkashin ‘Water Aid’.

Advertisement

labarai