Bilkisu Yusuf Ali" />

Wasika Zuwa Ga Gwamna Ganduje: Bayan Tiya Akwai Wata Cacar!

Wasika Zuwa Ga Gwamna Ganduje: Bayan Tiya Akwai Wata Cacar!

Daga Bilkisu Yusuf Ali

 

Zuwa ga Mai Girma Gwamnan Jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Bayan Gaisuwa da fatan alheri da fatan an yi ummara lafiya an dawo kan aiki cikin nasara, Allah ya amshi ibada amin. Ya a ka ji da hayaniya da fadi-tashin zabe? Alhamdllah, bukatar maje hajji sallah. Don haka mu na addu’ar Allah ya rika ma ka, amin. To, amma fa Your Edellency, bayan tiya akwai wata cacar. Don haka na rubuto ma ka wannan wasikar. Mu masu kishin jam’iyyar APC kuma masoya jam’iyya mu kadai mu ka san bacin rai da takaici da kunci da firgici da faduwar gaban da mu ka shiga a lokacin da a ka kai iya wuya ranar zaben gwamna kafin tafiya Inconclusibe. Allah shi ne abin godiya a karshe, jam’iyyarmu ta yi nasara kuma mun tsoma kafa a nedt lebel, ko ba komai dodar ta tabbata.

To, amma Bahaushe ya ce tuna baya fa shi ne roko! Don haka zan hasko ma ka manyan kurakuran da ka aikata na siyasa, wadanda su ne mu ke gani ummul aba’isin da ya kai mu ga tafiya Inconclusibe. Da a ce babu ko da rabinsu, da ba mu girgiza ba har wankin hula ya kusa kai mu dare. Da tuni mun jijjige PDP tun da sanyin safiya kafin ma sha biyu mun lashe zabenmu, kamar dai yadda mu ka yi a zaben shugaban kasa. Sannan an ce daga na gaba a ke gane zurfin ruwa. Don haka duk mai hankoron maye gurbinka bayan shekaru hudu masu zuwa, lallai ya tabbatar bai kuskura ya aikata irin wadannan kurakuren a siyasa ba. Wadannan kuwa abubuwan su ne:-

 1. Soke ilimi kyauta, wanda a ka faro a gwamnatin baya. Duk da cewa an da ma an kullo maganar bada ilimi kyautar ne, don a ga wallen wanda zai gaji gwamnatin baya, amma da a ce ka kamanta ko da a mataki guda ne ko firamare ko kuma a sakandare ne da ka kusanto kanka da iyayen yara wadanda duk ka ga dansa a wannan makarantun ka san talaka ne. Gaza hakan ne ya fara kulla ma ka gaba da talakawan jahar Kano. Da fatan a gaba za ka gwada yin haka, sannan wadanda ba za a dau nauyinsu ba a ba su wani abu ko da ba yawa na abinci ko da sau daya ne.
 2. Rabuwarku da Kwankwaso ta janyo ma ’yar tsama tare da dakushe haskenka, amma da ka bi halayyar da a ka san ka da ita ta kau da kai da hakuri ka yi shiru da mayar da martani ga bangaren Kwankwasiyya, ka bar yaranka su tare ma ka fadan, da ya fi ma ka. Maimakon hakan ka cigaba da yin ayyukanka na alheri, wanda shi ya janyo Kwankwaso na kan mulki, amma Kanawa na cikin gwamnati da mu na gefe mu ka lashi takobin sai kai, kuma Allah ya tabbatar da fatanmu. Amma sai ka gaza yin kwatankwacin abin da ka yi a bayan, ka mulki zuciyar Kanawa.
 3. Rikicin zaben ciyamomi na 2018 shi ma ya janyo fushin ’yan jam’iyya. Na farko dai an tsula wa fama-faman takarar ciyaman da kansiloli kudi kuma babu wani tallafi da jaha ta bayar. Sannan kowa ya san yadda a ka yi zaben firamaren, wanda daga fadarka a ka yi zaben na son zuciya. Ba za a ce laifinka ne dari bisa dari ba, amma dai ka dau kaso mafi tsoka, don kai ka sakar wa wasu daidaikun ’yan jam’iyya maimakon ka nemi ra’ayin talakawan da ke karamar hukumar.
 4. Kananan ’yan kasuwa musamman ’yan tebura na Kwari da na kasuwar Kofar Wambai da sauran kasuwanni babu wani tallafi da ya zo hannunsu kai tsaye ko a kaikaice, don harkar neman abincinsu. Wannan ya kuma sa wa adawa da gwamnatinka ta na zagayawa.
 5. Gaskiya a bangaren yada labarai ka sami matsala. Ba ka da masu yaki da baka ko a rubuce sam-sam! Wannan kuwa a bayyane ya ke , ba wani tsari da a ka fito da shi, don yada ayyukanka da farfaganda ta siyasa a kafofin sadarwa. Misali; makarantun da ’yan adawa ke ta ya madidi Kwankwasiyya ta gina kuma a ke zargin ka rufe, ba wata hujja da ta zagayawa kan dalilan da ya sa ka rufe su. Misali; Legal ta Kunci wadanda ke da alaka da ilimi sun san yadda a ka yi karo-karon malamai a ka zuba su, amma ba a yi wani tanadi ba na koyarwa a gwamnatin da ka gada. Da kansu malaman su ka roki a mayar da su inda su ka fito wanda sun san ba laifinka ne ba, yaudarar su gwamnatin baya ta yi. Watakil da ma an yada da hotunan kangwayen da ta gadar ma ka, da watakila da Kanawa sun sasssauta daurin zanin da su ka yi ma ka da tsanani a wannan bangaren. Amma ina! a kafofin Facebook da Tweeter da sauran kafofi inda a nan ne a ke wanke zuciyar matasa a ke sa mu su akida a ke zayyana mu su hujjoji na su so ko su ki, to fa APC ba ta da wadannan sai ka kwana ka wuni ba ka ji wani abu na cigaba ba. Wannan ma fa kai kenan, kada kwamishinoninka su ji labari; su sun dauka har yanzu rayuwar Analog ce. Gaskiya jam’iyya na bukatar bita ta musamman a wannan gabar.
 6. Karbar haraji a wannan gabar musamman ga kananan masu neman na abinci gaskiya matsala ce musamman ma da ba fito da wata hanya don more rayuwar talakan ba. Sannan ma karbar harajin ba wani tsari da a ka bi na hikima, sai ku ka bar ’yan adawa su ka ci karensu ba babbaka, musamman a harajin gidaje da na ’yan adaidaita da kuma na ma’aikata. Shi fa dan Najeriya ma a batun harajin nan sai an yi ma sa bita.
 7. Matsalolin inshorar lafiya ga ma’aikata ita ma ta bar baya da kura Mai girma Gwamna. Rashin bayani da yin kudin goro da rashin tambayar jin ra’ayin ma’aikatan. Watakil da an bude abin ga mai so, ba wai wajibi ba, da ya fi zama daidai.
 8. Zaben fidda gwani da a ka yi na ’yan majalisun jaha da na tarayya Mai girma Gwamna shi ne ya janyo rabin matsalar da a ka samu a zaben nan. Akwai wadanda su ka cancanta talakawa ke son su, amma sai a ka bi sanayya da kara a ka ki zabin talaka. Sannan zantuttuka sun yi ta zazzagayawa cewar sai an bayar da na goro kafin a tsayar mutum takara. Su wadanda a ka ce sun bayar, su ne su ka dinga yadawa. Wannan ma ya sa da zabenka ya zo su ka ce su ma kujerarsu saya su ka yi. Don haka kowa tashi ta fisshe shi. Wadanda kuma su ka cancanta ba a ba su takara ba duk kuwa da cewa su na da mutane, su ka ga gara su rama ta hanyar anti-fati. Ka san komai kuma na san an sanar da kai ko su waye, ba sai mun maimaita ma ka ba. Idan kuma ka na bukatar ji, mu mu na da shaida.
 9. Rikice–rikicen cikin gida da rashin kalamai masu dadi daga bakin shugaban jam’iyya ya sa ’yan jam’iyya cire hannu da zuba ido, sannan ya kara assasa rarrabuwar kai, inda a ke zaben ’yan marina a jam’iyyar, wato kowa da inda ya sa gaba.
 10. Kafin zaben 2015 gwamna ya sa an yi kungiyoyi, don yakin neman zabensa. Wadannan kungiyoyi sun yi aiki kuma ya sani, amma da ya hau kan mulki ba wani tsari da ya bi wajen neman wadannan kungiyoyi a kyautata mu su. Haka nan kuma da yawansu ba su yi fushi ba da zaben 2019 ya zo, domin da dama su na sa rai za a tafi da su a lokacin zaben, to amma sai a ka yi shakulaton bangaro da su.
 11. Rashin daukar ma’aikata kuma ko da za a dauka din sai mai kafa da dan siyasa. A bayyane ta ke aiki a jihar Kano sai ta hannun shugaban jam’iyya ko babban dan siyasa ko kuma ’yan majalisa na jaha ko tarayya, amma talaka bai da ikon ya ji a na neman aiki ya nema ya samu. Idan ba ka sani ba Ya Mai girma Gwamna, to ka sani talakawa kar su ke kallon ku a wannan bangaren. Za a yi shelar neman aiki, amma tuni a karkashin kasa an rabe guraben. Wannan shi ya kara hada ma ka gaba da ’yan boko ’ya’yan talakawa, don sun ga yadda a gwamnatin baya a ka yi da wadda kai ma ka san yadda a ka yin.
 12. Rashin daukar nauyin karatun matasa masu digiri da daya da na biyu da na uku ya sa matasa sun ji kamar ba su a ke mulka ba. Ka kuwa san da shi ku ka rudi Kanawa a shekarar 2011-2015. Me ya hana ka kamantawa? Idan kun kamanta me ya sa ba ku yayata ba? Ya na da kyau daukar nauyin karatun wadanda su ka fito da kyakkyawan sakamako a sakandire ko a makarantun gaba da sakandire musamman wadanda ba su da karfi kuma sai an tabbatar da ba su da hali. Ba fa sai an kai su kasashen waje ba a jami’o’in kasar nan za a iya samo musu gurabe kuma za a sami kyakkyawan sakamako na jan ra’ayin talaka.

13 Mai girma Gwamna a yi hakuri, amma batun Gaskiya sanyin gwamnatinka da son ka kyautatawa kowa ya mayar da kai ba tsayayye ba a bangaren shugabanci. Shi kuwa shugaba a na son a same shi tsayayye mai magana daya kaifi guda marar tsoro. A fa mutane akwai ma fa wadanda su zuma ne sai da wuta. Za ka yarda da ni a haka idan ka dubi kunshin kwamishinoninka da dama kai ka san ba mataimaka ba ne. Ka ma ga hujja a zaben nan wasu ma ka san ba ’yan jam’iyya ba ne, wasu kuma ba ’yan siyasa ba ne, wasu ramin kura ne daga su sai ‘ya’yansu, wasu kuwa irin wadanda iyayensu ba sa mutuwa ne a siyasa tun daga lokacin Malam Shekarau su ke rara gefe da kai zance, amma abin mamaki sai ga su a hannun damanka sun shallake kowa. Kuma su na nan jikinka, amma su ka tafi taya PDP yakin neman zabe, kowa ya gan su. Ba a yi mamaki ba don da ma an san duk wanda ya sai rariya ya san za ta zub da ruwa. Ka yi tsam in ma da hali ka sa a yi ma kyakkyawan nazari a kunshin kwamishinoninka tunda suka hau zuwa zabe sau nawa kowanne aka ja sunan sa a radiyo ko talabijin ko ma a kafofin sadarwa ta zamani? In da zan rantse b azan yi kaffara ba za ka sami wani ba a ja sunansa sau uku ba. Amma za a ce ba a ji sunan wasu ba?

 1. Tsarin da ka assasa na ‘ya’yan bora da mowa a gwamnatinka ya janyo rarrabuwar kai da rashin taimakon gwamnatin ta kowanne janibi. Mai girma Gwamna a na zargin ka da fifita wasu da kuma danne wasu a cikin gwamnatin. Wasu an sakar mu su dama su na damawa, wasu kuwa an kyale su talakawa da abokanan adawa su na tunzura su. Adalci a matsayinka na gwamna na da muhimmanci.
 2. Yaudara da rashin cika alkawari na damun talaka. Misali a kwanan baya a ka sa yara masu N.C.E su ka yi tururuwa su ka fito ‘ya’yan talaka za a dauke su koyarwa, amma ashe ba haka ba ne hatta a baya an ce al’umma su fito su bude asusun ajiya a bankin sitalin kai ne za ka tsaya a ba su kudin jarin. Mu ka yi ta yayatawa amma daga baya a bankin in ka je ka tambaya ya shuru sai su ce ai zancen ‘yan siyasa ne kawai. Ire-iren wannan da dama wanda da ya kamata in har an san abu ba zai yi wu ba to kada a fara ya fi alheri. Ko kuma a yi dai-dai ruwa dai-dai tsaki.

16 . Kananan hukumomi fa mai girma gwamna sun zama tamkar zaman kare a karofi. Ba wani abu da yake zagaya wa Kuma nan talaka yake. Anan ne a ke zabe a nan ne matansu da ‘ya’yansu mata ke fitowa kome zafi kome sanyi su dangwala kuri’a amma sun fi kowa shan wuya da zama abin tausayi. Da za a samar da wata santa a duk karamar hukuma ta din-din-din don tallafawa yan karamar hukumar ta koya musu sana’a da ta yaki da jahilci ta ka assasa wani alheri da za a gani.

 1. Rashin bibiya bayan ka damka amana ta aiki a hannun wasu sannan a hukunta duk wanda aka samu da cin amana a fili tare da fito da hujjojin da aka kama mai laifin a bayyane. Zai taimaka kwarai wajen ayyukan da aka yi don talaka ya isa gare shi.
 2. Akwai wadanda su ka shigo jam’iyyarmu ta APC daga PDP kuma sun taka muhimmiyar rawa a tafiyar ya kamata in a ka zo raban mukamai kada a manta da su don kuwa da su za a tsara tafiyar 2023. Don kuwa sun taka rawar da dama ‘yan jam’iyya ba su yi kwatanta ba, sannan ragowar ‘yan’uwansu da ke PDP da PRP kun dai ga tasirinsu a can wannan dama ce da za a janyo su don sharewa Dan takarar Gwamna hanya a 2023 in Allah ya nuna mana.
 3. Batun Gaskiya Mai girma Gwamna ka tula dattijai a gwamnatinka, babu matasa kuma matasa a kowacce nahiya sune ruhin al’umma su ne suke da kishi da karfin gwiwa da karsashi da rashin nauyi da kurde-kurde kuma su ke shiga cikin al’umma su sake saboda rashin nauyin da ke kansu don haka su ne suka fi jin me al’umma musamman ‘yan’uwansu matasa ke ciki. Kai hatta a wajen yada ayyukan gwamnati da farfaganda da sanin hanyoyin sarrafa na’uororin zamanin nan sune a kan gaba ya kamata a ba su dama. In ka lura jam’iyyar adawa abin da ya sa ta wannan farin jinin ai matasa ne.
 4. Mai girma Gwamna ko ka sani ko ba a sani ba iyalanka musamman mai dakinka ta shiga cikin gwamnatinka ta yi kaka-gida har jama’a sun gane cewa idan a na son wani abu a gwamnatinka fa sai an yi kamun kafa ta hanyar kai gaisuwa ko zargin bayar da na goro. Wannan nakasu ne a gwamnatinka da ‘yan adawa ke sukar ka da shi kuma ka sani sukar na yin tasiri. Hotunan da ke yawo a social media da ire-iren hotunan ya ishi shaida. Sannan bayanan sirri da hotunan iyalanka mata kan fito da shiga wadda a matsayinka na Bafulatani mai riko da addini bai kamata ba. Kada ka manta har yanzu kano suna nan fa da rikon al’adunsu da aka san su da shi da kuma kamanta addini
 5. Akwai ’yan Lagasi Fati, wadanda a ka hadu a ka kafa APC, Mai girma Gwamna su ma fa korafinsu ababen dubawa ne. Misali a gwamnatin baya da ku ka faro da Mai girma Kwankwaso ya zamana duk mataimakin shugaban karamar hukuma dan Lagasi ne sannan an saka su a gwamnatin, amma a lokacinka sai ya zamana an mayar da su aljihun baya. Wannan ya sa su ka nade hannayensu su ka zuba ma ka ido su ma a lokacin zabe.
 6. Mai girma Gwamna akwai rashin tallafi ga ma’ikatanka kama daga kwamishinoni, ciyamomi har kansiloli an bar su babu wani welfare kwamishina na kukan babu yana jiran a yi albashi ciyamomi da an bayar da giran yau gobe babu ko dubu bare kansiloli ba me kallonsu da kima. Wannan kuskure ne kudin nan fa na karamar hukuma shi ne ke tallafar na kasa wato talaka da su ake kananan ayyuka kamar kwalbati gyaran makarantun firamare gidan wani ya rushe ibtila’i ya fada ma wasu ko gyaran makabarta ko kasuwa da sauransu. Bai kamata ka matse mataimakanka ba kamar yadda mu ke ji na kusa da su na fadi da abin da su suke fada da abin da idonmu ya gane mana in har a nedt lebel aka ci gaba da haka to fa ba a yi wa mai jiran gado kyakkyawar shimfida ba. Ya kamata a girmama su kamar yadda gwamnatocin baya ke yi.
 7. Matsalolin ‘yan kwangila Mai girma Gwamna a kuma dubawa. Akwai son zuciya da rashin tabbas da ma zubewar kimar kwangilar a Kano. Misali ‘yan kwangila na kukan bayan sun bayar da 25% ko 30% na al’ada sai kuma a bijiro musu da wasu wadanda ba su da ma hurumi a kwangilar a ce su ma a ba su wani kaso. Babbar illar da za ta biyo shi ne Samar da ayyuka marassa inganci.

A karshe Mai girma Gwamna Ina kara taya ka murna da yi ma fatan alheri. Kamar yadda a ka saba ayyukan alheri kowa ya sanka da zumunci da son addini da kunya da girmama manyanmu muna fatan ka dore.Ina rokon a kalli wasikata da idon basira kafin ka nada sababbin kwamishinoni da mukarraban gwamnatinka don kada ka kuma yin kitso da kwarkwata duk wanda bai taka rawa a zaben da ya wuce ba ko ma ya yi Anti-fati muna fatan za ka ajiye shi don ba shi da amfani.

Bissalam! Sai ka kuma ji na, idan har na ga kunshin kwamishinoninka. Zan bi su daya bayan daya in yi warwara a kan su, idan har irin wadancan taron tsintsiyar ne ba shara.

 

Bilkisu Yusuf Ali (Dr), marubuciya ce kuma ’yar jarida, ta rubuto daga Kano. Za a iya tuntubar ta a imel bilkisuyusuf64@gmail.com ko lambar waya 08064159965.

Exit mobile version