Wasikar Malam Aku (2)

Tare Da: Abdulyassar Aminu Abubakar, 08093824782 abdulyassaraminu782@gmail.com

Gyara Kayan Ka..!

Yau ma sallama na ke yi mu ku irin wadda Annabin Tsira ya horar da mu rika yi ga dukkan wanda muka tarar bisa wani abu a tsugune ko ko yana tsaye.

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

Dira ta cikin wannan yanki da majalisar gungun samari na yi kwalli wanda a nan din tunda fari na so taka birki ko kuma mai ya kare min tsayuwa wajensu dole na. Dan sakon da na saba zagaya wa da shi don yin babban kira ga sauran mutane na fiddo daga wani zamalon aljihuna da madinkin ya yi shi har bisa gwiwa, na yi kokarin janyo hankalinsu gareni don na sami karbuwa ko Allah zai datar da ni wani guda ya ji ya gyara.

Sai da na fara bai wa kowa hannu muka yi musabiha fuskata sake kai ka ce yau ne daren sallah.

Nan na fara da karanta wata zungureriyr takarda da na rika mamakin yadda hannuna bai yi batan dabo wajen yin rubutu ko in soke wani layin ba, komai na yi shi daidai bisa tsari kai ka ce ba rubutun hannu ba ne na inji ne.

Na fara kamar haka: Ba rayuwar Malam Bahaushe ce abin tir ba, a’a dabi’ar da yake sallada wa kan shi ita ce ta ci sunan tir!. A loton da aka ta shi bukukuwa irin namu na gargajiya musamman a buki irin na aure nakan ga duka dabi’u na matasa maza ya zuwa iyayenmu mata da suke amsa sunan ‘yanmata ba ka bambance wanne irin matsayi suke taka wa wajen sanya sutura. Yayin da za ka kai ga ganinka da bululu wanda kodayaushe ganinka sai da shi, ka ga shiga da yanayin mu’amalarsu duka ta sauya ta yadda ba ka iya bambance Habu da Sabira saboda sauyi da za ka gani dan Bahaushe ya cakudu da mata muharramansa kuma ba su zamo ba.

Kai a wasu lokutan ma ka kan iya ganin hargitsuwar da za su yi ko kafurai sukan sassauta a yayin da wasu dalilai suka ta so, su ne dai ake yi wa kallon marasa ta ido wadanda muka ga ni a littafi mai tsarki (Alkur’ani) Allah ya kira su da kafiruna, sallah da salati duka ba ka gani suna yi, da za ka bincika suma da irin tasu tarbiyar. Ba iya ga samari ko kuwa ‘yanmata ba, nakan ga abin har kan manyan mata da igiyoyi uku na Sunna suke daure da su. Ba igiyar shanya ba ballantana da sun so su katse ta su sauya ko ko ta jan ruwa ga rijiya.

Da an ce an zo sharholiyar buki, to a nan ne kuma suke samun lasisin yaye lullubin da aka yano shi tun daga daka.n mace da diyanta garma-garma ka ganta a kan layi da sauran mata suna buga lomar abin da masu jajayen kunnuwa ke ambaliyo ta cikin kasarmu (shinkafa), kullum ana ci amma kallonta ake jinjirin wata.

A gidan buki ne za ka hadu da mace ta kure maka wasu kilo mitoci ba tare da rufi a jikinta ba wai da sunan Musulma, anya kuwa ba musulmama ba ce?.

A dan sanin da na yi kuma da sauraren fadakarwa ta Malaman kasarmu ina ji suna ambata wa da yawa al’adun Musulmi Bahaushe ba su sabawa Musulunci ba ko da, da wucin layi guda kuwa. Ba fa iya bangaren mata abin ya yi karfi ba, har ga na mu huren ya zo.

Haka nan na yi duba matasan yanzu maza babbar dabi’ar da suka rika ita ce sanyo na su abubuwan wadanda sun ci karo da addini da.kuma al’adar Malam Bahaushe. Haba Malam Mula ka tuna tarbiyar da ake ta kakarin ka ta so cikinta a wannan bigire naku wanda babu wandanda suke wannan fafutuka sai wadanda ta silar su ka fado duniya har ka ke samun ‘yan

kwabbai ka na baddawa, amma su kake sanya wa a sahun masu rashin waye wa? To, ko dai ya ya ma dai suke ta silar su ka zo idan kuma batun zamani kake yi, ai kafin ka ga zamanin su sun gani har ma suka hada da ganin naka gurbatacce da bai kunshe da komai sai raina iyaye da bayin Allah nagari. Baki daya ba a amfani da fadar Allah abin da ya zo rai kawai shi ake yi an sani ake take sanin.

Duk wadanda suke wajen haka na ga jikinsu ya yi lakwas kai ka ce da gawa aka gifta.. yo a wannan loton ma ai ba a tsoron wuce wa da gawa har shiga ake yi da takalmi cikin makabarta wanda kuma haramun ne. Bawan Allah ko kai ke kwance ai ba ka so a taka ka ba ballantana wanda Allah ya karbi rayuwarsa ka sani ni, kai su da ita mun san dole mu amsa wancan kira!.

Da kai wa karshe na linke wannan takarda da nake kira JI BA DOLE, YARDA SAI KA GA DAMA ina shirin kara wuta ya zuwa bigiren da Allah ya ajiye ni, wani guda daga cikin su ya tambaye ni da ya ya suna na? Na ba shi amsa da “BAKI ABIN MAGANA sunan da mutan gari ke ambata ne wannan, sunan yanka kuma YAKUBA.”

Nan yau ma zan dasa aya idan da rabon mu sake gamo ma yi sai dai ina tunashe da ku yayin tashi daga majalisi ka da ku mance da koyarwar Shugaban duka bayi.

Wassalam, ni ne naku MALAM AKU. Sai mun sake gamuwa.

 

Exit mobile version